HausaTv:
2025-11-27@21:52:01 GMT

An Bude Juyayin Ashura A Fadin Iran

Published: 28th, June 2025 GMT

A ranar farko ta watan Muharram, an bude juyayin Ashura ta hanyar yin taron kananan yara a matsayin nuna  juyayi ga jaririn Imam Hussain          ( a.s)  Ali Asgar ( a.s) da abokan gaba su ka kashe a Karbala.

Iyaye mata dauke da kananan yaransu  masu watanni  6 daga  haihuwa sun cika wurare mabanbanta na Iran suna masu mika juyayinsu na shugaban Shahidai Imam Hussain ( A.

S).

Bugu da kari iyaye matan sun gargadi HKI da Amurka akan fada da Iran, suna masu cewa; Dukkanin ‘ya’yansu da za su girma za su kasance sojojin Imamul Hujja ( a.s) da za su yake su.

Baya ga Iran da akwai kwasu kasashe 45 da ake juyayin Ashura a duniya.

Taro mafi girma na juyayin Ashuda din shi ne na hubbaren Imam Riza     ( a.s) dake birnin Mashhad. Adadin wuraren na juyayin Ashura na kananan yara sun kai 700 a cikin birane da kauyukan Iran.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: juyayin Ashura

এছাড়াও পড়ুন:

An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina

Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.

A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra
  • Makaman Iran Masu Linzami Ne Kandagarkon  Dake Takawa Makiya Birki
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta