2025-08-06@03:45:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1490
«da fara biyan»:
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya. Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina. A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa. Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yayin da ya rage kwanaki biyu a yi bikin bude gasar wasanni ta duniya karo na 12, shugaban kungiyar shirya wasanni ta duniya (IWGA) Jose Perurena Lopez, ya bayyana shirye shiryen da aka yi a Chengdu a matsayin wadanda suka zarci tunani, yana cewa abu ne da zai kafa tahiri. Perurena ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na Xinhua a yau Talata cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, yana da burika sosai kan gasar, amma yana ganin abun da aka shirya ya zarce tunaninsa. Ya ce suna da tabbacin birnin Chengdu zai gudanar da gasar wasanni mafi kyau a tarihi saboda ingancin wuraren wasa da na masu aikin sa kai da ma na kwamitin shirya gasar, na nuna matukar kwarewa....

Matakin Baiwa Kansa Hakuri Ba Zai Kawar Da Matsayin Gwamnatin Lai Ching-te Na Kasancewa ’Yar Dara A Hannun Amurka Ba
Wannan kuma ya tabbatar da cewa, gwamnatin Lai Ching-te a zahiri ‘yar dara ce a hannun Amurka, wadda za ta iya amfani ko watsi da ita. (Mai fassara Bilkisu Xin) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin. “Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya. Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar. A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya...
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya shirya da wani gagarumin biki domin karrama Nafisa Abdullah ’yar shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema ’yar shekara 15, wadandan ’yan asalin jihar ne, bayan sun lashe gasar duniya da aka gudanar da kasar Birtaniya. Nafisa ta lashe Gashar Iya Turanci ta Duniya a yayin da Rukayya ta lashe Gasar Muhawar ta duniya, inda suka doke kasashe 69 a Gasar TeenEagle na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan. Bayan doke dalibai sama da 20,000 da suka fafata a gasar inda suka wakilci Najeriya daga Kwalejin Nigerian Tulip (NTIC) da ke Jihar Yobe. Nafisa da Rukayya dukkansu sun ci gajiyar shirin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ya kunshi cikakken dawainiyar karatun...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Rasha tana shirin kara dankon zumunci da kungiyar Brics saboda fuskantar takunkuman tattalin arziki wadanda kasar Amurka ta daura mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Maria Zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, kungiyar BRICS kungiya ce wace kasar Rasha ta dogara da ita don magance irin wadannan matsaloli. Sannan kasashen iya magance takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suke dorawa kasar Rasha. Zakharova, ta kara da cewa kasashen Global south da BRICS sune kawayen Rasha a kan abinda ya mshafi matsalolin takunkuman tattalin arziki da kuma kawayenta a cikin harkokin siyasar duniya. Zakharova ta kara...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince kan cewa Burtaniya zata maida dukkan wadanda suka iso Burtaniya ta amfani da kananan kwale kwale ta maida su Faransa, a inda ita kuma faransa zata mikawa kasar Burtaniya masu nrman mafaka wadanda suke da iyali a kasar Burtaniya dai dai adadin da ta mayar daga Burtaniya. Firai ministan kasar Burtanita Keir Starmer da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel macron sun amince haka a cikin...
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya ta fara taron shekara-shekara karo na 19 na kimiyya da nufin yin amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi a fannin likitanci a kasar. Da yake yiwa manema labarai jawabi gabanin taron a Sokoto, shugaban kwalejin na kasa, Dokta Peter Ebeigbe ya ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi domin tunkarar manufofi aiwatarwa mai inganci da shigar da kamfanoni masu zaman kansu a fannin ilimin likitanci na gaba da digiri na biyu. Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, ana sa ran taron zai kuma tattauna kan ingancin aikace-aikacen kirkirariyar fasaha ta Artificial Intelligence (AI) da illolinsa na isar da sahihanci mai inganci. Shugaban na kasa ya...
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu. Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta. Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa...

Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen iskar gas na Amurka da kuma zuba jarin dala biliyan 3.3 a masana’antun Amurka a wata yarjejeniya da tawagar shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar. Wannan yunƙurin ya ci tura. Jami’an Afirka ta Kudu sun ce, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters, harajin Amurka zai iya janyo asarar dubunnan ayyuka, musamman a fannin noma da kera motoci. A wani taron manema labarai, ministocin ciniki da...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya. Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe....
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano, yana da tarihin shekaru 115. An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi. Hadimin gwamnan ya ce an yanke shawarar sauya ma’anar wurin,...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin. Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na da nufin inganta lafiyar mata da yara tare da rage mace-macen da za a iya kauce wa ta hanyar samar da dama ga ayyukan kiwon lafiya. Cibiyoyin lafiya a fadin karamar hukumar, ciki har da Asibitin Gwamnati na Gwarzo da Asibitin ‘Yar Kasuwa, sun bayar da rigakafi kyauta, shawarwari kan abinci mai gina jiki, kulawar haihuwa da sauran muhimman ayyuka na kiwon lafiya. Jami’in...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu? Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi Wata majiya daga dan garin Kagara wanda ya bayyana sunansa da Abubakar Sani ya shaidawa LEADERSHIP cewa ya rasa ‘yan uwansa guda biyu a harin wanda ya afku a ranar Asabar din da ta gabata. Ya ce, ‘yan fashin da suka yiwa kauyen su kawanya da...
Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015. Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar. A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar. Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025. Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji Saleh Abubakar, ya ce, “Kowane iri ƙwaya ɗaya na iya samar da miliyan 100 na dabino, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan ɗaya. Ga shi kuma sau biyu dabino ke yin ’ya’ya a shekara. “Muna hasashen manoma za su samar da Naira biliyan 300, wanda tabbas zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya,” in ji shi. Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba irin dabino miliyan...
Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace. An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas An ƙara hakimai 6 a Masarautar Katsina Bayan samun sahihan bayanai, sojoji da DSS suka fara bincike tare da ƙoƙarin ceto shi a wurare da dama, ciki har da Kente, Sondi 1 da 2, Yaku, da Warawa. A cewar Laftanar Umar Muhammed, mai magana da yawun rundunar, sojojin sun yi arangama da ’yan bindigar, inda suka yi musayar...
Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada. Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.” Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana...
“daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba. Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira. “Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar. Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya...
“Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba a fannin ilimi. To, kwatsam, sai wannan mataki ya samu tasgaro, yara ba su iya cin jarabawar WASC, zuwa makaranta ya yi ƙasa da ƙasa, ba a kula da malamai yadda ya kamata. Wasu makarantun ba su da malamai. Za ka ga makaranta mai yawan dalibai 300 tana da malami daya ko biyu, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba,”in ji shi. Ya ci gaba...
Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka zo ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen. Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin....
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Mai Martaba Shehun Bama, Dakta Umar ibn Kyari Umar El-Kanemi, ziyara a fadarsa da ke Bama. Ya ce an riga an kammala gina matsuguni 1,000 a Darajamal, sannan kuma aikin gina wasu a sauran garuruwan hudu. “Mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan gudun hijira gida. A Mayanti,...
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba. Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu. Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta...
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da barazanar kungiyoyin ta’addanci na ISIS da Al-Qaeda a nahiyar Afirka Wani sabon rahoto da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya suka fitar ya yi gargadin karuwar barazanar da kungiyoyin ‘yan ta’adda ke da alaka da ISIS da Al-Qaeda suka yi kan kasashen nahiyar Afirka. Rahoton ya yi nuni da cewa: Nahiyar Afirka na fuskantar karuwar barazanar ayyukan ta’addanci da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da wata gungun jama’a da take karkashin kungiyar al-Qaida ke ci gaba da fadada ikonta a arewacin Mali da Burkina Faso tare da samun ‘yancin kai, gami da samun goyon bayan ayyukan ci gaba da suka hada da jiragen sama marasa matuka ciki da nau’o’in makamai na zamani....
