Limamin Tehran: Duniya Ce Ta Yi Yaki Da Iran
Published: 28th, June 2025 GMT
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran ya bayyana cewa; A cikin kwanaki 12 da su ka gabata duniya ce ta yi yaki da Iran.
Hujjatul Islam Wal Muslimin Abu Turabi Fard, ya fara hudubarsa da mika sakon ta’aziyyar shigowar ranakun Ashura, haka nan kuma jinjina ga shahidan jamhuriyar musulunci masu daraja da HKI ta yi wa kisan ta’addanci a tsawon kwanaki12 na yaki.
Limamin na Tehran ya kuma ce; Abubuwan da su ka faru a cikin kwanaki 12 na yaki sun bude wani sabon shafi na siyasa a cikin wannan yankin da kuma a fagen siyasar kasa da kasa.
Hari la yau limamin na Tehran ya jinjinawa jagoran juyin musulunci na Iran saboda yadda Iran a karkashin jagorancinsa ta zama cibiyar gwgawarmayar musulunci a cikin wannan yankin.
Limamin juma’ar na Tehran ya kuma kara da cewa; HKI ta kawo wa Iran hari ne a jajiberin ranar Idan Gadir bisa cikakken taimakon bayanai na asiri daga Amurka.”
Limamin ya kuma kara da cewa; Masu bin diddigin abubuwan da suke faruwa suna bayyana cewa; Makiya, sun dauki shekaru kusan 20 suna shirya wannan yakin. Shi kanshi fira ministan HKI ya yi furuci da hakan.
Hujjatul Islami Wal Muslimin Abu Turabi Fard ya kuma ce; HKI ta kawo wannan harin ne adaidai lokacin da ake tattaunawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a Tehran ya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kwara Ta Yi Gargadi Ga Manoman Ruwan Malka Na Wata Agusta
Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana.
A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci.
Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma, amfanin gona, da kuma dabbobi.
Sanarwar ta yi gargadin cewa ambaliya na da matukar hadari ga noma da samar da abinci a fadin jihar.
Yana ba manoma shawara da su girbe amfanin gona da aka shirya cikin gaggawa, su mayar da dabbobi, injunan gona, da kayan aiki zuwa wuri mafi aminci, wurare masu tsauni, da tabbatar da kula da magudanan ruwa a gonakinsu don ba da damar kwararar ruwa.
Ta bukaci jami’an aikin gona da su kasance a shirye don tallafa wa manoma da kare kadarorin noma da rayuwa a tsawon wannan lokaci.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU