Masanan sun kuma bayyana cewa, kashi 25 cikin 100 na manya a Nijeriya na dauke da kwayar cutar Sikila.

Ana bikin ranar Sikilar ne a kowace shekara, ranar 19 ga Yuni, domin wayar da kan jama’a game da cutar da kuma yadda ake sarrafa ta.

Wasu iyayen da suka bayyana irin abubuwa na renon yara masu fama da cutar, sun bayyana cewa; ba don an yaudare su da kuskuren sakamakon gwajin da aka yi musu kafin aure ba, da sun kaucewa matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu.

Wata uwa mai ‘ya’ya uku daga unguwar Dagbana da ke babban birnin tarayya Abuja, ta bayyana wa LEADERSHIP yadda aka ba ta takardar shaidar cewa; ita da maigidanta za su iya yin aure ba tare da fuskantar wata matsala ba, inda aka gano ainahin matsayinsu a lokacin da aka gano yaronsu na karshe na dauke da cutar.

Matar, wadda ta nemi a sakaye sunanta ta ce, “Mun yi gwajin jinsin da ake bukata a yi kafin aurenmu, kamar yadda Coci ta bukata. Kazalika, nawa sakamakon ya nuna cewa, ni AA ce; shi kuma mijina AS, saboda haka; mun yi tsammanin cewa, babu wata matsala; sai ga shi yaranmu na uku an gano yana dauke da cutar, bayan mun kai ziyara asibitoci da dama; aka ce mana yaron SS ne.

Har ila yau, ta bayyana yadda abin ya faru cikin ban tausayi, tana mai nuna cewa; ba don an samu matsala tun a farko wajen yin wannan gwaji ba, da yaron nata bai shiga wannan matsala da ya samu kansa a ciki ba.

“An yi kuskure wajen yi mana namu gwajin, yanzu kuma an bar mu cikin tsanani da wahalar rayuwa”, in ji ta.  

Madam Mary Ukaibe, wata mazauniyar Nyanya a babban birnin tarayya Abuja, ita ma ta bayyana yadda ta samu sakamakon bincikenta na karya. An fada mata cewa; AA ce ita, amma gwajin da aka yi mata kwanan nan ya nuna cewa AS ce.

“Allah ya taimake ni, mijina AA ne. Amma da a ce shi ma AS ne, dukkanin mu ba mu sani ba, da za mu buge ne da haihuwar ‘ya’ya masu dauke da wannan cuta ta Sikila mai ban tsoro”, in ji ta.

Ko shakka babu, wadannan ma’aurata na daya daga cikin da dama a Nijeriya da ke fuskanta wannan matsala sakamakon kuskure ko gwaji na karya da aka yi musu. 

Dakta Ifeanyi ya shaida wa LEADERSHIP cewa, tsarin yanayin dakunan gwaje-gwajen jini, ya yi matukar tara na bogi da ma’aikatan da ba su cancanta ba da kuma na’urori marasa inganci, wanda hakan ya haifar da karuwar sakamon jinsi na karya, musamman a tsakanin ma’auratan da ke neman gwajin kafin su yi aure.

“Matsalolin da ake samu daga masu yin gwajin na bogi daga cibiyoyi da dakunan gwaje-gwaje, na taimakawa wajen karuwar haihuwar Sikila a Nijeriya. Wannan matsala ta yadu a tsakanin manya da kuma matsakaita, wadanda kan yi gwajin jinsin halittar kafin su yi aure, amma daga karshe; sai su samu sakamakon bogi ko kuma wanda ke dauke da kuskure a ciki”, in ji shi.   

A cewar tasa, an yi kuskuren sanar da ma’aurata da yawa cewa; sun dace da jinsi, daga nan sai su kai ga yin aure, sai kuma daga bisani a gano cewa; ashe abin ba haka yake ba, watakila bayan sun fara haihuwar ‘ya’ya masu ciwon Sikilar.

Shugaban AMLSN ya ce, wannan ba wai ya takaita kadai ga dakunan gwaje-gwaje masu zaman kansu ba ne, har ma da kafatanin cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da masu zaman kansu, wadanda ba a tantance ba tare da na’urorin da su ma ba a tantance su ba da na jabu da kuma rashin sa ido yadda ya kamata. 

“Ni da kaina na shiga shagunan kwanan nan, don samo kayan aiki, kuma na gano cewa; yawancin samfuran da ke cikin kasuwa na bogi ne. Idan masanin harkar kamar ni, za a iya ba ni na bogi, idan ba na lura sosai ba, ina kuma ga wadanda ba su kware sun san harkar yadda ya kamata ba?”, in ji Dakta Ifeanyi.

Har ila yau, ya yi kira ga hukumomi, musamman kungiyar kimiyyar lafiya ta Nijeriya (MLSCN), da su dauki matakin gaggawa kan daidaita wadannan al’amura tare da tabbatar ganin cewa; ana aiwatar da bin ka’idoji da dukkanin tsare-tsaren da suka kamata.

A cewarsa, dole ne dukkan masana kimiyyar gwaje-gwajen lafiya a fadin tarayyar Nijeriya, su hada karfi da karfe wajen yaki da matsalar sayar da wadannan kayayyaki da suka shafi kiwon lafiya na bogi, wanda ya bayyana hakan a matsayin wata babbar barazana ga lafiyar al’umma baki-daya.

Lokacin da LEADERSHIP ta tuntubi cibiyar MLSCN, kan kokarin da take yi na dakile wannan al’amari yayin gwaje-gwaje, ta dage cewa; sai an gabatar da takarda a hukumance kafin ta yi magana kan al’amarin. 

Dakta Ifeanyi ya kuma bukaci kungiyoyi masu zaman kansu (CSOs) da cibiyoyin addini da sarakunan gargajiya, da su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma, kan illolin da ke tattare da auren da za a iya kamuwa da wannan cuta ta Sikila.

Yayin da yake amincewa da ci gaban da aka samu wajen tilasta yin gwaje-gwaje kafin a kai ga yin aure ya ce; ana ci gaba da samun raguwar yaduwar cutar a duk shekara.  

“Dole ne mu sake gina al’ummarmu, musamman ta hanyar wayar da kan jama’a game da kimiyya da fasaha da kuma ingantaccen tsarin gwaje-gwajen da ya kamata kowa ya yi”, in ji shi.

A nasa bangaren, mataimakin daraktan sashen kula da gwaje-gwaje a babban asibitin kasa na Abuja, Anthony Ilegogie ya gargadi ‘yan Nijeriya kan dogaro da dakunan da ba su da inganta ko na bogi, domin yin wannan gwaje-gwaje na kawayar halittar Dan’adam, yana mai jaddada cewa; yanayin halittar mutum ba ya canzawa, sannan kuma bai kamata bayan an yi gwaji na gaskiya a sake komawa ya ce za a sake yin wani ba.

A yayin da yake magana kan batun kura-kuren da ake samu dangane da sakamakon gwajin kwayar halittar, Ilegogie ya fayyace cewa; irin wannan matsala na faruwa ne sakamakon rashin horar da ma’aikata da rashin kayan aiki a dakunan gwaje-gwajen da ake da su.  

 “Mutane iri daban-daban, kan shiga wannan harka ko kasuwanci na harkar gwaje-gwajen jini, inda a karshe bayan mara lafiya ya fada hannunsu, sai su buge da ba shi sakamako na karya ko mara kyau”, kamar yadda Ilegogie ya yi gargadi.  

Sannan ya kuma kara da cewa, hanyoyin gwaji na zamani a halin yanzu, sun banbanta da wadanda ake amfani da su a da, domin kuwa yanzun an dogara ne da ingantattun na’urori na zamani da fasahohi, wadanda ke bayar da sakamakon da ake bukata daidai-wadaida. 

LEADERSHIP ta gano cewa, Nijeriya ce kasa mafi dauke da wannan cuta a duk fadin duniya, inda kashi 25 cikin 100 na manya ke dauke da kwayar cutar Sikila tare kuma da kamuwar jarirai kusan 150,000 a duk shekara, wanda hakan ke nuni da cewa; kusan kashi takwas cikin 100 na mace-macen jarirai a kasar na afkuwa.

A cewar mashawarciya ta musamman kan cutar Sikila ga ministan lafiya ta kasa, Farfesa Obiageli Nnodu, a halin yanzu kimanin ‘yan Nijeriya miliyan hudu ne ke dauke da wannan cuta ta Sikila.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yara dakunan gwaje gwaje da wannan cuta wannan matsala gwaje gwajen cutar Sikila

এছাড়াও পড়ুন:

Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya

Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan.

Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin.

Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna.

“A bangaren gyaran manufifin kudade kuwa, za a duba dokoki guda shida ciki har da dokar da za ta ba da iko ga hukumar rarraba haraji ta kasa don tilasta bin doka da rarraba kudaden haraji daga asusun gwamnatin tarayya da kuma inganta tsarin nazarin hanyar rarraba kudaden.

“A cikin wata sabuwar mataki tare da magance rashin daidaiton jinsi, kwamitin zai kuma yi nazarin wata doka da za ta samar da karin kujeru ga mata a cikin majalisun tarayya da majalisun jihohi.

“Don karfafa masarautun gargajiya, za a duba wani kudirin doka za sauya kundin tsarin mulki domin kafa majalisar masarautu gargajiya ta kasa da majalisar masarautun gargajiya ta jihohi da majalisar masarautun gargajiya ta kananan hukumomi.

“A kan gyaran tsarin zabe kuwa, za a tattauna wani shawarwari da ke neman gyara kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 don ba da damar tsayawa takara kai tsaye a kowane mataki na zabe, daga kananan hukumomi zuwa shugabancin kasa a taron sauraron jin ra’ayoyin.

“Jimlar wasu kudirorin doka fiye da 20 da ke neman gyara tsarin shari’a na kasar, ciki har da lokacin da ake zartar da hukunci da kuma fadada ikon kotunan zabe, suna daga cikin batutun da za a duba.

“Shawarwari guda talatin da daya kan kirkiro jihohi, suna cikin batutun da za a dubawa a taron sauraron jin ra’ayoyin.”

Kwamitin ya jaddada muhimmancin shigar jama’a wajen tsara kundin tsarin mulkin kasar, ya yi kira ga kowa da ya halarci taron sauraron jin ra’ayin jama’a na yankin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu
  • Gyaran Tsarin Mulki: Majalisa Ta Shirya Sauraron Jin Ra’ayoyin Jama’a A Wasu Sassan Nijeriya
  • Madarar Shanu Da Nijeriya Ke Samarwa Ta Karu Da Tan Miliyan 1.4 A Shekara Biyar
  • Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
  • Har yanzu mun gaza gano dalilin ɓullar COVID-19 — WHO
  • Yunwa ta kashe ƙananan yara 66 a Gaza
  • Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
  • Limamin Tehran:  Duniya Ce Ta Yi Yaki Da Iran
  • Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekara 101 a duniya