A yau Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Beijing ta sanar da cewa, an dawo da wutar lantarki da ayyukan sadarwa a dukkan kauyukan da ibtila’i ya shafa a fadin birnin na Beijing, biyo bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka, yayin da kuma ake ci gaba da aikin ceto wadanda suka bace. Ruwan sama da iska mai karfi da aka yi fama da shi daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da mutane tara suka bace, a babban birnin kasar, kamar yadda aka sanar a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin...
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa. Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki. Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin...
Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
Kungiyar wasan Taekwondo ta JMI kuma guragu, sun zama zakara a wasan taekwondo gurago sun lashe gasar ta Asia karo na 10 a jere. Kanfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto cewa an gudanar da gasar ne a kasar Malasiya, kuma yan wasa 107 ne daga kasashe 18 suka sami damar halattar gasar a ranar Jumma’an da ta gabata. Alireza Bakht da Mamed Haqshenas da kuma Marzieh Nasrollah sun sami lambobin Zinari sannan Saeed Sadeghianpour, Maryam Abdollahpour, da Amir mohammad Haghitshenas sune suka sami lambobin azurfa. A yayinda Aylar Jami, Leila Mirzaei, Mohammad Taha Hassanpour, Roza Ebrahimi, Leila Rahimi, da Mehdi Pourrahnama kuma suka sami lamabobin tagulla guda 6. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
A bisa ƙiyasin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya yi, ya ce; tumatirin da ake nomawa a shekara a Nijeriya, ya kai kimanin tan miliyan 1.701, wanda kuma ake amfani da shi a shekara ya kai aƙalla tan 2.93, inda wannan adadin ya nuna cewa; a shekara, ana samun ƙarancinsa da ya kai na kimanin tan miiyan miliyan 1.2, inda kuma a duk shekara ake cike giɓin da ake da shi na wanda ake shigo da shi kimanin na ƙalla dala biliyan 2.5. Wani ƙiyasi da kamfanin ‘Reportlinker’ ya gudanar ya ce, buƙatar tumatir a shekara , za ta ƙaru zuwa tan miliyan 3.01 a 2028. Jerin Manyan ƙalubalen da Ke Shafar Farashin Tumatir A Nijeriya: 1- Noman Tumatir...
Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da aka gabatar da ke tabbatar da wannan zargi, wanda hakan ya sa binciken ya tsaya. Kimanin wata biyar ke nan da Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai na Nijeriya suka fara bincike kan zargin, amma har yanzu babu wani sakamako ko rahoto. Aminiya ta gano cewa tun sama da shekara goma da suka wuce, ake zargin wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da...
daga ƙarshe, kwamitin ya tabbatar da cewa zai miƙa dukkan shawarwarin da al’ummar yankin suka bayar gaban Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Malam ɗikko Raɗda don daukar matakin da ya dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya “A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.” “Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan. Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar...
A cewar Adelabu, har yanzu dai wutar lantarki ne ƙashin bayan kamfanoni a Nijeriya da kuma tattalin arziki, ya nemi haɗin kan dukkanin wadanda lamarin ya shafa domin sake farfaɗo da sashin wutar lantarki yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa. Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.1 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul Hakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke...
Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan. “Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin. ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan...
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya Aikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba...
Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin. Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Hakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba. Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing. Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da...
Allah Ya yi wa Mai Martaba, Sarkin Gudi Alhaji Isa Bunuwo Ibn Khaji rasuwa a asibitin Nizameye da ke Abuja ranar Alhamis. Mai martaba Sarkin wanda ke garin Gadaka a Ƙaramar hukumar Fika cikin Jihar Yobe ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya. Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Sakataren masarautar Gudi da ke Gadaka ne ya tabbatar da rasuwar Sarkin, ya kuma ce an shirya gudanar da Sallar Jana’izar marigayi Sarkin a ranar Juma’a da ƙarfe 2:00 na rana a fadar Sarkin da ke Gadaka. Labarin rasuwar Sarkin dai ya tayar da hankalin a ɗaukacin al’ummar masarautar da ma Jihar Yobe...
Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni mai nazari ne, kuma ina nazarin ra’ayoyi, a jihohin Arewa Peter Obi a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP zai doke duk wani ɗan takara, saboda mutanenmu suna da gaskiya.” Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam Peter Obi ya fice daga Jam’iyyar PDP a watan Mayun 2022 inda ya jagoranci Jam’iyyar LP a...
