2025-09-24@12:47:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 13
«kafafen yaɗa labarai»:

Ƙungiyar masu kafafen yada labarai na Arewa za ta daukaka kara kan hukuncin kotu a kan tashar Arewa24
Ƙungiyar masu kafafen yaɗa labarai ta Arewacin Najeriya (NBMOA) ta yi watsi da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na yin watsi da ƙarar da ta shigar a kan tashar Arewa24, inda ta ce za ta ɗaukaka ƙara. Idan za a iya tunawa, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a watan Agusta, ta yi watsi da karar da kungiyar NBMOA ta shigar a kan Arewa24, saboda “rashin hukunci da rashin cancanta”, kamar yadda aka gani a cikin kwafin takardar hukuncin kotun (CTC). Kotun, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da cewa AREWA24 tana gudanar da harkokinta ne bisa ƙa’ida, kuma ba ta da hurumin samun ƙarin lasisin gudanar da ayyukanta, ba tare da karya wata doka...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Ya ƙara da cewa, Tinubu na mutunta dimokuraɗiyya da doka. Haka kuma, gwamnati ta san cewa ba za ta iya aiki yadda ya kamata ba tare da kafafen yaɗa labarai ba. Idris ya ce a baya, wasu jami’an gwamnati suna sukar gwamnati, amma shi kullum yana tattaunawa da ƙungiyar ’yan jarida da masu wallafa jaridu domin warware matsaloli cikin lumana. “Idan muna yin daidai, ku yabe mu,” in ji shi. “Idan kuma muna kuskure, ku faɗa mana cikin lumana domin mu inganta ayyukanmu.” Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana da kyakkyawar mu’amala da kafafen labarai kuma hakan zai ci gaba. Ya roƙi ’yan jarida ka da su ɗauki wasu ƙananan matsaloli su yi wa gwamnati hukunci a kai gaba ɗaya....
Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
Jimillar fursunoni: 80,879 Adadin cibiyoyin gyaran hali: 256 Kashi na rijista da aka kammala: 74% Umar ya jaddada cewa sauran fursunonin da ba a yi wa rijistar ba za a cigaba da yi musu, kuma an kafa duk wasu hanyoyi da za su tabbatar da nasarar kammala aikin cikin sauki. Hukumar ta bayyana wannan aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin dijital, da sake gyaran rayuwa, da shigar da fursunoni cikin tsarin ƙasa. Ya kuma buƙaci kafafen yaɗa labarai da su tabbatar da sahihancin bayanansu daga hukumomin da suka dace kafin wallafawa domin kaucewa yaɗa bayanan da za su iya dagula fahimtar jama’a ko rage ƙwarin gwuiwar al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista. “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya. “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba. “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...

Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin ZamfaraBabu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista – Gwamnatin Zamfara
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Zamfara kan munanan labaran ƙarya da ke yawo a kan wata mata mai suna Zainab Muhamadu ‘yar shekara 22, wacce ke fuskantar hukuncin kisa saboda ta shiga addinin Kirista. “Muna so mu bayyana cewa aikin maƙiya zaman lafiya ne, waɗanda suke neman hanyar haifar da tashin hankali a inda ake zaman lafiya. “Labarin ƙaryar, wanda wani dandali na yanar gizo da ya yi ƙaurin suna wajen yaɗa labaran bogi ya yaɗa, ba wani abu ba ne illa yunƙurin dagula zaman lafiya da ba za a yi nasara ba. “Gwamnatin jihar Zamfara ta yi gaggawar ɗaukar matakin gayyato dukkan hukumomin da abin ya shafa da jami’an tsaro domin tabbatar da sahihancin labarin, wanda...

Gwamnatin Tarayya Da Majalisar Dokoki Za Su Haɗa Gwiwa Kan Sake Duba Dokar Laifukan Intanet — Minista
Idris ya jaddada cewa Gwamnatin Tinubu tana da ƙudirin kare ’yancin faɗin albarkacin baki da ’yancin kafafen yaɗa labarai, waɗanda ya ce su ne ginshiƙan dimokiraɗiyya a ƙasar nan. Ya ce: “Na bayyana ra’ayi na ga Jakaden, kuma na kuma jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da kare ’yancin faɗin albarkacin baki da kuma rashin takura wa ‘yan jarida wajen gudanar da aikin su. Za mu ci gaba da kare wannan. “Muna ganin aikin jarida da kafafen yaɗa labarai wani muhimmin ɓangare ne na dimokiraɗiyya. “Babu wata dimokiraɗiyya da za ta yi nasara ba tare da kafafen yaɗa labarai ba.” Sai dai kuma ministan ya buƙaci ‘yan jarida da su riƙa amfani da ‘yancin da suka...
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai. Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji. Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.” Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu. Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa. Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu. ’Yan sanda ku yi amfani da iko cikin adalci — CP Wakili An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...
Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...