Yadda Yaƙin Iran Da Isra’ila Zai Iya Shafar Zamantakewa Da Tattalin Arziƙin Nijeriya
Published: 29th, June 2025 GMT
Tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya ci-gaban mai hakar rijiya ne ga Nijeriya wadda ke kan gaba wajen fitar da mai ta yadda za ta samu makuddan kudin shiga sai dai gagarumar matsala ce ga ‘yan kasa wadanda za su fuskanci karin mai a cikin gida wanda zai zama silar karin kunci a dalilin farashin abubuwa da dama da zai hau sama.
A cewar masana, Gabas ta Tsakiya da ke samar da akalla kashi 34 na mai a duniya da kashi 18 na gas, gumurzun kasashen biyu ya haddasa farashin danyen mai tashi da kashi 10, yayin da gas ya kara da kashi 7. Haka ma akwai fargabar Isra’ila na iya illata harkokin mai da jigilarsa a mashigar Hormuz da ke karkashin ikon Iran.
Baya ga wannan farashin rarraba kaya da fitar da kaya ta jiragen ruwa ya karu a bisa ga tashin kudin inshoran jiragen ruwa a Gabas ta Tsakiya wanda ya kawo tsaikon kasuwanci a duniya.
A yanzu haka dai a wannan makon kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya fitar da sanarwar karin kudin mai a gidajen man sa a fadin kasar bakidaya.
Tun a kwanan baya masana suka bayyana cewar farashin man fetur zai tashi a kasuwannin duniya a dalilin fafatawar yakin Iran da Isra’ila.
Kamfanin ya bayyana karin kudin mai zuwa naira 945 wanda karin ya biyo bayan karin kudin mai da matatar mai ta Dangote mai zaman kan ta ta yi zuwa naira 880.
A bayyana yake cewar Iran babbar kasa ce daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin arzikin man fetur da ke fitar da shi a kasashen duniya don haka wajibi ne yaki da kasar ya shafi tattalin arzikin kasashe da dama.
Duk da matatar mai ta Dangote ta na aiki amma har zuwa yanzu shigo da man fetur ake yi a Nijeriya don haka tashin farashin a kasuwannin duniya na nufin tashin farashinsa a Nijeriya kamar yadda masana suka bayyana.
Da yake bayani kan illar yakin ga Nijeriya, masani kan tattalin arziki da huldar diflomasiyya kuma Shehin Malami a jami’ar Ibadan, Farfesa Tayo Bello ya yi gargadin yakin zai shafi Nijeriya da babban kalubale sosai.
Ya ce Nijeriya wadda ita ce babbar kasar Afurka mafi albarkatun mai za ta ci-gaba da amfana da karin kudin mai a gajeren lokaci, amma hakan zai haifar da gagarumar illa ga ‘yan Nijeriya a gida.
“Yakin tamkar takobi biyu ne mai kaifi ga Nijeriya, a daya hannu a na tsammanin farashin mai a kasuwar duniya zai tashi sosai. Hakan na nufin Nijeriya za ta ci-gaba da samun karin haraji sosai musamman idan farashin ya tashi daga dala 75 a ganga daya zuwa dala 90 ko sama da haka.”
“Karin kudin mai a duniya na nufin karin kudin mai a Nijeriya. Man dizel, fetur da sauran abubuwa za su yi tsada sosai wanda hakan na nufin hauhawar farashi sosai.”
Injiniya Yabagi Sani fitaccen mai sharhi kan al’ummarran man fetur a Nijeriya ya bayyanawa BBC Hausa cewar illar da yakin ya yi wa sauran kasashen duniya shine ya shafi Nijeriya.
Ya ce a bayyane yake kusan kashi 20 zuwa 30 na mai da ake hada- hadarsa a kasuwannin duniya a na yin sa ne ta mashigar Hormuz da ke karkashin kasar Iran don haka su ke da ikon shiga da ficen mai.
Masanin ya bayyana cewar a sakamakon wannan yakin Iran ta yi barazanar rufe mashigar wanda sakamakon fargabar matsalar da za ta iya biyowa baya, jiragen dakon man fetur suka fara kauracewa mashigar wanda a cewarsa wannan ne ya haifar da karancin mai a kasuwandnin duniya bakidaya.”
Shi kuwa tsohon jakadan Nijeriya a kasar Ethiopia, Bulus Lolo na ganin ko kadan ba alheri ba ne ga kowa ciki har da Nijeriya kan ci-gaba da nunawa juna yatsa da kasashen biyu ke yi.
Ya ce a wasu lokutan fada irin wannan yana da amfani, a wasu lokutan kuma ba ya da amfani. Nijeriya ba ta fuskantar farmaki kai tsaye, amma ta na amayar da muryar ta kan kasashen biyu da su tsagaita wuta su daina kaiwa juna hari, a zauna a teburin sulhu.*
Ya ce kasuwar mai a duniya za ta shaidi artabun da ke faruwa a ma’ajiyar man Iran, amma ba su fatar kazantar lamariin a kasuwar duniya, a cewarsa suna fatar abubuwa za su daidaita domin hasashen su ya tafi daidai.
“Akwai yiyuwar karin kudi ta yadda farashi zai hau sama sosai amma har zuwa yaushe? Sabani ne wanda ba mu san yadda karshensa zai kasance ba.” In ji Lolo.
Masana da jama’a na ganin mafitar kawar da radadin farashin mai a Nijeriya shine gwamnafi ta inganta matatun mai, ta yadda za su rika aiki yadda ya kamata domin samar da wadataccen mai ga ‘yan kasa.
Haka ma gwamnati za ta iya saukakawa jama’a ta hanyar rage farashin mai wanda hakan zai magance hauhawar farashin kaya da al’umma ke fargaba a halin yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Iran Isra ila War Yaki a kasuwannin duniya karin kudin mai a
এছাড়াও পড়ুন:
Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza
A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
A wata sanarwa da ya fitar ta hanyar gidan radiyo Sputnik ta kasar Rasha, Hazam al-Assad ya tabbatar da cewa: Yemen za ta dakatar da kai hare-hare kan gwamnatin mamayar Isra’ila, idan har ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza.
Tun da farko dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da kungiyar Hamas sun rattaba hannu kan matakin farko na shirinsa na zaman lafiya.
A nata bangaren, Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, wadda ta hada da shigar da kayan agaji da musayar fursunoni. Ta yi kira ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da kasashen da suka amince da yarjejeniyar, da kuma kasashen Larabawa, da na Musulunci, da na kasa da kasa, da su tilastawa haramtacciyar kasar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar gaba daya.
A yau litinin ne za a gudanar da shawarwarin a Sharm el-Sheikh a birnin Alkahira, tare da halartar shugaban Amurka Donald Trump da kasashe masu shiga tsakani, domin kafa dukkanin sharuddan da suka dace domin samun nasara da kuma ci gaba da aiwatar da shirin, wanda bangarorin Falasdinu da gwamnatin mamayar Isra’ila suka amince da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci