Indomie Ta Kaddamar Da Shirin Gangamin Abinci Mai Gina Jiki Na ‘Ingantaccen Abinci Domin Nasara’
Published: 28th, June 2025 GMT
Tallan na talabijin ya bayar da labarin rayuwar Binta, ya kuma mayar da hankali akan irin tasirin da abinci mai kyau ya ke da shi wajen tallafawa iyali. Da labarin ya yi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da goyon bayan iyali ya ke taka muhimmiyar rawa wajen cin nasara a rayuwa.
Indomie tun da daɗewa tana da yaƙini kan cewa ciyarwa bai tsaya kawai ga jiki ba ne. Har da taimakawa wajen cikar buri da samar da makomar kowanne yaro zuwa mataki na gaba. Shi ya sa muka ƙirƙiri shirin ‘Indomie AI
Career Generator,’ wata Manhaja ce ta musamman da ke taimaka wa yara su hango manyan burikansu ta hanyar hotuna masu kayatarwa da ƙarfafa guiwa.
Ta hanyar ziyartar shafin https://nasarada.indomie.ng kawai, iyaye za su bi wasu matakai masu sauƙi domin su samar da hotunan yaransu a matsayin likitoci da lauyoyi da injiniyoyi da dai sauransu. Wannan wata hanya ce daga gare mu domin kusanta su da mafarkinsu da kuma nuna wa kowane yaro cewa makomarsu tana da amfani, ana iya hangenta, kuma ta na dab da su.
Indomie Na Ɗauke Da Muhimman Sinadaran Gina Jiki
Taliyar Indomie na dauke sinadarai masu matuƙar amfani ga jiki, kamar su: calcium da iron da protein da Vitamin B da kuma Vitamin A. Duka suna taimakawa wajen girma da bunƙasa kwakwalwa da kuma lafiya mai ɗorewa. Wannan ya sanya Indomie ta zama abinci inganci da sauƙin sarrafawa da samar da ingantatun sinadaraida ake buƙata daga kowane kalar abinci.
“Muna alfahari da ƙaddamar da gangamin ‘Nasara da Indomie’ wanda ke taka rawa wajen wayar da kai kan amfanin samar da abinci mai gina jiki wajen samar da kyakkyawar rayuwa anan gaba,” cewar Jamiu Abdulrasheed, jami’in tallace-tallace a Manhajar zamani ta Indomie “Wannan girmamawa ce da sadaukarwar da iyaye mata ke yi wajen ciyar da iyalansu da abinci mai amfani, da kuma nuna yadda Indomie ke bayar da daɗin ɗanɗano da gina jiki domin tallafawa zuwa kai wa ga matakin nasara.”
Ana shawartar masu kallo da su kalli wannan labari mai zaburarwa da saka ƙaimi wajen samar da Ingantaccen abinci domin samun nasara a shafukan sada zumunta na: @IndomieArewa a Manhajar Facebook da
@indomie_arewa a Manhajar Instagram.
Indomie Nigeria za ta cigaba da jajircewa wajen samar da hanyoyin abinci masu gina jiki ga iyalai da kuma tallafawa hanyarsu ga cinma nasara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abinci Domin Nasara Taliya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kammala shirye-shiryen yi wa yara sama da miliyan daya da rabi ‘yan ƙasa da shekaru biyar allurar rigakafin shan inna zuwa karshen watan Nuwamba a jihar.
Shugaban Hukumar Kula Lafiya a Matakin Farko ta Jihar (JSPHCDA), Dakta Shehu Sambo, ya bayyana haka a taron tattaunawa da manema labarai na yini guda da aka shirya, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, a Dutse, babban birnin jihar.
Dakta Sambo, wanda Mataimakin Mai wayar da kan jama’a na hukumar, Malam Nura Ado ya wakilta, ya ce ana sa ran adadin yara 1,516,244 ne za a yi wa rigakafin a wannan watan.
Ya ƙara da cewa rigakafin watan Nuwamba za a gudanar da shi ne tare da Makon Lafiyar Uwa, Jariri da Yara (MNCH), inda ake ba mata masu juna biyu kulawar lafiya.
Dakta Sambo ya roƙi goyon bayan kafafen yada labarai domin isar da sako da kuma wayar da jama’a.
A nasa jawabin, Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Mohammed Rahama Farah, ya yaba wa jihar Jigawa bisa rage yawaitar cutar ta shan inna da kashi 58 bisa dari a shekarar 2024.
Sai dai ya yi gargadin ccewahar yanzu cutar na barazana a Najeriya , domin an samu lamura 72 a jihohi 14 a shekarar 2025, don haka akwai buƙatar ƙara faɗaɗa rigakafi.
Rahama Farah ya yi kira shugabannin kananan hukumomi da su sa ido sosai kan yadda ake gudanar da aikin domin tabbatar da nasara, tare da bukar kafofin watsa labarai su ƙara wayar da kai ga iyaye.
Ya kuma yi kira da a ɗauki aikin a matsayin na kowa da kowa domin kawo ƙarshen yaduwar cutar shan inna a Jigawa da sauran jihohin ƙasar nan.
Ita ma da yake jawabi a madadin Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Ƙasa (NPHCDA), Hajiya Firdaus Aminu ta yaba wa jihar bisa kyawawan shirye-shirye game da shirin yaki da cutar.
Za a gudanar da rigakafin shan innan na watan Nuwamba daga 27 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba, 2025.
Aikin, tare da makon MNCH, za su gudana ne ta hanyar ƙungiyoyi 2,015 na ma’aikatan wucin-gadi a fadin kananan hukumomi 27 na jihar.