Tawagar kananan yan wasan damben gargajiya na kasar Iran sun zama zakara a wasannin da aka gudanar a na wannan shekara ta 2025 tare da Zinari guda, azurfa guda da kuma Tagullah 4. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jami’an gasar wasan na damben gargajiya na kasar Iaran suna fadar haka a birnin Athen na kasar Girka. Sun kuma kara da cewa tawagar yan wasan zun zama zakara a wannan gasar ne duk da cewa mutum guda daga cikinsu bai shaga wasan ba. Labarin ya kara da cewa matasan kasar Iran sun kware a wammam wasan gargajiya, wanda ake kiransa damben Roma. Tawagar ta sami, zinari 1, azurfa 1 da Tagulla 4 , ta kuma sami maki...
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar. Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da...
Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external) Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external) Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro...
“Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi. A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa. Makabartar Jajeri Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa. Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas...
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati. Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno Bakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace. “Jihar Katsina na...
Adamu ya bayar da hujjar cewa, Sarkin Musulmi ne ke shugabantar daular gargajiya mafi girma a Arewacin Nijeriya, tare da dukkan sarakunan yankin karkashin jagorancinsa na ruhi da al’adu. Ya yaba da shugabancin Sarkin Musulmi Abubakar na tsaka-tsaki, samar da zaman lafiya, da jagoranci na hadin kai. Sun bayyana shi a matsayin mutum mai kishin kasa wanda ya yi namijin kokari wajen inganta tattaunawa tsakanin addinai da hadin kan kasa. Kungiyar ta yi kira ga Majalisar Dokoki ta kasa, da fadar shugaban kasa, da sauran al’ummar Nijeriya da su goyi bayan nadin, inda ta ce hakan zai karfafa cibiyoyin gargajiya da kuma samar da hadin kai a tsakanin sarakunan gargajiya a fadin kasar. Daga kanmu, magana...
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Olumode Samuel Adeyemi a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa. Sabon shugaban hukumar zai fara aiki a hukumance daga ranar 14 ga watan Agusta, 2025. Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno An sanar da wannan naɗin ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa da Hukumar CDCFIB, ta fitar, wacce sakatarenta, Abdulmalik Jibrin, ya rattaba wa hannu. Wannan naɗin na zuwa ne bayan da shugaban hukumar na yanzu, Injiniya Abdulganiyu Jaji Olola, ke shirin ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2025, bayan cika shekaru 60 a duniya. Olumode Samuel Adeyemi yana da ƙwarewa da gogewa a aikin...

Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Daraktan Kula da Yankin Arewa maso Yamma na Rediyon Najeriya, Mallam Buhari Auwalu, shi ne ya gabatar da tawagar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga iyalinsa, Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Yayin ziyarar, Daraktan Sashen Injiniya na Hedikwatar Rediyon Najeriya, Injiniya Sanda Askira, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin...
Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai. Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su. A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT. Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya,...
Kwamandan, Nigerian Defence Academy NDA, Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya bukaci dalibai da su jajirce wajen ganin sun samu nagartar ilimi. Manjo Janar Abdul Khalifa Ibrahim ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai da jawabai da kuma bayar da kyaututtuka da aka yi a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Malali Kaduna. Kwamandan NDA wanda tsohon dalibi ne a kwalejin ya bayyana jin dadinsa da yadda dalibai ke gudanar da ayyukansu ya yabawa mahukunta da ma’aikatan FGC Kaduna bisa yadda suke kiyaye ka’idoji. A nasa jawabin shugaban kungiyar tsofaffin dalibai ta FGC Kaduna, Kwamared Seyi Gambo ya ce kungiyar za ta ci gaba da bayar da gudummawar ta wajen daukaka darajar kwalejin ta hanyar daukar matakai na koyar...
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa. Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang Gwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya...
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar. Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi. Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu. Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka hada da yiwuwar gudanar da harkokin yada labarai, da nazarin yiwuwar bunkasa hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da hanyoyin yin tasiri a kafofin watsa labaru, da matakan hadin gwiwa don kara fahimtar ra’ayin jama’a a kasashen biyu. Bangarorin biyu sun yi tsokaci kan yadda kafafen yada labarai ke yada jita-jita da nufin yin zagon kasa ga dangantakar...

Birtaniya Ta Yi Barazanar Amincewa Da Kasar Falasdinu A Watan Satumba Idan Yanayin Gaza Bai Canza Ba
Fira ministan Birtaniya ya bayyana cewa: Za su amince da kasar Falasdinu a watan Satumba idan yanayin Gaza bai canza ba Keir Starmer ya kara da cewa, an dauki wannan matakin ne domin kare tsarin kasashe biyu, kuma kasarsa na da wani nauyi na musamman da ya rataya a wuyanta wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu. Ya ce tallafin da kasarsa ke baiwa Tel Aviv yana nan daram. Fira ministan na Burtaniya ya jaddada cewa kin amincewar da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi na samar da kasashe biyu kuskure ne kuma kuskure ne na dabi’a da dabaru. Ya jaddada cewa dole ne a bude mashigar kasa sannan kuma a bar manyan motocin...
Har ila yau, Ribadu ya ce yanzu mutane suna iya zuwa gonakinsu a wuraren da a baya ba a iya shiga saboda barazanar ‘yan bindiga. Sai dai duk da wannan ikirari, har yanzu wasu yankunan kamar Zamfara, Benuwe da Filato na fama da hare-haren ‘an bindiga da rikicin ƙabilanci. A ƙarshen makon da ya gabata, ‘yan bindiga sun kashe mutane a Kauran Namoda a Jihar Zamfara. Sannan ƙungiyar Boko Haram har yanzu na ci gaba da zama barazana a Arewa Maso Gabas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...

Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba, Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma. Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
2. Asibitin Turai Yar’Adua 3. Asibitin Amadi Rimi 4. Asibitin Jibia 5. Asibitin Funtua Zango, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wanda ke fama da cutar ya samu magani cikin sauƙi ba tare da biyan kuɗi ba. Zazzabin taifod yana yaɗuwa ne musamman a lokacin damina, kuma yana da nasaba da amfani da ruwa mai datti da rashin tsafta. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, ciwon kai, da gajiyar jiki. Gwamnati ta shawarci jama’a da su riƙa kula da tsafta da kuma hanzarta zuwa asibiti idan sun ga irin waɗannan alamomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa. Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba. Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe...
Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”. A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 ya zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa shirin da aka tsara, kana, bisa hasashen da aka yi. Sakamakon haka, jimillar haraji da kudaden da hukumomin buga haraji sun karba ta zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 155, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na yawan kudaden shiga na kasar Sin. Cikin adadin, kudin haraji zai kai sama...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.” Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare. Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin Taro a birnin New na kasar Amurka a dai-dai lokacinda ake gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Bin Farhan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, za’a gudanar da taron a ranar 28-29 ga watan Yulin da muke ciki , kuma akwai fatan kasashen duniya zasu tattaunawa wannan batun sosai don kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya bayan shekaru fiye da 70 ana gudanar da ita. Ministan ya kara da cewa a wannan taro...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu. Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman A taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna. Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda. Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici...
A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa. Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma. LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF A wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya,...
Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata. A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda su ka ci kwallaye 2-0, sai dai bayan komawa hutu, ‘yan wasan na Najeriya sun farke kwallon da aka zura musu, sannan kuma su ka kara da daya akai. Sai dai duk da cewa an sami galaba akan kungiyar kwallon kafar ta Moroko, magoya bayanta da suke bakin ciki, sun jinjinawa kungiyar tasu. Wasu sun bayyana cewa ba su tsammaci za a sami galaba akansu ba,, domin sun...
