2025-06-14@05:12:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5672

«ko sarki ko»:

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi karin haske game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, wanda shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarta a Kazakhstan, yana mai cewa, Sin na da yakininta hanyar taro, ita da sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya biyar, za su zurfafa dunkulewa, da amincewa da juna, da gina matsaya guda ta fuskar hadin gwiwa, da zurfafa daidaiton dabarun ci gaba, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da kara kuzarin gina al’umma mai makomar bai daya ta Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya.   Bisa gayyatar da shugaban jamhuriyar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev ya yi masa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron koli na...
    Babu abin da ya rage yanzu, illa babatun zantukan siyasa da ‘yan siyasar ke ta fama yi a kasar, wadanda suka jarabtu da matukar son mulki. Wannan abu da ke faruwa yanzu, ko shakka babu zai canja, zai canja din ne kuwa yayin da ‘yan siyasar ke aiwatar da tsare-tsarensu, sai masu jefa kuri’u a Nijeriya kuma su yanke hukunci. Shekarar 2027, za ta kasance mai ban mamaki tare da kalubale ga ‘yan Nijeriya. A bisa dukkan alamu, jam’iyyar APC ta dukufa wajen kara habaka karfinta ne kawai da ganimar ‘yan adawa. Tana ta faman sa kanta cikin rigingimu, har wadanda ba su shafe ta ba a cikin shekaru biyun da ya rage mata ta yi gaba na kunci da...
    Da yake magana kan muhimmancin bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta bana, Idris ya ce wannan ba lokacin murna kaɗai ba ne, har ma lokaci ne na nazari kan cigaban ƙasar wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da farfaɗowar tattalin arziki.   Ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka tara daga cire tallafin man fetur wajen gina muhimman ababen more rayuwa, ciki har da manyan tituna guda biyu da za su haura kilomita 1,700, waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da haɗa yankuna daban-daban.   Ya ce: “Manufar ba wai haɗa yankuna ba ce kawai, amma samar da damarmakin tattalin arziki.   “Nijeriya na ƙoƙarin komawa kan sahihiyar hanyar ta. Tana sake zama ƙasa mai daraja a idon duniya.   “Martabar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi koyi daga akidun dan mazan jiya, kuma jagora na gari Chen Yun, tare da kara azamar dorar da kyawawan dabi’unsa cikin himma da kwazo, don gina kasar Sin mai matukar karfi. Shugaba Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar, ya yi kiran ne a yau Juma’a, cikin jawabin da ya gabatar, yayin taron bikin murnar cika shekaru 120 da haihuwar Chen Yun, taron da ya gudana a babban dakin taruwar jama’a dake tsakiyar birnin Beijing Shugaban na Sin ya ce, an haifi Chen a shekarar 1905, ya kuma shiga JKS a shekarar 1925. Ya kuma kasance shahararren dan gwagwarmaya...
    Bayan hakan, Pogba ya kunce kwantiraginsa da Juventus a watan Nuwamban 2024, kuma tun watan Maris da ya gabata ya samu damar komawa fili domin shirya dawowarsa. Yanzu haka yana ci gaba da atisaye tare da fatan ƙulla sabuwar yarjejeniya da Monaco domin ci gaba da taka leda a ƙasarsa ta haihuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Farashin Man Fetur ya tashi a kasuwar duniya bayan harin da Isra’ila ta kai wa Iran, lamarin da ya tayar da hankalin masu zuba jari. Ana fargabar cewa rikicin da ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin ƙasashen biyu zai iya kawo tangarɗa wajen samar da man fetur daga yankin Gabas ta Tsakiya. An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Wani muhimmin wurin da ake safarar man fetur na duniya, wato mashigar Hormuz da ke kusa da Iran na da matuƙar tasiri, domin kashi ɗaya cikin biyar na dukkanin man da ake fitarwa daga nan ne ake bi da shi. Amma duk da haka, kasuwannin hannun jari sun fuskanci faɗuwar...
    Ya yabawa hukumar bisa yadda ta aiwatar da dokar da ta ba da damar, ‘Dokar Ci Gaban Man Fetur da Gas ta Nijeriya (NOGICD) ta 2010. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kafofin yada labarai na kasa da kasa na matukar zura ido kan taron farko na tsarin tattaunawa game da tattalin arziki da cinikayyar Sin da Amurka da aka gudanar tsakanin ranekun 9 zuwa 10 ga watan nan da muke ciki a London na kasar Burtaniya. An yi muhimmin shawarwarin ne kan matsaya daya bisa manyan tsare-tsaren da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ran 5 ga watan nan. A wadannan raneku 2, wakilan Sin da Amurka sun yi mu’ammala mai zurfi cikin sahihanci, kuma sun amince da tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma ta wayar tarho da ba da tabbaci kan ci gaban da aka samu a yayin tattaunawar ciniki da tattalin arziki da aka gudanar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A sandiyyar harin da ‘yan sahayoniya su ka kawo wa Iran da asubahin yau, masana fasaahr Nukiliya da dama sun yi shahada. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambaci cewa: Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai tsohon shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran; Faridun Abbasi. Shugaban jami’ar Azad, Muhammad Mahdi Dahranji. Shugaban Kwalejin fasahar Nukiliya, Abdulhamid Minochehri. Hakan nan kuma Malamin fasahar Nukiliya Ahmda Riza Zulfiqar, sai mataimakin shugaban hukumar  makamashin Nukiliya Amir Husain Fiqhi.
    Hukumomin ’yan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na daƙile munanan laifuka a ƙasar. Na baya-bayan nan dai shi ne ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan bindigogi da alburusai a jihohin Delta da Katsina. Mulkin Tinubu ya fi kowane muni tun bayan dawowar mulkin farar hula — Dalung An kama ’yar Najeriya da laifin safarar ɗalibai 15 a Australia A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a jihar Katsina an samu gagarumar nasara a ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda haɗin gwiwar JTF...
    Jagoran juyin musulunci na Iran wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojan kasar Iran, ya nada sabbin kwamandoji da maye gurbinsu da wadanda su ka yi shahada. Bayan shahadar kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci Shahid Hussain Salami, da kuma  babban hshahid Muhammad Hussain Bakiri, sai Shahid Gulam Ali Rashid wanda shi ne kwamandan Bakirin soja na “Khatamul-Anbiya, jagoran juyin ya sanar da sunayen wadanda su ka maye gurbinsu. Birgediya Muhammad Pakphur shi ne wanda jagoran ya sanar a matsayin sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci, sai kuma  Manjo Janar Musawi a mastayin sabon kwamandan rundunar sojan kasar, yayin da aka nada janar Ali Shadmani a matsayin kwamandan Barikin soja na Khatamul-Anbiya.
    Kwamandan  sararin samaniya na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Janar Amir Ali Haji Zadeh yana cikin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar harin da sojojin HKI su ka kawo wa  da asubahin yau Juma’a. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto majiyar juyin juya halin musulunci ta Iran tana tabbatar da shahadar Janar  Amir Ali Haji Zadeh.
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya yi Allawadai da harin da HKI ta kai wa Iran, wanda ya bayyana shi da cewa; Yana da hatsarin gaske, kuma ‘yan sahayoniyar sun yi hakan ne bisa cikakken goyon bayan Amurka. Sheikh Na’im Kassim ya kuma bayyana cewa; Harin na ‘yan sahayoniya ba shi da wani dalili da ya wuce a rufe bakin gaskiya wanda yake taimakawa al’ummar Falasdinu a Gaza da ake yi wa kisan kiyashi, haka nan kuma taimakawa da goyon bayan gwgawarmayar Lebanon da dukkanin wannan yankin. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma kara da cewa; Wannan harin da wuce gona da irin za iyi tasiri mai girma a cikin wannan yankin, sannan ya kara...
    Sabon kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Birgadiya Muhammad Pakphur ya aike wa da jagoran juyin musulunci na Iran wasika da a ciki ya bayyana cewa: ” Laifukan ta’addanci da HKI ta aikata, wanda ya yi sanadiyyar shahadar manyan kwamandojin  da kuma  malaman Nukiliya, haka nan  mata da kananan yara da ba su ji ba su gani ba, ba zai wuce ba tare da mayar da martani ba.” Bugu da kari sabon kwamandan dakarun kare juyin musuluncin ya ce; Ba da jimawa ba, Za a buwa wa wannan haramtacciyar kasa kofofin jahannama.” Birgeriya Muhamad Pakphur ya kuma kaddamar da ta’aziyya da kuma taya murnar shahadar kwamandojin, ya kuma yi godiya ga jagora da ya gaskata dakarun juyin....
    Da yake maida martani, Mokwa ya ce gwamanti ta fara biyan bashin tallafin rage radadin ga ma’aikata. Ya ce za a ci gaba da biyan kudin ne kashi-kashi har zuwa nan da watanni hudu masu zuwa. “Mun fara biyan bashin nira 35,000 ga ma’aikata. Illar kawai wasu ma’aikatu da suka kasance masu cin kashin kansu da suke biyan tallafin kai tsaye, misali, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa. “Amincewa da tallafin naira 35,000 ga ma’aikata shi ne mafita ta wucin gadi da gwamnatin tarayya ta yi kafin amincewa da mafi karancin albashi na naira 70,000. “Wannan ya faru a cikin watanni biyar, amma kungiyar kwadago ta ce ba a fara biya a kan lokaci ba, yanzu kenan akwai bashin...
    Rundunar ’yan sandan ƙasar Australia ta kama wata ’yar asalin Najeriya da ke ƙasar Australia, Binta Abubakar bisa zarginta da safarar ɗalibai daga ƙasar Papua New Guinea tare da tilasta musu yin aikin da ba a biya a gonaki a faɗin jihar Ƙueensland da sunan bayar da tallafin karatu. Binta mai shekara 56, an kama ta ne a ranar Laraba a filin jirgin saman Brisbane a lokacin da ta isa ƙasar Papua New Guinea, inda take zaune. Ambaliyar Mokwa: An sake gano gawar mutum bayan kwanaki 8 Abin da muke da shi a Najeriya ba cikakkiyar dimokuraɗiyya ba ce — Fayemi Kamen nata ya biyo bayan wani bincike na tsawon shekaru biyu da ƙungiyar masu fataucin bil-Adama ta AFP ta...
    Gabanin tafiyar shugaban kasar Sin Xi Jinping birnin Astana na kasar Kazakhstan, inda zai halarci taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu, an kaddamar da bikin gabatar da jerin shirye-shiryen shirye-shiryen telebijin da fina-finai, na babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG na shekarar 2025 a birnin Astana. Za a gabatar da shirye-shiryen CMG guda 12, ciki har da alakar dake tsakanin shugaba Xi Jinping da al’adun kasar Sin, da hanyar zamanintar da kasa mai salon kasar Sin na musamman da sauransu, a manyan kafofin watsa labaru na kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan, da Uzbekistan da dai sauransu. Shugaban gidan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, a ta bakin...
    Yayin taron shekara-shekara na tattaunawar CBD na shekarar 2025 da aka rufe a yau Juma’a 13 ga wata, mashawarci kana kwararre a hukumar kasuwancin kasar Sin ta kasar Birtaniya, kuma shugaban cibiyar bunkasa kasuwanci tsakanin Birtaniya da Sin mista John Mclean, ya bayyana yayin da yake hira da wakilin CMG cewa, kasuwar kasar Sin tana cike da damammaki, don haka dole ne ya shiga a dama da shi a cikinta. A ganinsa, yayin da ake tinkarar tashe-tashen hankula da rashin tabbaci a duniya, babbar baiwar da Sin take da ita, da muhalli mai aminci da bude kofa ga kowa, sun samarwa kamfanonin Birtaniya da ma duniya baki daya damammaki. Tun bayan kafuwarsa a shekarar 2000 zuwa yanzu, taron ya kasance...
    Ya ce Jihar Kurus Ribas ita ce ta farko a yankin kudu da ta shiga a dama da ita a harkar noman alkama, lamarin da ke nuni da gayar nasara wajen samar da abinci a kowani sassa na kasar nan. Kyari ya kara da cewa shirin rabar da takin zamani ya taimaka wajen bunkasa samar da shinkafa zuwa tan 58,000, lamarin da ya bai wa gwamnatin tarayya sanya tallafi a bangaren rabar da shinkafa ga jihohin da ambaliyar ruwa ta shafa. Ministan ya ce akwai bukatar kare masu amfani da kuma kayan da ake nomawa, “kaso 80 cikin 100 na abincinmu manoman cikin gida ne suka samar da su.” A daidai gabar da ake hasashen adadin ‘yan Nijeriya zai kai...
    Rundunar Ƴanandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane. An kama Yau, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara. Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane. CSP Ahmed Wakil, kakakin rundunar, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki. Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da...
    A cewarsa, dukkanin takardar neman kirkirar sabon masarauta ko sarki ko gunduma dole ne a aike zuwa addireshin gwamnan jihar ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatar kananan hukumomi da kula da masarautu na jihar. Kazalika, ya ce dole ne masu nema su gabatar da takaitaccen tarihin al’ummar da suke nema wa masarauta ko sarki ko gudunmawa tare da tarihin masarautar ko sarki ko gundumar da ke yankin da suke neman fita daga ciki. Sanarwar ta kuma nemi a sanya dukkanin wani muhimmin bayanin da aka san zai iya taimakawa wajen la’akari da bukatar masu nema. Har ila yau, sanarwar ta ce dole ne a takardar neman a samu sahihin sanya hannun hakimi, sarakunam kauye, da shugabannin al’umma tare da tabbacin wannan...
    Rundunar Ƴansandan Nijeriya, tare da haɗin gwuiwar sauran hukumomin tsaro, ta samu nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ceto mutane 11 da aka sace a jihohin Delta da Katsina. Wannan na cikin ƙoƙarin ci gaba da yaƙi da miyagun laifuka a faɗin ƙasa. A jihar Katsina, an daƙile wani yunƙurin garkuwa da mutane a ranar 8 ga Yuni, 2025, a hanyar Danmusa zuwa Mara Dangeza, inda jami’an haɗin gwuiwa suka yi artabu da ‘yan bindiga. Bayan musayar wuta mai tsanani, jami’an suka tilasta masu laifin guduwa da raunukan harbi tare da kuɓutar da mutum 11 da suka sace ba tare da raunuka ba. Yanzu-yanzu: Gwamnan Delta Oborevwori Ya Fice Daga PDP Zuwa APC...
    Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zargin da wasu ke yi cewa ta karɓo sabon bashi na dala miliyan 6.6 daga watan Yuni zuwa Disamba 2023, tana mai cewa wannan zargi ƙarya ne marar tushe da aka ƙirƙira domin ɓata mata suna. Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiyar siyasa mai suna APC Patriotic Volunteers ta yi zargin cewa gwamnatin NNPP mai ci a jihar ta karɓo bashi daga ƙasashen waje ba tare da bayyana hakan ba. Darakta Janar na Ofishin Gudanar da Basussuka a jihar, Dr. Hamisu Sadi Ali, ya bayyana cewa tun daga lokacin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta hau mulki, ba ta karɓi wani sabon bashi ko na gida ko na waje ba, balle a ɓoye shi...
    Ya umurci jami’an tsaro su gaggauta kai dauki ba tare da bata lokaci ba don tabbatar da an gurfanar da masu laifin a gaban kuliya, yana mai jaddada cewa za a hukunta duk wanda aka samu dauke da muggan makamai ko kuma aka samu yana da hannu wajen aikata laifuka. “Ga iyalai da ‘yan uwa da masoyan marigayi Ahmed, ina mika sakon ta’aziyyata, da na gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, kuma muna jimami tare da ku, ina ba ku tabbacin za a yi adalci. “Ina kuma kira ga jami’an tsaro su kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da kuma sintiri kan tituna, musamman a wuraren da ke fuskantar irin wadannan laifuka. Jama’armu sun cancanci tafiya cikin walwala ba tare da...
    An shiga yanayin zaman dar-dar a yankin Gabas ta Tsakiya bayan wasu munana hare-hare da Isra’ila ta kaddamar a kan tashoshin Nukiliya da manyan sojojin Iran a ranar Alhamis. Hukumomin Isra’ila dai sun tabbatar da kai harin inda suka ce ya kunshi daruruwan jirage kan abin da suka kira da kololuwar wurin hada makaman Nukiliya na Iran da kuma manyan sojojinta. NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna Daga cikin manyan mutanen da ake zargin harin ya hallaka har da Manjo-Janar Hossein Salami, Shugaban Rundunar IRGC ta Iran da wasu manyan kwamandoji da manyan masana a tashar Nukiliyar. Rundunar...
    Ya kuma tuna irin muhimmiyar rawar da Majalisar tarayya ta taka a lokuta masu sarƙaƙiya a tarihin Nijeriya, ciki har da daƙile shirin ƙara wa’adi na uku da kuma kafa “Dokar Bukata” lokacin rasuwar tsohon shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da cewa, yanayin zafi ya yawaita a kasar ta Saudiyya, yayin gudanar da aikin Hajjin 2025, koda-yake; akasarin wadanda suka mutu daga Nijeriyar tsofaffi ne. Rasuwar farko da aka sanar ta wani Alhaji ce daga Jihar Oyo, Alhaji Sulaimon Hamzat, wanda ya rasu a ranar 17 ga Mayun 2025 a kasar ta Saudiyya. Na biye da shi kuma daga Jihar Abiya ne, mai suna Alhaji Saleh, Shugaban Kasuwar Shanu ta Lokpanta, wanda ya rasu a garin Makka a daren ranar Litinin 26 ga watan Mayun 2025. Bayan haka kuma, sai wata Hajiya mai shekaru 75 daga Jattu Uzairue a Karamar Hukumar Etsako ta yamma da ke Jihar Edo, Adizatu Dazumi, wadda ta mutu a ranar Litinin 26 ga Mayun...
    Sai dai, ya sanar da cewa, ya janye kurin ne, bayan ya tuntubi daidaikun mutane da sauran kungiyoyi a daukacin fadin kasar. Halin girma da dakkun da Shugaba Abba ya nuna na janye wannan kurin bayan korafe-korafen alummar asar kasar, babu shakka janyewar abu ne, da ya dace, musamman duba da cewa, tursawa ‘yan kasa a tsarin Dimokiradiyya abu ne da bai dace ba, domin kuwa a tsarin dimokiradyya ana bai wa ‘yan zabin abinda zuke bukata, wanda hakan ya sabawa batun tilasta masu yin zabe. Bugu da kari, batun fitar jama’a yin zabe, abu ne da ake bukatar a rinka wayar da kan ‘yan kasa da nuna masu amincewa, amma bai wai ace za a tilasata su, yin zaben...
    Ya kammala da cewa, “Gwamnatin ta yi amfani da kuɗaɗe da yawa fiye da gwamnatocin Yar’Adua, Jonathan, da Buhari jimilla, amma babu wani cigaba da aka samu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hadisin Aikin Hajjin Annabi (SAW) ya koyar da cewa sumbantar Hajrul As’wad yayin da aka shiga Ka’aba da kuma sake sumbantarsa yayin fita sunnah ce, amma idan mutum bai samu iko ba; ya yi sumbar ta hanyar nuni da hannu. Hadisin ya kuma nuna mutum zai je ya yi Safa da Marwa. Zai fara da Safa kamar yadda Annabi (SAW) ya yi. Mutum zai hau kan Safa har sai ya ga dutsen, da yake sun rufe shi da gilashi sai a matsa kusa da shi. Idan ya yiwu sai a kalli Ka’aba a ambaci Allah, sannan a yi addu’a. Za a maimaita haka sau uku. Idan mutum ya iya, ya ce “Subhanallahi wal-Hamdulillah wa La’ilaha’illallahu wal-Lahu akbar. La’ilaha’illallahu wahdahu lashariyka...
    Tsarin yanayin masana’antu na Masar yana bunkasa kan fitar da kayayyaki zuwa Turai da Gabas ta Tsakiya. Tare da kasancewa mai karfi a cikin sinadarai, siminti, da kantin magani, Masar ta sanya kanta a matsayin jagorar masana’antun nahiyar da ke goyan bayan gyare-gyaren masana’antu. An san kasar da samar da siminti, yadudduka, magunguna, da sinadarin man fetur da sauransu. Sai kuma kasar Nijeriya mai rike da kambu na uku wacce ta kasance mai samun habaka a bangaren kasuwanci da masana’antu. Kamfanonin Dangote, musamman matatarsa da kuma rukunin kamfanonin BUA sun taimaka wa kasar wajen jan ragamar a bangaren masana’antu. Manyan masana’antun kasar nan sun hada da na siminti, kayayyakin mabukata, abinci da abin sha, da tace mai, wanda manyan masana’antun...
    Bayan harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai kasarmu, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya aike da sako ga al’ummar Iran. Ga sakon kamar haka Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai Al’ummar Iran masu daraja! Gwamnatin yahudawan sahyoniya ta hanyar aikata wani laifi da sanyin safiyar yau, ta sake bayyana munanan dabi’arta da fasadi. Ta hanyar kai hari dole ne wannan ya fuskanci hukunci mai tsanani. A wannan harin makiya, kwamandoji da masana kimiyya da dama sun yi shahada. Wadanda suka gaje su kuma da abokan aikinsu za su ci gaba da aiki nan take akan wannan tafarki, godiya ta tabbata ga Allah. Ta hanyar wannan danyen aiki, gwamnatin Sahayoniya ta kaddara akan ta cewa...
    A cewar Bawa, gwamnatocin da a karkashinsu aka wawashe dukiyar kasa, su ne na Mulkin Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo (daga 1999 zuwa 2006), sai Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua (daga 2007 zuwa 2009), kazalika a mulkin Shugaba Goodluck Jonathan daga (2010 zuwa 2014), sai kuma mulkin Muhammadu Buhari (daga 2015 zuwa 2023). Wadannan bayanai na kunshe cikin littafin, ‘The Shadow Of Loot and Loss – Uncobering Nigeria’s Petrol Subsidy Fraud,’ wanda tsohon sarkin yaki da cin hanci da rashawa ya rubuta. Alkaluman da Bawa ya bayyana daga cikin gwamnatocin hudu, shugaba Buhari ne ke kan gaba wajen biyan tallafin da ake ta cece-kuce akai na Naira tiriliyan 11, sai kuma na Jonathan wanda ya kashe Naira tiriliyan 3.9. Gwamnatin...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun sanar a cikin wani sako mai cike da alhini da shahadar Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun IRGC wanda ya yi shahada da asubahin ranar Juma’ar nan yayin wani hari na ta’addanci” da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan hedkwatar rundunar. Hukumar soji tana jinjinawa wannan babban kwamandan da aka gabatar a matsayin babban jigo wajen kare manufofin juyin juya halin Musulunci na Iran, tare da yin alkawarin mayar da martani mai tsauri ga makiya. Ga yadda sanarwar IRGC ta kasance : Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai A cikin bakin ciki da radadi muna sanar da shahadar Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci,...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta ce mayar da martani ga gwamnatin Isra’ila hakki ne na shari’a ga Iran kamar yadda doka ta 51 ta kundin tsarin mulkin MDD ta tanada. Da farko dai ma’aikatar ta mika ta’aziyyar shahadar wasu kwamandoji da jami’an kasar Iran a harin da Isra’ila ta kai wa kasar. “Hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai wa Iran sun sabawa doka ta 4 sakin layi na 2 na kundin tsarin mulkin majalisar dinkin duniya a matsayin wani mataki na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma Iran tana da hakki na shari’a na halal ta mayar da martani kan wannan zalunci kamar yadda yake a cikin sashe na 51 na kundin tsarin mulkin majalisar...
    Wani mummunan hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Zariya ya yi sanadin mutuwar mutum takwas ’yan gida daya, yayin da wasu mutum biyu ke can kwance a asibiti rai a hannun Allah. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Litinin a garin Barakallahu da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, ana tsaka da bukukuwan Babbar Sallah. A cewar rahotannin, lamarin ya faru ne lokacin da wata mota da ke tsala gudu ta kwace sannan ta danne mutanen da ke tsaye a gefen hanya bayan dawowarsu daga yawon sallah. Sojoji sun kashe kasurguman ’yan bindiga 3 a Zamfara Mutum ɗaya ya tsira da ransa cikin 242 a hatsarin jirgin India A cewar mahaifin mamatan,...
    Isra’ila ta kaddamar da hare hare kan wasu gine-gine da cibiyoyi a sassa daban daban na Iran ciki har da Tehran babban birni a cikin daren jiya wayewar wannan safiya ta Juma’a. Kafofin yada labarai na Iran sun ce akwai mata da yara da dama daga cikin wadanda suka yi shahada a hare-haren. An kuma bayar da rahoton kai hari a wurare a Natanz, Khorramabad, da Khondab, da dai sauransu. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce harin da Isra’ila ta kai wa Iran zai kai tsawon kwanaki idab akwai bukatar hakan. “Za a ci gaba da gudanar da wannan aiki na tsawon kwanaki kamar yadda ake tsara don kawar da wannan barazanar,” in ji Netanyahu a cikin wata sanarwa ta...
    Zuzzurfar tattaunawa da ta wakana tsakanin tsagin Sin da na Amurka a birnin Landan, ta sa masu bayyana ra’ayoyin jin karfin gwiwa game da makomar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Kuri’un jin ra’ayin jama’a na kafar CGTN ta kasar Sin, sun nuna yadda masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, shawarwari sun nuna kyakkyawan fata game da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin tattaunawar da suka yi ta wayar tarho, tare da sassauta sabani a batutuwan tattalin arziki da cinikayya tsakanin sassan biyu. Yayin kuri’un jin ra’ayoyin, masu bayyana mahanga sun goyi bayan matsayar Sin, inda kaso 87.1 bisa dari suka amince cewa ba wani batu na wa ya yi nasara, ko wanda...
      Sai dai kuma shugaba Tinubu ya yi amfani da wannan damar wajen yi wa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas ado da lambar yabo ta GCON, yayin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, da lambar yabo ta CFR.   Ga cikakken jerin sunayen sabbin mutane 67 da aka karrama da lambar yabon, kamar yadda fadar shugaban kasa ta fitar:   Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).   Shehu Musa Yar’Adua Rt Hon Tajudeen Abbas Senator Godswill Akpabio Wole Soyinka   Commander of the Order of the Niger (CON) Ghali Umar Na’Abba Salisu Buhari Umaru Dikko Uche Chukwumerije Bala Mohammed Gwagwarwa Aisha Yesufu Innocent Chukwuma...
    Da yake nasa jawabin, Sangare ya ce, Nijar na bin manufar Sin daya tak a duniya, kuma tana ba da fifiko ga hadin gwiwarta da kasar Sin, da mayar da hankali sosai kan harkokin tsaro, kana tana son kara amincewa da juna, da ci gaba da yin shawarwari bisa mutunta juna a tsakaninsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jirgin saman fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Landan wanda ya yi hatsari a birnin Ahmedabad na Indiya a ranar Alhamis. Mutum ɗaya ne ya tsira daga cikin mutane 242 da ke cikin jirgin, tare da fasa gine-ginen likitoci da iyalansu. Wani ɗan jarida na AFP ya ga gawarwakin da aka zaƙulo daga wurin da jirgin ya faɗi, da kuma bayan jirgin ƙirar Boeing 787-8 Dreamliner a rataye a gefen wani gini da ya rutsa da shi a lokacin cin abinci. Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu An ciro gawarwaki sama da 200 daga jirgin Indiya da ya yi hatsari “Iftila’in da ya afku a Ahmedabad ya ba mu mamaki da kuma ɓacin...
    Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray a wannan Alhamis din ta sanar da daukar dan wasan Jamus, Leroy Sane daga Bayern Munich. Kungiyar ta Turkiyya ta dauki dan wasan ne kyauta bayan kwantaraginsa ya kare a Munich. Mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu — Tinubu Ƙwazo da juriya suka sa na zura ƙwallaye 10 a wasanni 10 – Mane Sane mai shekaru 29 ya rattaba hannu kan kwantaragin shekaru uku inda zai rika daukar albashin Yuro miliyan 9 — kwantankwacin Dala miliyan 10.4 — duk shekara kamar yadda kulob din bayyana. Sane ya buga wa kasarsa ta Jamus wasanni 70, inda kuma ya lashe kofunan Bundesliga guda hudu a Bayern Munich tun bayan raba gari da Manchester...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da zargin cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin mayar da Nijeriya kan tsarin ƙasa da ke kan tafarkin jam’iyya ɗaya a ƙarƙashin mulkinsa. Shugaban ya kore wannan zargin ne a yayin jawabin da ya yi na zagayowar Ranar Dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis. Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya Tinubu ya ce masu tunanin cewa APC na son mayar da Nijeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya, to tunanin nasu kuskure ne, kuma suna yin sa cikin ruɗani ne. Ya ce: “Tsarin jam’iyya ɗaya ba ya cikin manufofinmu. Kuma ba zai taɓa zama cikin manufofinmu ba.” Sai dai shugaban...
    Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu. Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu. Sai dai daga baya kotun ta ba da ranar sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2025 domin sauraron karar. Lauyan wanda ake tuhuma ya nemi a ba shi belin, wanda ICPC ba ta yi adawa da shi ba. Mai shari’a Iheabunke ya bayar da belinta a kan kudi naira miliyan 10, tare da mutane biyu da za su tsaya mata. Ya ce dole ne...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An sanar da tashin shi daga City kafin karshen kakar wasa ta bana, kuma De Bruyne ya yi bankwana da magoya baya a filin wasa na Etihad bayan wasansa na karshe a gida da suka buga da Bournemouth a watan Mayu, City ta yi kokarin cike gibin da De Bruyne ya bari, yayinda ta dauki yan wasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan da Rayan Cherki daga Lyon. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
    A wannan lokaci da wasu sassa ke kafa shingaye, GCI na gina gadoji. Manufar na kuma karfafa gwiwar tattaunawa, da gudanar da shawarwari tsakanin sassan duniya masu bambance-bambance, ta yadda za a kafa managarcin tsarin hadin kan bil’adama mai dorewa. GCI da ranar tattaunawa tsakanin wayewar kan kasa da kasa ta MDD, za su kara zamewa duniya muhimman manufofi na “tafiya tare a tsira tare”!(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban baturen ’yan sanda na birnin Ahmedabad da ke ƙasar Indiya ya bayyana cewa, an ciro gawar mutane sama da 200 na fasinjojin jirgin Air India da ya yi hatsari a yau Alhamis. Babban jami’in ɗan sandan ya bayyana hakan ne a matsayin bayani na baya-bayan nan kan hatsarin jirgin, wanda ya rikito ƙasa jim kadan bayan tashi, kan hanyarsa ta zuwa birnin London na Birtaniya. Ranar Dimokuraɗiyya: Gwaman Zulum ya yi wa fursunoni 66 afuwa 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya Shugaban hukumar kula da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce jirgin na ɗauke ne da mutum 242, kuma akasarinsu Indiyawa ne. Fasinjojin jirgin Indiya da yawa sun mutu a hatsarin A cewar Kamfanin Dillancin Labarai...
    Da yake tuna tarihin siyasarsa a matsayin daya daga cikin gwamnonin adawa a farkon shekarun 2000, Tinubu ya sake jaddada matsayinsa a matsayin mai kare dimokradiyyar jam’iyyun adawa.   Ya kuma mika godiyarsa ga magabacinsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa yadda ya fahimci tare da gyara abin da ya bayyana a matsayin “kuskuren zaben 1993,” wanda aka yi imani da cewa, Cif Moshood Abiola da Alhaji Babagana Kingibe ne suka lashe amma gwamnatin soja ta soke zaben. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis ne aka bude bikin baje kolin hada-hadar tattalin arziki da cinikayya na Sin da Afirka karo na hudu a birnin Changsha fadar mulkin lardin Hunan, taron dake kara jaddada himmar kasar Sin ta fuskar karfafa alaka da nahiyar Afirka, nahiyar dake da mafiya yawan kasashe masu tasowa a duniya baki daya. Kusan kamfanonin Sin da na kasashen Afirka 4,700, da sama da mahalarta 30,000 ne za su halarci bikin na kwanaki hudu, wanda aka yiwa taken “Sin da Afirka: Tunkarar zamanantarwa tare.” Rahotanni daga mashirya bikin na cewa, kwarya-kwaryar darajar ayyukan hadin gwiwa da aka amincewa sun haura dalar Amurka biliyan 11. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci bikin bude baje kolin, inda kuma...
    A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne...
    Ministan yakin Isra’ila, Israel Katz, ya umarci sojojin kasar da su hana ayarin motocin agaji na arewacin Afirka shiga yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya. A cikin wata sanarwa ofishin Katz ya umarci sojojin Isra’ila da su hana “masu fafatuka daga Masar shiga yankin Zirin Gaza. Katz bukaci “Hukumomin Masar dasu hana zuwan masu fafatukar a kan iyakar Masar da Isra’ila.” Ministan ya ya bayyana hakan a matsayin hadari ga jami’an tsaron Isra’ila na IDF.” Wannan dai na zuwa ne bayan ayarin motoci 100 da ya kunshi dubban masu fafatuka daga kasashen Morocco, Aljeriya, Tunisia, Libya da Masar, suka yunkuri anniyar wayar da kan al’ummar duniya kan matsalar jin kai a Gaza, da neman kawo karshen yakin kisan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi a India sun ce da yiwa a samu wanda ya tsira daga hatsarin jirgin samanAir India da ya faru a yau Alhamis. Jirgin samfarin Boeing 787 Dreamliner wanda ya tashi Ahmedabad zuwa birnin Landan ya yi hatsari jim kadan bayan tashinsa dauke da fasinjoji 242 da ma’aikatan jirgin inji kamfanin air India. Bayanan farko da kamfanin na Indiya ya fitar sun ce akwai, Indiyawa 169, ‘yan Burtaniya 53 da, ‘yan  Portugal 7 sai dan Canada guda a cikin jirgin. Kuma babu wanda ya tsira, a cewar shugaban ‘yan sandan Ahmedabad. Hukumomin India da na Ingila da Portigal duk sun jajanta game da mummunan hatsarin. Jami’an kashe gobara a arewa maso yammacin Indiya tun da farko sun shaidawa kamfanin dillancin...
    A yayin da ake tsaka da bikin Ranar Dimokradiyya a Najeriya, al’ummar jihar Gombe sun wayi gari da sabuwar dokar takaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe a duk faɗin jihar. Sanarwar da ta fito ne daga hannun Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Buhari Abdullahi, ranar Alhamis, a madadin kwamishinan ’yan sandan jihar Bello Yahaya. Sanarwar ta ce an kafa dokar ne don rage ayyukan ta’addanci a fadin jihar. Guguwa ta hallaka mutum 6, ta jikkata 30 a Taraba An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato  Kafa dokar na zuwa ne kwana uku bayan wasu matasa da ba a tantance su wane ne ba suka kashe...
    A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai  mataki na daya, da mai mataki na shida a cibiyar “Pardo.” Bayanin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da ta fito daga kwamitin alkalai na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa akan Iran. Bugu da kari, bayanin na Iran ya kuma ce; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran Manjo Janar Hussain Salami ya fada a yau Alhamis cewa; Abokan gaba suna yi mana barazana da yaki, sannan ya tabbatar da cewa a shirye suke su fuskanci duk abinda zai faru. Manjo janar Salami wanda ya gabatar da jawabi ga taron dakarun sa-kai na “Basiji a nan Tehran ya kuma kara da cewa;  Babu wani wuri komai zurfi da nisansa a HKI da ba mu tsinkayowa, idan kuwa aka ba mu umarni to za su yi nasara, mu Sanya abokin gaba ya yi nadama. A gefe daya ministan tsaron Iran ya bayyana cewa; Duk wani hari da ake tunanin kawo wa Iran, to kuwa zai fuskanci mayar da martani mai...
    Wata mummunar guguwa ta yi sanadin mutuwar mutum shida sannan ta jikkata wasu 30 a garin Garba-Chede da ke karamar hukumar Bali a jihar Taraba. A cewar wani mazaunin yankin wanda guguwar ta lalata wa gida mai suna Abubakar Dodo, an shafe shekaru masu yawa ba su ga irin ta ba a yankin saboda munin barnar da ta yi. Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato A cewarsa, ban da gidaje, guguwar ta kuma lalata makarantu da masallatai da coci-coci, sannan kayan abinci na miliyoyin Naira sun salwanta. Dagacin garin na Garba-Chede, Kaigama Maigandi, ya yi kira ga Gwamnan Jihar, Agbu Kefas, da ya taimaka wa...
    Majiyar tsaron kasar ta Kamaru sanar da cewa, da dama daga cikin sojojin kasar sun rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da kungiyar Bokoharam ta kai musu ta hanyar amfani da manyan bindigogi da kuma jirgin sama maras matuki akan iyaka da Najeriya. Majiyar ta ce an kai harin ne a yankin Sagami dake kusa da tafkin Chadi a gundumar Logun mai iyaka da kasar Najeriya. Ita dai kungiyar Bokoharam ta addabi kasashen Najeriya, Kamaru da kuma jamhuriyar Nijar. Yankun arewacin kasar ta Kamaru ya fara fuskantar kai hare-hare daga wannan kungiyar ne tun a 2014 wanda kuma har yanzu yana ci gaba da faruwa daga lokaci zuwa lokaci.
    Jami’in tafiyar da sha’anin Mulki a yankin Cape ya fada a jiya Laraba  cewa; An sami karuwar wadanda su ka rasa rayukansu ya karu zuwa 49. Shugaban tafiyar da sha’anin Mulki a yankin na garin Cape, Oscar Mobyan  ya bayyana haka ne a wani taron manema labaru,kamar yadda kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto. Wasu yankuna na kasar ta Afirka Ta Kudu sun fuskanci saukar ruwa kamar da bakin kwarya, haka nan kuma saukar kankara, da hakan ya sa aka shiga cikin yanayin sanyi mai tsanani da kuma yankewar wutar lantarki a wasu yankunan. Ambaliyar ruwan da aka samu a kusa da wata makaranta ya ja motar da take dauke da dalibai 13, da hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsu. Tuni...
    Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal. APC ta ƙaryata wannan zargi. Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa. Jam’iyyar APC ta ƙalubalanci Kaura da ya kawo hujjoji kan wannan zargi da kuma wasu mutane da aka sace a jihar, kamar satar ɗalibai mata 270 daga makarantar Government Girls Secondary School da ke Jangebe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, da kuma satar ɗaliban Kwalejin Noma da Kiwo da ke Bakura. APC ta jaddada cewa gwamnatin...
    Aƙalla mutum huɗu ciki har da jaririn wata tara aka kashe a wani hari da aka kai ƙauyen Nkiendowro da ke Ƙaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Mutanen da suka rasu sun haɗa da mata biyu da namiji ɗaya, wanda aka ce suna aikin jigilar kwashe tumatir daga ƙauyen zuwa kasuwar Farin-Gada da ke Jos lokacin da aka kai musu hari. Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato  Wasu mutum biyu kuma sun jikkata a harin, wanda yanzu haka suna karɓar magani a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba. Shugaban tsaron al’ummar Miango, Josiah Zongo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an...
    Haka kuma, ya taɓa zama mataimakin kocin Super Eagles lokacin da Jose Peseiro ke jan ragamar ‘yan wasan Nijeriya. A kakar bara ta NPFL, ya jagoranci Kano Pillars ta ƙare a matsayi na 9. Ko da yake Usman bai bayyana cikakken dalilin saukarsa ba, masu sharhi a wasan ƙwallon ƙafa na ganin matsin lamba daga magoya baya da rashin nasara sun taka rawa. Har yanzu, ƙungiyar ba ta fitar da sabuwar sanarwa kan wanda zai maye gurbinsa ba. Masu sha’awar wasan ƙwallon ƙafa a Kano na fatan za a kawo sabon kocin da zai dawo da martabar Pillars a wasannin gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
    Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta kama mutane 11 da ake zargi da aikata damfara a Intanet a Jihar Kaduna. Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargin ne a unguwannin Mahuta da Barnawa bayan samun sahihan bayanai game da ayyukansu na yaudara ta yanar gizo. Yadda Kasar Sin Ta Zo Da Sabon Salon Zamanantar Da Sashen Jigilar Kayayyaki Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Kaso Kusan 80% Sun Soki Musabbabin Barkewar Tarzoma A Amurka A lokacin da aka kama su, EFCC ta ƙwace wasu kayayyaki daga hannunsu da suka haɗa da mota ƙirar Mercedes Benz C300 mai launin baƙi, wayoyi 14, kwamfutoci guda biyu, iPad, na’urorin mifi guda...
    Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki. Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV. An kashe mutum 41 cikin mako ɗaya a Filato  Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali. Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji....
    Aƙalla mutum 41 aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai wa jama’a daban-daban a Jihar Filato cikin mako guda da ya gabata. Yankunan da aka kai wa hari sun haɗa da Bassa, Riyom, Bokkos da Ƙaramar Hukumar Mangu. Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Hakazalika, an ruwaito cewa ɗaruruwan mutane sun rasa matsugunansu, an kuma ƙone gidaje da ba a san adadinsu ba. Ɗaya daga cikin mafi munin hare-haren ya auku ne a ranar 8 ga watan Yuni, a ƙauyen Bauda da ke yankin Langai a Ƙaramar Hukumar Mangu. ’Yan bindiga sun shiga garin da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma gwagwarmayar da ta biyo baya, wasu masana na ganin har yanzu ba a kai ga amfanin da ake murad daga dimokuraɗiyyar ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Ko mene ne hujjar kowane ɓangare? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a wannan lokaci. Domin sauke...
    A cewarsa, gobarar na iya kasancewa ta samo asali ne daga wani gini da ke bayan gidan man. Rahotanni sun nuna cewa gobarar na iya tashi ne daga tankunan mai da ke ƙasa, kafin ta bazu zuwa cikin gidan man gaba ɗaya. Hukumar kashe gobara ta jihar ta yi gaggawar killace wajen domin hana cunkoso da tabbatar da tsaron jama’a yayin aikin kashe gobarar. Mai magana da yawun hukumar kashe gobarar, Shakiru Amodu, ya tabbatar da cewa an samu nasarar kashe gobarar kafin ta bazu zuwa gidajen da ke kusa. Kafin ƙarfe 6 na yamma, jami’an agajin gaggawa sun shawo kan lamarin gaba ɗaya, tare da killace yankin da abin ya shafa domin kaucewa wata barazana. Daga kanmu, magana...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalar Kwacen Waya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    JMI ta bayyana cewa zata yi amafani da hakkinta wanda doka ya bata na ficewa daga yarjeniyar NPT don sake farfado da takunkuman tattalin arziki na MDD a kan kasar. Jakadan kasar Iran a MDD, Amir Saeid Iravani ne ya bayyana haka a jiya Laraba. Kamfanin dillanbcin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Iravani yana fadar haka a wata wasika da ya rubutawa kwamitin tsaro na MDD a jiya. Ya kuma kara da cewa Iran zata yi amfani da dokokin da suka bada damar yin hakan. Kasashen Turai guda Uku jamusa Farana da Burtania suna son su yi amfani da damar da ake kira snap back don sake farfado da takunkuman MDD a kan kasar na yarjeniyar JCPOA. Ya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun yi maganar rikice-rikicen da ke faruwa a yankin da kuma hanyar warwaresu. Taron oslo na shekara shekara dai a wannan karon ya maida hankali ne kan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya da kuma hanyoyin da yakamata abi don rage halin da ake ciki a yankin. Musamman matsalar yaki da kima kissan kiyashin da ke faruwa a...
    Ministan tsaro na kasar Iran ya bayyana cewa sojojin kasar sun yi gwajin wani makami mai linzami wanda yake iya daukar abubuwan fashewa hart un biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Burgediya Janar Amir Nasirzade yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa . wannan gwajin sako ne ga gwamnatin Amurka da kawayenta. Idan wani ya dora mana yaki sai sun fi mu shan wahali. Don tare da wadannan shirye shiryen da kuke na kare kammu sai mun kori amurka daga yankin nan. Yace iran tana cikin fushi kan abinda yake faruwa a Gaza don haka duk wata dama da ta samu zata maida martanin da ya dace. Ministan ya bayyana haka ne a jiya Laraba...
    Ministan man fetur na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana cewa kasarsa zata ci gaba da saida danyen man fetur ga masu sayensa a kasashen waje duk tare da kokarin gwamnatin kasar Amurka na kara kuntatawa kasar a bangaren saida makamashin kasar ga kasashen waje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya laraba bayan taron majalisar ministocin kasar a nan Tehran. Ministan ta kara da cewa shirin Amurka na hana Iran saida danyen manta ga kasashen waje zai rugurguje kamar yadda ya rugurguje a baya. Y ace don mun rika mun gano kan zaren lalata duk wani shiri na hana mu saida danyin man ga masu sayan man kasar. Ministan ya bayyana...
    Ya ce ya fahimci haka ne bayan kallon wani shiri a talabijin inda ya ga wasu mutane na nuna rashin jin daɗi. Wike ya ce wannan baƙin ciki na su shi ne ke ba shi ƙwarin gwiwa. “Na ji wani irin abu a zuciyata, sai na kunna talabijin. A nan ne na gano cewa wasu na cikin baƙin ciki saboda abubuwan alheri da ake yi,” in ji shi. Ya ƙara da cewa: “Yanzu da na gane suna cikin baƙin ciki, zan ci gaba da sanya musu ƙarin ciwon zuciya. Farin cikinmu na ƙaruwa ne da jin haushinsu. Wannan shi ne sabon aikina na ci gaba da sa musu hawan jini.” Wike ya yi raha da cewa yayin da suke cikin...
    Wani ɗan ƙasar Indiya, Harpal Singh, ya rasa ransa bayan katangar rumbun ajiya ta kamfanin ATCO da ke Zariya ta rushe a kansa ranar Talata. Mutumin dai daya ne daga cikin ma’aikatan kamfanin da ke unguwar Cikaji a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Hajjin 2025: Jihohi 11 sun kashe N6.2bn wajen tallafa wa Alhazai Ana shirin mayar da rantsar da Shugaban Nijeriya zauren majalisa Wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyanawa Aminiya cewa Ba’indiyen ya gamu da ajalinsa ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren Talata, bayan tashin guguwa gabanin a fara ruwan sama. Ma’aikacin ya ce sai dai ba a san musabbabin rushewar katangar ba, sakamakon lokacin da lamarin ya faru ba lokacin...
    A Shenzhen dake kudancin Sin ma, ana amfani da jiragen marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya ta yadda hakan ke magance tsaikon da ake samu saboda cunkoson motoci a tituna da kuma taimakawa wajen ceto rayukan marasa lafiya da ke bukatar daukin gaggawa. Bugu da kari, an samar da tsarin sufurin jirage masu tafiya kusa da doron kasa a lardunan Jiangxi, Sichuan da Guangxi inda ake fuskantar dimbin kalubalen fadada hanyoyi saboda yanayin tsaunukansu. Tabbas, duka wadannan sun zo da wani irin sabon salo a duniya da kasashe za su yi koyi da kasar Sin wajen zamanantar da sha’anin jigilarsu. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin yi wa ‘yan kasa jawabi kai tsaye da aka shirya gudanarwar tun farko a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, domin tunawa da cikar ranar dimokradiyyar Nijeriya shekaru 26. A maimakon haka, zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar. An bayyana sauyin ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ofishin SGF, Segun Imohiosen ya fitar a ranar Laraba. Amma Duk da haka, sauran shirye-shiryen ranar Dimokradiyya za su ci gaba da gudana kamar yadda aka sanar a baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    A yau ne aka gudanar da taron ministoci masu daidaita ayyukan da aka amince, a gun taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, a birnin Changsha dake lardin Hunan na kasar Sin, inda ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci bikin kaddamar da taron, tare da karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana ministan harkokin wajen kasar Kongo Brazaville Jean-Claude Gakosso, ya karanta wasikar murnar bude bikin ta shugaban kasarsa Denis Sassou Nguesso. Taron ya samu halartar ministocin kasashe membobin kungiyar FOCAC, da wakilan kwamitin AU, da jakadun kasashen Afirka dake kasar Sin, wadanda adadinsu ya zarce 100. Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata Sin da Afirka su nuna goyon...
    Majalisar Dattawan Nijeriya ta bayyana shirin kafa dokar da za ta mayar da rantsar da shugaban kasar a kwaryar majalisar, maimakon yadda ake yi a dandalin taro na Eagle da ke tsakiyar birnin Abuja. DW ta ruwaito cewa ita dai Majalisar Dokokin Nijeriya ta 10 ta yi fice wajen dauko batutuwan da ke haifar da cece-kuce, kama daga yunkurin mayar da yin zabe ya zama dole da kuma hukunta duk wanda ya ci mutuncin taken Nijeriya sai kuma wannan batu na amfani da doka domin sauya tarihin da aka daura dambarsa tun a shekara ta 1999 da aka sake kafa dimokuradiyya a kasar. Tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka cikin shekaru uku masu zuwa — Bankin Duniya Dalilin da babu abin...
    Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai haɓaka ba tare da taɓarɓarewa nan da shekaru uku masu zuwa. Bankin ya yi hasashen haɓakar ma’aunin tattalin arzikin cikin gida, GDP da kashi 3.6 cikin 100 a shekarar 2025, sai kashi 3.7 a shekarar 2026 da kuma kashi 3.8 a shekarar 2027. Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci A cewar sabon rahoton tattalin arzikin duniya da Bankin ya fitar, ana sa ran za a tallafa wa matsakaicin lokaci na Nijeriya ta hanyar samar da ingantattun albarkatun mai, da gyare-gyaren da ake ci gaba da yi, da kuma farfado da ƙwarin gwiwar masu zuba jari....
    Tarzoma ta barke a sassan Amurka da dama, har ta kai shugaban kasar ya bayar da umarnin kama gwamna. An kuma jibge dubban sojoji a birnin Los Angeles, kamar dai yadda jaridar “The Mirror” ta bayyana. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta fitar, ya nuna kaso mai yawa na Amurkawa sun damu da yiwuwar barkewar yakin basasa a kasar. Sakamakon kuri’un jin ra’ayoyin ya nuna cewa, kaso 78.3 bisa dari na ganin a matsayin Amurka ta kasa da ta ginu bisa hadakar bakin haure, kuma a yanzu take aiwatar da akidun yaki da bakin haure, hakan ya saba wa matakan bunkasar kasar bisa tarihi, zai kuma illata alkiblar ci gabanta a nan gaba....
