Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027
Published: 29th, June 2025 GMT
Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya.
An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP.
Jigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar.
“Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun amince a shirya zaɓen shugabanni a duk lokacin aka ba da izini daga matakin ƙasa,” in ji shi.
Shugaban PDP a Jihar Kebbi, Usman Suru, ya nemi afuwar jama’a bisa halin matsin da suke ciki, ya kuma ce akwai fatan samun sauyi mai amfani a gaba.
Shi ma tsohon ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023, Janar Aminu Bande (mai ritaya), ya soki matsin tattalin arziƙi da halin da jihar ke ciki, inda ya zargi gwamnatin APC da tsare ‘yan adawa ba bisa ƙa’ida ba.
“Zan mara wa PDP baya a duk wani yunƙurin da za ta yi domin a kawo gwamnati mai adalci a Kebbi da Najeriya gaba ɗaya,” in ji shi.
Jam’iyyar PDP ta ce tana da yaƙinin cewa da haɗin kai da gyaran cikin gida, za ta iya samun nasara a 2027.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.
Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.
Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.
Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.
Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.
DAGA SULEIMAN KAURA