Daraktan Gidajen Rediyon Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Ndace, ya bayyana cewa an kammala shirin fara watsa shirye-shirye da harshen Mandarin, wanda shi ne harshe a hukumance na ƙasar China. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai tare da tawagar VON ga Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai. Ndace ya ce ƙara harshen Mandarin zai kawo yawan harsunan da VON ke amfani da su zuwa tara. A yanzu, hukumar na watsa shirye-shirye da Hausa, Igbo, Yarbanci, Fulfude, Turanci, Faransanci, Larabci da Swahili. Ya bayyana cewa dukkan kayan aiki da tsare-tsare sun kammala don fara aikin, da nufin tabbatar da ɗorewar wannan sabon shiri. China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta. Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta. Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN David Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”. Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro,...
Tsare-tsaren farko: Da yake su Turawan mulkin mallaka su riga sun kasance sun zauna daram a Arewacin Nijeriya, daganan sai suka aiwatar da tsare tsarensu wadanda sun bullo da su ne domin hana cinikin Bayi.Suka maida lamarin wanda a shekarun baya ba matsala bace,amma yanzu a shar’ance, an hana shi,sannan kuma naka samu damar ‘yantar da wadanda Iyayen su suka zama Bayi bayan wani lokaci. Yadda aka bullo ma lamarin: Yayin da ake ta kokarin hana cinikin Bayi, su Turawan mulkin mallaka sun,amince da yadda cinikin Bayi ya shafi lamarin zamantakewa da tattalin arziki a sashen na Arewacin Nijeriya. Don haka sai suka bi abin sannu- sannu, har dai suka samu damar kawo karshen lamarin, ta hanyar bada zabi...
Firai ministan kasar Burtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa ya fara tuntubar wasu kasashen turai kan nshirin jefawa Falasdinawa abinci daga sama tare da taimakon kasar Jordan. Shafin yanar gizo na Arab News ya nakalto Starmer yana fadar haka a yau Asanar ya kuma kara da cewa ya yi magana da kasashen Faransa da Jamus kan wannan shirin. Labarin ya kara da cewa banda jefa masu abinci kasashen zasu sauka su dauki marasa lafiya musamman yara kanana don jinyarsu.. Tun kimani watanni 4 da suka gabata ne gwamnatin HKI ta rufe kofofin shiga zirin gaza ta kuma hana shigowar abinci da magunguna, da nufin kashe dukkan falasdinawa kimani miliyon biyu a Gza, don ginawa yahudawa matsugunai a yankin. Tun fara...
Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu. Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar. Edword yace abu mafi...
Don haka nema tayi kira da jama’a kada suyi amfani da shi labarin daya zaman a kanzon kurege da ake ta yadawa,idan wani bayani suke bukata su tuntubi kafa da suka san ba zata yi zuki ta malle ba,ko kuma jami’an ma’aikatar ilimi ta kafar sadarwarsu ko kuma na, WAEC, da NECO. “An ja hankalin ma’aikatar ilimi ta tarayya akan wani labara ko rahoton da ya karade kafafen sadarwa na zamani,inda aka yi maganar cewar ban soke jarabawar WAEC ta shekarar 2025 da aka yi saboda an samu laifin aikata magudi lokacin da ake yin ta. “Ma’aikatar tace don haka tana sanar da jama’a cewa ta yi nesa da kanta,dangane da ita sanarwar ko labarin saboda kuwa ai na kanzon...
A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
Yau Juma’a, 25 ga Yulin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karbi takardun nadi daga sabbin jakadun kasashe 16 da suka hada da Angola, da Benin, da Sudan ta Kudu, da Amurka, da Iran, da Chile da sauransu a Babban Zauren taruwar Jama’a dake nan birnin Beijing. Shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin tana darajanta dangantakar abota da al’ummomin duniya, kuma tana fatan kara hadin gwiwa a mabambantan bangarori, da kowace kasa bisa mutunta juna, da daidaito da samun moriyar juna. Ya ce Sin za ta ci gaba da fadada budadden tsarin tattalin arzikinta mai zurfi, tare da ba da damar yin amfani da babbar kasuwarta, ta yadda sabon ci gaban kasar zai zama dama ga kasashen duniya, kuma...
A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu. A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya. Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin. Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa. Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya. Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a. Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis. NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana. Ya...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar. Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma...