Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Suna Shakku Kan Tsagaita Bude Wuta Zai Dore Da Isra’ila
Published: 29th, June 2025 GMT
Manjo Janar Mousawi ya bayyana cewa: Suna shakka da kokwanto kan gaskiyar tsagaita bude wuta shin za ta dore kuwa tsakaninsu da ‘yan sahayoniyya
Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Iran ya yi gargadin gazawar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai nuni da rashin kwarin gwiwa kan kudurin makiya na cika alkawuran da suka dauka.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Saudiyya Yarima Khalid bin Salman, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Seyyed Abdurrahim Mousawi ya bayyana cewa: Harin da yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kaddamar kan kasar Iran ya zo ne duk da kamewa da kai zuciya nesa da Iran take yi, kuma a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka.
Mousavi ya bayyana cewa: Wadannan gwamnatocin biyu sun sake tabbatar da rashin amincewarsu da duk wani tsari na kasa da kasa, kamar yadda aka nunawa duniya karara a tsawon kwanaki 12 na yakin.
Ya kara da cewa: “Ba su fara yakin ba, amma sun mayar da martani ne da dukkan karfinsu, duba da irin shakkun da suke da shi kan jajircewar da makiya suka yi, ciki har da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, amma Iran a shirye take ta kaddamar da wani muhimmin martani idan aka sake kai mata hari.”
A nasa bangaren, ministan tsaron Saudiyya Yarima Khalid bin Salman ya ce: “Ba wai kawai masarautar ta yi Allah-wadai da hare-haren ba ne, har ma ta yi kokarin kawo karshen yakin wuce gona da irin.” Haka nan kuma ya mika ta’aziyyarsa ga shahadar wasu kwamandojin sojojin Iran a yakin baya-bayan nan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988).
Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki.
Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100. Sannan sauran gawakin shahidan, wadanda aka ganosu a tsibirin Maimoon da Shalamce, an yi masu jana’iza a lardin Golestan, Qom, Fars, Sistan da Baluchestan, Ardabil, gabacin Azerbaijan da wasu wurare.
Wadannan shahidan sun yi shahada ne a ayyukan farmaki na Kheibar, Karbala-4, Karbala-5, da kuma Valfajr-1.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci