An Fara Gudanar Da Jana’izar Shahidan Yakin Kwanaki 12 A nan Tehran
Published: 28th, June 2025 GMT
A safiyar yau ne aka gudanar da tattakin jana’izar shahidai kimani 60 a nan Tehran, wadanda suka hada da kwamandojin sojojin kasar da da masana fasahar Nukliya da sauran mutane maza da mata.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto cewa, an fara tattakin Jana’izar ne daga danganlin inkilabi ko juyin juya hali har zuwa dandalin yenci dake tsakiyar birnin na Tehran .
Daga cikin manya-manyan bakin da suka halarci tattakin har da shugaban kasa Dr Masoud Pezeshkiyan da kuma wasu ministocinsa . A ranar 13 ga watan Yuni ne HKI ta fara kaiwa kasar Iran yaki inda ta kashe mutane da dama daga daga ciki har da manya-manyan kwamandojojin sojojin kasar da masana fasahar Nukliya da kuma sauran mutanen gari maza da mata da yara. Muta ne kimani 600 ne suka yi shahadi a cikin yakin kwanaki 12 da HKI ta kai hare-haren.
Bayan yan sa’o’I ne sojojin kasar ta Iran suka fara maida martani da dandazon makamai masu linzami. Wadanda suka lalata biranen HKI, har sai da suka nemi tsagaita wuta. Kafin karshen yakin dai sojojin Iran sun kai dandazon makamai har sau 22. An tsagaita wuta ne a ranar 24 ga watan Yuni.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12
Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya.
Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri kan kasarta a fagen diplomasiyya zuwa wani lamari da duniya ta amince da shi.”
Har ila yau Baqeri Kani ya yi ishara da hadin kan kasa a matsayin mafi girman bayyanar da Iran ta taka rawa a wannan yaki yana mai cewa: Wannan hadin kai yana nuna irin gagarumin goyon bayan da jami’an diflomasiyyar Iran suka nuna.
Ya kara da cewa: Goyon bayan jama’a ga manufofi da matakan gwamnatin na iya taimakawa wajen cimma manufofin diflomasiyya. Har ila yau ya bayyana cewa: A halin da ake ciki yanzu, kasashen yammacin duniya, baya ga Amurka, sun taka rawa wajen tallafawa hare-haren da aka kai wa Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza August 10, 2025 Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba August 10, 2025 Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci