Atiku, Obi, El-Rufai, Amaechi Da Wasu Sun Halarci Taron ADC Na jam’iyyar Haɗaka
Published: 2nd, July 2025 GMT
Wasu manyan ƴan siyasa daga jam’iyyun adawa sun hallara a Cibiyar Yar’Adua da ke Abuja a yau Laraba da rana don taron ƙaddamar da sabbin shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), a wani mataki na shiryawa zaɓen shekarar 2027. Taron ya samu halartar manyan fitattun ’yan takara da tsofaffin gwamnoni daga sassa daban-daban na ƙasa.
Cikin waɗanda suka halarta akwai Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP; Peter Obi na LP; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; da tsohon Ministan Sufuri kuma gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi. Haka kuma, Solomon Dalung, Dino Melaye, Dele Momodu, Sanata Gabriel Suswam, da Sanata Ireti Kingibe sun samu halarta. Emeka Ihedioha da Air Marshal Sadique Abubakar (rtd.) suma sun bayyana.
David Mark Da Aregbesola Sun Zama Shugaba Da Sakataren Jam’iyyar ADC Ana Sa Ran Samun Bunkasuwar Dangantakar Sin Da Kungiyar SADCA yayin taron, an sanar da cewa haɗakar jam’iyyun adawa ta ɗauki jam’iyyar ADC a hukumance a matsayin dandalin siyasa da za ta yi amfani da shi don ƙalubalantar jam’iyyar APC a 2027. An bayyana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, a matsayin shugaban riko na ƙasa. Ya fice daga jam’iyyar PDP domin jagorantar sabon tsarin siyasar.
An kuma nada tsohon gwamnan Osun kuma jigon APC, Rauf Aregbesola, a matsayin sakataren riko na ƙasa, alamar yiwuwar sauyin tunani da haɗewar ƙarfi daga jam’iyyu daban-daban. Ana sa ran David Mark da sauran shugabanni za su fara ƙaddamar da sabuwar tafiyar siyasar, yayin da taron ke ci gaba a lokacin haɗa wannan rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
APC ta nemi INEC ta soke zaɓen cike gurbin Kano
Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano.
Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana.
An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan daba 100 a Bagwai — INECA cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Felix Morka ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta ce ta samu rahotannin da suka tabbatar an samu rikici a Shanono, Bagwai da Ghari.
Ta ƙara da cewa masu kaɗa ƙuri’a sun tsere daga rumfunan zaɓe sakamakon tashin hankali, yayin da jami’an tsaro suka kasa shawo kan lamarin.
“APC na kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gaggauta soke zaɓukan cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma zaɓen mazaɓar Ghari a Jihar Kano saboda tashin hankali da kuma tada hargitsin ’yan daba da aka samu.
“’Yan daba ɗauke da makamai sun tarwatsa rumfunan zaɓe da dama,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa barin zaɓukan su ci gaba da gudana ya saɓa wa tsarin gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, kuma hakan zai iya zama barazana ga zaɓuka a gaba.