Za a tono gawar tsohon Gwamna Alao-Akala domin gwajin jinin ’ya’yansa
Published: 28th, June 2025 GMT
Ana neman tono gawar tsohon Gwamnan Jihar Oyo, marigayi Otunba Christopher Adebayo Alao-Akala, domin yin gwajin jini (DNA) da nufin tantance halastattun ’ya’yansa da za su ci gadon dukiyar da ya bari.
Batun tono gawar ta kunno kai ne bayan taƙaddama ta yi tsami a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan a kan rabon gadonsa.
Babbar ’yar marigayin mai suna Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ce ta shigar da ƙara a gaban Mai Shari’a Taiwo na Babbar Kotun Jihar Oyo ta hannun lauyanta, Oladipo Olasope (SAN), inda ta roƙi kotun ta bayar da umarnin tono gawar mahaifin nasu daga kabarinsa domin yin gwajin ƙwayar halittarsa ga wasu mutane bakwai da ke iƙirarin cewa su ne halastattun ’ya’yan marigayin.
Uwargida Aderinto ta shigar da ƙarar ne bayan abin da ta kira barazanar da ’yan uwanta ke yi na neman cire sunanta daga cikin jerin halastattun ’ya’yan marigayin da za su gaje shi.
Bom ya kashe mutum hudu da raunata 21 a Yobe Sojoji sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a NejaA takardar ƙarar, ta bayyana cewa ɗaukar matakin tono gawar mahaifin nasu da yin gwajin jini ga ’yan uwan nata su bakwai, har da ita kanta, shi ne zai taimaka wajen tantance ainihin halastattun ’ya’yan
marigayin da suka cancanci cin gadon ɗimbin dukiyar da ya bari a ciki da wajen Nijeriya.
Tsohon Gwamna Otunba Adebayo-Alao Akala ya mutu ne cikin watan Janairu na shekarar 2022, inda aka binne shi a cikin watan Oktoban shekarar a wani ƙasaitaccen kabari da aka gina a harabar gidansa da ke mahaifarsa a garin Ogbomosho da ke jihar.
Dukiyoyin da tsohon gwamnan ya mutu ya bari da ’ya’yan nasa suke jayayya a kai, waɗanda Lauya Oladipo ya gabatar gaban kotun, sun haɗa da rukunin gidajen alfarma a biranen Ibadan da Legas da Abuja da kuma ƙasashen Amurka da Birtaniya da wani katafaren otel a ƙasar Ghana.
Sauran sun haɗa da motocin alfarma da maƙudan kuɗaɗe a bankuna daban-daban a Nijeriya da ƙasashen Amurka da Birtaniya.
Tushen rikicin rabon gadon Alao-AkalaAn fara wannan taƙaddama a tsakanin ’ya’yan tsohon gwamnan ne bayan da aka binne gawarsa a watan Oktoba na shekarar 2022.
Rikicin ya samo asali ne bayan mutum biyu daga cikin ’ya’yannsa masu suna Kemi Alao-Akala da Olamide Alabi suka samu izinin daga magatakardan kotun rabon gado na Jihar Oyo, ba tare da sani ko amincewar Uwargida Oluwatoyin Alao-Aderinto ba, a matsayinta na babbar ’ya ga marigayin.
Ta yi zargin cewa ’yan uwan nata sun kitsa lamarin ne da gangan ta bayan fage, kuma abin da suka yi ya saɓa wa dokokin rabon gado na Nijeriya. Don haka ta zargi ’yan uwan nata da neman yin kwanciyar magirbi a kan dukiyar da mahaifinsu ya bari.
A watan Agustan2023, Lauya Oladipo Olasope (SAN) ya yi zargi a cikin wata wasiƙa cewa, ƙoƙarin cire sunan Uwargida Oluwatoyin AlaoAderinto, a matsayinta na babbar ’yar Marigayi Adebayo Alao-Akala daga cikin jerin ’ya’yansa zai iya haifar da babbar ɓaraka da rabuwar kawunan wannan babban gida. Saboda haka ya nemi kotun ta hanzarta ɗaukar matakin biyan buƙatun wadda yake karewa, na tono gawar marigayin domin a kawo ƙarshen matsalar ɗungurungum.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adebayo Alao Akala dukiya gwajin jini Tono gawa
এছাড়াও পড়ুন:
Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.
Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.
A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.
A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.
Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.
Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci