Aminiya:
2025-07-03@11:22:54 GMT

An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima

Published: 3rd, July 2025 GMT

Tauraron Kannywood kuma mai sayar da maganin gargajiya, Abdullahi Alhikima ya magantu bayan da wasu ‘yan Kannywood suka caccake shi kan kalaman da ya yi a kansu.

Aminiya ta rawaito cewa hatsaniyar ta samo asali ne bayan fitattun ‘yan Kannywood da suka hada da Abdul M Sharif, Nura M Inuwa, Abubakar Bashir Maishadda, Sadik Sani Sadik, da sauransu suka kai wa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP Atiku Abubakar ziyarar goyon baya.

Ambaliya: Zulum ya bada umarnin tallafa wa mutanen Damboa da Askira-Uba Majalisar Dokokin Filato ta zaɓi sabon shugaba

Wannan ya tunzura Alhikma kasancewar wasu daga cikin wadanda suka je mubayi’ar ‘ya’yan kungiyar YBN ne a baya, da kuma 13/13 ta ubangidansa, mawaki Rarara.

A cikin wadanda Alhikima ya caccaka har da Shugaban Hukumar Fina-finai ta Ƙasa, Ali Nuhu.

Sai dai a kan hakan ne kuma wasu ke hasashen lallai ta tabbata alaƙa ta yi tsami tsakanin Alin da Rarara, wadanda a da suke abokai.

To sai dai Alhikman ya yi mi’ara koma baya, inda a ranar Laraba ya fito yana bayar da haƙuri, a cikin wani bidiyo da ya karade soshiyal midiya.

“Ina amfani da wannan dama domin janye kalamaina, na kuma bayar da hakuri ga ‘yan masana’antar Kannywood. Na yi wasu maganganu kuma zan janye bisa dalilai guda uku.

“Na farko maganar da na yi wasu na ganin ciyaman Alhaji Dauda Kahutu Rarara shi ne ya saka ni na yi wannan maganar. Ina ba da hakuri domin barranta shi da ita, domin ni na yi ta. Domin ya kira ni ya kuma nuna min kuskuren da ke cikin maganganuna. Kuma dama cikar dan adam shi ne idan shugabanka ya ce ka yi daidai ka karbi daidai ne. Idan shugabanka ya ce kayi kuskure ka karba.

“Haka kuma akwai abokiyar aikina Aishatul Humaira ta zaunar da ni ta gwada min kurakuran da ke cikin maganar da na yi, musamman a kan mai girma MD, Ali Nuhu. Wanda uba ne a wurinta a masana’antar. Hallau a cikin masana’antar tana da aminai maza da mata wanda suke da alaka ta mutunci da mutunta juna.”

Sai dai Alhikma ya yi togaciya a ban hakurin nasa, in da ya ce iya ‘yan Kannywood zai bai wa hakuri ban da wadanda ya kira da ‘yan shisshigi’.

Ita ma dai Aishatul Humairan ta bai wa ‘yan Kannywood din hakuri duk da ba da yawunta Alhikima ya tayar da hazon ba,  musamman Ali Nuhu, wanda ta ce uba ne a gare ta.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Aisha Humaira kannywood Rarara yan Kannywood

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata

Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza

Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka sami raunuka, wanda ake ganin yanki ne mai aminci ga iyalan da suka rasa matsugunansu. Duk da haka, an sha kai hare-haren bama-bamai kansa a cikin ‘yan makonnin nan.

Shaidun gani da ido sun kara da cewa; wasu Falasdinawa hudu ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da ‘yan mamaya suka kai wa wani gida na dangin Zeno da ke titin Jaffa a tsakiyar birnin Gaza.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 6, sun raunata wasu a Kwara
  • ’Yansanda Sun Ceto Ɗan Ghana, Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 3
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata
  • Magajin Garin Birnin Tehran Ya Karyata Da’awar ‘Yan Sahayoniyya
  • Kotu A Kasar Iraki Ta Yanke Hukuncin Kisa Kan Wadanda Suka Kashe Ayatullahi Baqir Sadr
  • Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
  • Sabani Tsakanin Bin Gafir, Smotresh Da Zamir Kan Makomar Fursinonin Yahudawa A Gaza
  • An Kashe ‘Yan Kungiyar Shabab 19  A Kasar Somaliya
  •   ‘Yan Guudun Hijirar Sudan Miliyan 4 Suna Fuskantar Yunwa A Kasashen Makwabta