Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
Published: 2nd, July 2025 GMT
Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba, don tattaunawa kan yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai harin wuce gona da iri kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, cewa: Wannan farmakin da aka kai kan Iran, wani rauni ne ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da kuma nuna cewa dokar daji ta mamaye duniya, kuma wadanda ba su da karfi ba za su iya ci gaba da rayuwarsu ba lamarin da tuni al’ummar Iran suka fahimci hakan da kyau.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Nukiliya ta Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Irin Aniyar Da Gwamantinsa Ta Kudurta Wajen Kare Tsaron Kasa Da Al’ummarta
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sun kuduri aniyar kare kan iyakokin Iran da tsaron kasar da kuma al’ummarta
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: “Suna goyon bayan zaman lafiya, kuma ba su amince da yaki ba, amma a lokaci guda kuma, suna tabbatar da aniyarsu ta kare kan iyakokin Iran da tsaron kasarta da kuma al’ummarta.”
A yau, Laraba ne, Shugaban kasar Iran Pezeshkian ya wallafa wani rubutu a shafinsa na sadarwa, inda ya jaddada babban kudirin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na kare kan iyakokin kasar da tsaro da al’ummar kasar. Yana mai jaddada cewa: “A tushen al’adu da wayewar Iran, suna da gogewa da yawa wajen rage wahalhalun da mutane ke fuskanta.”
Shugaban ya kara da cewa: Iran na cike da kayan ado da kyau kuma gaskiya tana bayyana a kowane lungu da sako, a ko da yaushe suna neman gina gadoji ne tare da wasu, ba katanga ba.
A gefen taron Majalisar ministocin kasar, shugaba Pezeshkian ya ce: “A kwanakin nan tunaninsu ya fi karkata ne wajen magance matsalolin al’ummar kasa da kuma rage damuwarsu tare da jaddada wajibcin yin aiki tare a tsakanin al’ummar Iran don kaucewa jefa su cikin matsaloli; Ya kara da cewa: Al’ummar Iran sun nuna jajircewa da hadin kai wajen samar da alfahari da daukaka ga kansu, kuma sun yi nasarar dakile makircin makiya, kuma hakan ya cancanci a yaba musu.