2025-11-25@20:57:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 11945

«Matatar Dangote»:

    Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko.   A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi...
    Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari...
    Tashar Talabijin ta Press TV ta Iran ta kaddamar da sabon sashenta na harshen Hebrew don isa ga masu sauraro na Yaren Hebrew na duniya. Yanzu ana iya samun wannan sashen ta hanyar asusun X (@PresstvHebrew) da kuma tashar Telegram (@PresstvHebrew), kuma Za a kaddamar da cikakken shafin Intanet na tashar nan ba da jimawa...
    Adadin Falasdinawan da aka kashe a yakin kisan kare dangi na Isra’ila a Gaza na iya zama mafi girma fiye da yadda aka kiyasta a baya, in ji rahoton jaridar Die Zeit ta Jamus ta mako-mako. A bisa ga kiyasin masu binciken, tsakanin Falasdinawa 99,997 da 125,915 ne aka kashe a Gaza a cikin shekaru...
    Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu...
    ’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani...
    Rahotanni na cewa ’yan bindiga sun sace wasu mutum takwas a garin Biresawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano a daren jiya na Litinin. Wata majiyar da ta tabbatar da lamarin ta shaida wa Aminiya cewa maharan sun shiga garin tsakanin 11 na dare zuwa 12 na tsakar dare, inda suka yi awon...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan. Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a...
    Daga Musa kutama , kalaba Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da wat mai juna biyu da ƙananan yara Jihar Kwara. Maharan sun kai farmaki tare da sace mutanen ne a yankin Eruku da ke Ƙaramar Hukumar Ekiti da ke jihar. Ƙarin bayani na tafe…
    Gwamnonin jihohin  Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin. Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya....
    Hukumar da take kula da harkokin watsa labaru a kasar Mali ta sanar da dakatar da ayyukan wasu kafafen watsa labarun kasar Faransa biyu a cikin kasar. Wadannan kafafen watsa labarun dai su ne LCI da TF1 saboda zarginu da watsa gubatattun labaru akan matsalar makamashi da ake fama da ita. TF1 dai tashar talabijin...
    Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”. A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a...
    A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo...
    Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan harkokin ƙasashen duniya ya bayyana kasancewar al’ummar Iraki da sanin da ba a taɓa gani ba a zaɓen da aka yi kwanan nan a matsayin babban nasara da ba a taɓa gani ba a tarihin Iraki. Ali Akbar Velayati, Mai Ba da Shawara ga...
    Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin  ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani...
    Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin...
    Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa. Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta...
    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar. An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Sufeton ’Yan Sanda...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar...
    Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran...
    The Gaza Humanitarian Ffoundatin (GHF) a Gaza ta bada sanarwan kawo karshen ayyukanta a Gaza makonni 6 bayan an fara abinda suke kira tsagaita wuta a Gaza. Shafin yana gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya nakalto shugaban hukumar John Acree yana fadar haka ya kuma kara da cewa hukumar ta cimma manufar kafata...
    Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar...
    Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya...
    Gwamnonin jihohin kudu maso yammacin Najeriya sun bada sanarwan cewa lokacin kafa yansandan jihohi ya yi, har’ila yau dakuma karfafa kula da dazuzzukan kasar saboda magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar. Jaridar Daily Trust ta nakalto gwamnonin na fadar haka a jiya Litinin bayan taron gwamnonin shiyar kudu maso yammacin kasar da suka gudanar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 13 da rabi, da ya tashi daga Sada zuwa Danakari zuwa Unguwar Malam Kuda, zuwa Magina, a Karamar Hukumar Yankwashi ta jihar. A  jawabinsa wajen bikin kaddamarwar, Namadi ya bayyana kudirin gwamnatinsa na ci gaba da samar da muhimman...
    Gwamnatin Najeriya ta ce Amurka ta amince za ta ƙara faɗaɗa haɗin gwiwar tsaro tsakaninsu, wanda ya haɗa da samar da karin bayanan sirri, makamai da sauran kayan yaƙi, domin ƙarfafa yaƙi da ’yan ta’adda da ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya a ƙasar. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mashawarci na Musamman...
    Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon  na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar...
    Dubban ‘yan Tunisia ne suka fito zanga-zangar lumana a babban birnin kasar kan abin da suka kira rashin adalci da danniya na wannan gwamnatin, yayin da suke zargin Shugaba Kais Saied da mulkin kama karya. Zanga-zangar ta kasance wani babban al’amari ne a baya-bayan nan da ya mamaye wasu bangarori a kasar wanda ya shafi...
    Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin bakin wake a hedkwatar FC dake peshavar na kasar Pakistan da safiyar yau kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane 6, da ya hada da jamian tsaro 3 da kuma wasu guda 3 na daban, wannan shi ne hari mafi muni da aka kai kan jami’an tsaro a kasar Pakistan...
    Kakakin kungiyar Hamas yayi Tir da ci gaba da kai hare haren da Isra’ila ke yi a fadin yankin Gaza, yayi gargadin cewa wadannan matakai suna barazana sosai ga yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma tsakaninta da Isra’ila a kasar masar a watan Jiya. A cikin wani bayani da Hazem qassem yayi gargadin...
    Ƙungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da gaza kare yara kanana a fadin kasar, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da sace-sacen mutane da ake kai wa wasu makarantu a arewacin kasar. Amnesty ta ce ta na nuna damuwa akan yadda gwamnatin Najeriya ke kara nuna...
    Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya  yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen...
    Gwamnatin Jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun firamare, sakandare, da manyan makarantu—ciki har da Gwamnatin Tarayya da makarantu masu zaman kansu saboda matsalolin rashin tsaro da ke faruwa a faɗin ƙasar kan. Sanarwa da Jalaludeen Usman Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Bauchi, ya fitar ta ce, “Wannan shawara,...
    Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamred Shehu Sani, ya ce umarnin Shugaba Tinubu na janye ’yan sanda daga gadin manyan mutane zai iya zama magana kawai babu aiki. A daidai wannan lokaci na ƙara yawaitar rashin tsaro, Shugaba Tinubu ya ce yana sa ido sosai kan al’amuran tsaro a faɗin ƙasa tare da jajircewa wajen...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu...
    Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka.   Ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da...
    Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na...
    Daga Bello Wakili Gwamnatin Tarayya ta ce tattaunawa da tawagarta ta yi da jami’an Amurka ta kara karfafa huldar tsaro tsakanin kasashen biyu tare da bude sabbin hanyoyin hadin gwiwa domin kara kare ‘yan Najeriya. Tawagar, karkashin jagorancin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ta  gana da manyan jami’an Majalisar Dokokin...
    Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan...
    Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara ta sanya ranar 1 gawatan Disamba a matsayin wa’adin karshe na biyan kudin kujerar aikin Hajji na shekarar 2026, wanda ya kai sama da naira miliyan 7 da dubu 600. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya jaddada cewa babu...
    Mahukunta a tarayyar Nigeria sun sanar da cewa a tsakanin kananan yara 303 na makarantar Majami’ar Roman Katolika da aka sace a jihar Niger, 50 daga cikinsu sun gudu, sun kuma isa wurin iyalansu. Masu tafiyar da makarantar ne su ka sanar da hakan a jiya Lahadi tare da kara cewa shekarun yaran da su...
    Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen. Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce...
    Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara, Gwoza (Borno), bayan sun zarge su da yin shirka.   Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ƙungiyar kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar...
    Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah...
    A sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a jiya Lahadi ta ce; “A cikin dukkanin alfahari Hizbullah tana sanarwa da ‘yan gwgawarmaya da al’ummar Lebanon, shahadar babban kwamanda na jihadi Shahid Haisam Ali Tabtaba’i ( Sayyid Abu Ali) wanda ya yi shahada sanadiyyar harin wuce gona da iri na yaudara na Isra’ila a  yankin...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu...