Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli
Published: 1st, July 2025 GMT
Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ranar Matasa: Ciyaman ya jinjina wa gwamnatin Gombe kan ɗaukar matasa aiki
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata.
Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai.
Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13Ya ƙara da cewa, yanzu wasu daga cikin matasan sun za su hidimata wa al’umma, saɓanin halin da suke ciki a baya.
Ya roƙi matasan su zama masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, inda ya bayyana cewa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma.
Ɗaya daga cikin matasan da aka ɗauka aikin, Musa Abdullahi, ya ce shirin GOSTEC, ya sauya rayuwarsa daga neman aiki zuwa taimakawa wajen bunkasa tattalin arziƙin jihar.
Ita ma, Fatima Mohammed, ta bayyana farin cikinta da samun aikin gwamnati bayan samun horo a fannin shafukan Intanet, tare da yaba wa gwamnati saboda ƙoƙarin inganta rayuwar matasa.
Bikin, ya samu halartar jami’an gwamnati, ƙungiyoyin matasa, inda aka tattauna kan makomar matasa, ilimi da ci gaban tattalin arziƙi a jihar.