    Ƙungiya mai rajin kishin APC a Kano mai suna APC Patriotic Volunteers, ta ce shekaru biyun da jam’iyyar NNPP ta shafe tana mulkin jihar nakasu ne da ke nuna tsantsar rashin ƙwarewarta a gwamnatance. A taron da ta gudanar da manema labarai a Kano, ƙungiyar bisa jagorancin shugabanta Alhaji Usman Alhaji (Wazirin Gaya) ta ce nazarin da ta yi wa salon mulkin gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar mata da gazawarsa wajen haɓaka ɓangarori masu muhimmanci duk da makudan kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke bata, da kuma kudaden shiga na cikin gida da take samu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Amurka da China sun cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da ke kawo karshen zaman tankiyar da aka soma tsakanin kasashen biyu tun bayan hawan Donald Trump karagar mulki. Kasashen biyu sun cimma matsaya a kan kan cinikin wani rukini na ma’adinai da Chinar ke fitarwa, wadanda ake kira da sunan Terres Rares, wadanda ake yi amfani da shi wajen samar da lantarki da kuma makamashin da ake sabbintawa. An kashe mutum 15 a sabbin hare-hare a Filato Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m A baya a taron kasar Switzerland, Washington ta amince da rage haraji kan kayayyakin kasar China daga kashi 145 zuwa kashi 30 cikin 100, don musanya makamancin wannan mataki da Beijing ta...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ta sha bamban da majalisun da ke goyon bayan masu goyon baya masu laifi misalin masu kisan gilla a Gaza Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada a yau Laraba cewa: Matsayin majalisar shawarar Musulunci ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bambanta da kasashen duniya, kuma ya sha bamban da majalisar da ke goyon bayan zalunci, nuna wariya, banbance-banbancen ra’ayi da masu aikata laifuka irin su kisan gilla a Gaza. Yayin ganawarsa da mambobin majalisar shawarar Musulunci a ranar Laraba, Jagora ya yi la’akari da cewa: Majalisun dokokin duniya suna da kamanceceniya ta fuskar nauyi doka. Duk da haka, ya jaddada cewa ma’auni...
    Wani ganau mai suna Kespan Iliya wanda shi ma mazaunin unguwar ne ya shaida wa manema labarai cewa, ‘yan unguwar na cikin barci lokacin da ‘yan bindigar suka iso cikin shigar kwamandoji, inda suka rika harbe-harbe kan mazauna unguwar.   LEADERSHIP ta fahimci cewa, sama da gidaje 96 ne kuma aka kone a Gyenbwas, al’ummar gundumar Langai ta karamar hukumar Mangu a yayin harin.   Kokarin jin ta bakin jami’im yada labarai na rundunar ‘Operation Save Haven (OPSH)’, Manjo Samson Zhakom ya ci tura domin wayarsa a kashe take a lokacin rubuta wannan rahoto. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Inganta sinadarin Uranium da ɗage takunkumai na iya sa tattaunawar ta yi amfani Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta cewa: A bayyane yake cewa cimma yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya na dindindin na shirin makamashin nukiliyar Iran abu ne mai yiyuwa, kuma ana iya cimma shi cikin sauri. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya rubuta a shafinsa na Twitter game da sabon zagayen tattaunawa tsakanin Iran da Amurka da kuma matsayin Iran a kansu yana mai cewa: Shugaba Trump ya bayyana a lokacin da ya shiga fadar White House cewa ba lallai ne Iran ta mallaki makamin nukiliya ba, wannan matsayi ya yi daidai da akidar Iran...
    Rayukan aƙalla mutum 15 sun salwanta a wasu sabbin hare-haren da aka kai  wasu ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Mangu a Jihar Filato. Shugaban ƙaramar hukumar, Emmanuel Bala, ya shaida wa manema labarai cewa, a daren ranar Talata ce aka kashe mutum bakwai a kauyen Bwai sai kuma mutane takwas a kauyen Chinchim duk a ƙaramar hukumar ta Mangu. Mokwa: Zulum ya kai ziyarar jaje Neja, ya bayar da tallafin N300m Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Wannan lamari na daga cikin sabbin hare-hare da tashin hankali da ke ci gaba da faruwa a yankin a wannan makon tsakanin yan kabilar Mwaghavul da Fulani. Hare-hare daban-daban guda uku da suka faru a yankin ƙaramar hukumar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sake kunna ‘hanyar tayar da hankali’ zai gamu da martani mai ƙarfi na Iran Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Fitar da kudiri kan Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta yi ba zai shafi kudurin al’ummar Iran ba ko kuma ci gaban shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya. A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Iran a yammacin ranar Talata, Baqa’i ya yi la’akari da dukkanin rahotanni da kudurorin da suka shafi siyasa. Ya kuma kara da cewa Iran ba ta keta hurumin da ya rataya a wuyanta ba, kuma kasashen yammacin turai suna dora barazanarsu ne kan...
    Birnin Los Angeles na Amurka tana ci gaba da fuskantar tashe-tashe hankula kamar yadda zanga-zanga ta mamaye birnin An ayyana dokar ta-baci a birnin Los Angeles na Amurka yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin masu zanga-zanga da ‘yan sanda kan batun gwamnatin kasar kan batun neman murkushe bakin haure. Gwamnan California Gavin Newsom ya zargi shugaba Donald Trump da rura wutar zanga-zangar. Gavin Newsom ya dauki Trump a matsayin wani mai karya kundin tsarin mulki ta hanyar korar bakin haure da yawa ba tare da nuna bambanci ba, yana mai bayyana tura dakarun Marines da na National Guard a matsayin wani kara ruruta water tashin hankali na rashin hankali da zai kara tada zaune tsaye a birnin....
    Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, ya bukaci Amurka da ta warware takaddamar cinikayya da Sin ta hanyar tattaunawa, da hadin gwiwa da zai iya haifar da moriyar bai daya. He, ya ce Sin na jaddada burin ganin Amurka ta yi aiki da bangaren Sin, ta yadda za a martaba alkawura da matakai da aka amince, da nuna sahihanci wajen yin aiki tukuru, da aiwatar da gaskiya da kwazo wajen aiwatar da matsayar da aka cimma, ta yadda za a kai ga kare nasarorin da aka cimma ta hanyar shawarwari. He, ya yi tsokacin ne yayin taron farko na shawarwari game da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana a ranakun Litinin da Talata a birnin...
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna jiya Talata a Changsha, babban birnin lardin Hunan, da ministocin da suka hada da Musalia Mudavadi na Kenya da Yassine Fall ta Senegal da Mahmoud Thabit Kombo na Tanzania da Selma Ashipala-Musavyi ta Namibia da Phenyo Butale na Botswana da kuma Tete Antonio na Angola. Da yake ganawa da Musalia Mudavadi na Kenya, Wang Yi ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara Jihar Neja domin jajanta wa mutanen Mokwa da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa. Zulum ya kuma bayar da tallafin Naira miliyan 300 domin taimaka wa waɗanda iftila’in ya shafa. Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Zulum, ya ce Gwamnatin Borno ta kawo wannan taimako ne don tallafabwa gwamnatin Neja wajen rage raɗaɗin ambaliyar da ta kashe mutane da lalata dukiyoyi. Ya kuma buƙaci sauran gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi su haɗa kai don kare al’umma daga iftila’i da sauyin yanayi ke haddasawa. Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya nuna godiya bisa wannan...
    Yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Kongo Brazaville Denis Sassou Nguesso, sun aike da wasiku na taya murna ga taron ministocin kula da harkokin da suka shafi aiwatar da sakamakon taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, wato FOCAC, inda suka taya murnar bude taron. Cikin sakonsa, Xi Jinping ya jaddada cewa, a halin yanzu, yanayin kasa da kasa ya cika da sauye-sauye da hargitsi. Kuma kasar Sin ta dage wajen samar da sabbin damammaki ga duniya tare da sabbin nasarorin da aka samu na zamanantarwa iri ta kasar Sin, da samar da sabon kuzari ga kawayen kasashe masu tasowa na duniya kamar kasashen Afirka ta hanyar shiga a dama da su a...