Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji
Published: 29th, June 2025 GMT
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato, sun roƙi gwamnatin jihar da ta Tarayya da jami’an tsaro da su kai musu ɗauki kan barazanar da ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ke musu.
A farkon makon nan ne aka samu labarin cewa Bello Turji ya bai wa mazauna wasu yankuna a Isa wa’adin gina masa ƙaramin dam ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
Har ila yau, ya umarce su da su bar garuruwansu, domin ba ya buƙatar ganinsu a wajen.
Wani mazaunin yankin, Wanzami Abubakar Isa, ya bayyana damuwarsa cewa suna zaune garuruwansu kamar baƙi.
“Abin takaici ne yadda ’yan bindiga ke ba mu umarni a garinmu na haihuwa. Muna roƙon gwamnati ta taimake mu.“
Shi ma Alhaji Abdullahi Isa ya ce, “Rayuwarmu ta shiga mawuyacin hali. Ba za mu iya ci gaba da rayuwa a haka ba.
“Ta yaya za mu bar gidajenmu saboda barazanar ɗan bindiga? Gwamnati ta yi wani abu cikin gaggawa.”
Wani mazaunin yankin, Bashar Ahmad, ya ce ba daidai ba ne a bar Turji yake cin karensa babu babbaka.
“Gwamnati ta kare mu, mu ma ’yan ƙasa ne kuma muna da ’yancin zama lafiya.”
Sai dai duk ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Isa, Alhaji Sharifu Kamarawa, da mai bai wa gwamna shawara kan harkar tsaro, Ahmad Usman, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira ko saƙon da aka aike musu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
Yanzu haka, ko da yake Turji bai bayyana ranar da zai kai hari ba, akwai fargaba sosai a yankin.
Jama’a na ganin ya kamata gwamnati ta ɗauki mataki mai tsauri, maimakon ci gaba da yin sulhu da ’yan bindigar da ke addabar yankin gabashin Sakkwato.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗauki gwamnati hari Sakkwato
এছাড়াও পড়ুন:
Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027
Jam’iyyar PDP a Jihar Kebbi, ta bayyana shirinta na haɗa kai da sauran jam’iyyu da ƙungiyoyi domin karɓe mulki daga hannun APC a zaɓen 2027, a matakin jiha da kuma tarayya.
An bayyana wannan matsaya ne a garin Birnin Kebbi ranar Asabar, yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda aka jaddada buƙatar yin sulhu da warware rikicin cikin gida da ke damun PDP.
Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a MadinaJigo a jam’iyyar, Ibrahim Mera, ya ce sun amince su haɗa kai da kowa domin a samu nasarar kawar da APC a jihar.
“Za mu yi aiki tuƙuru don ganin haɗakar ta yi tasiri. Mun amince a shirya zaɓen shugabanni a duk lokacin aka ba da izini daga matakin ƙasa,” in ji shi.
Shugaban PDP a Jihar Kebbi, Usman Suru, ya nemi afuwar jama’a bisa halin matsin da suke ciki, ya kuma ce akwai fatan samun sauyi mai amfani a gaba.
Shi ma tsohon ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen 2023, Janar Aminu Bande (mai ritaya), ya soki matsin tattalin arziƙi da halin da jihar ke ciki, inda ya zargi gwamnatin APC da tsare ‘yan adawa ba bisa ƙa’ida ba.
“Zan mara wa PDP baya a duk wani yunƙurin da za ta yi domin a kawo gwamnati mai adalci a Kebbi da Najeriya gaba ɗaya,” in ji shi.
Jam’iyyar PDP ta ce tana da yaƙinin cewa da haɗin kai da gyaran cikin gida, za ta iya samun nasara a 2027.