Sarayal Kuds Ta Kai Wa Matsugunin ‘Yan Mamaya Na Sydriot Hari Da Makamai Masu Linzami
Published: 3rd, July 2025 GMT
Rundunar Sarayar Kudus dake karkashin kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da kai wa matsugunin ‘yan share wuri zauna na Sydriot hari da makamai masu linzami da su ka yi sanadiyyar kashe da jikkata sojojin mamaya.
Su kuwa kafafen watsa labarun HKI sun samar da cewa, an tsinkayo harba makamai masu linzami guda 3 daga Gaza zuwa Sydriot.
A gefe daya dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da cewa sun kai wasu hare-haren da makamai masu linzami zuwa yankin Q20 a sansanin ‘yan share wuri zauna na ” Nir-Ishaq” da “Miftahim.
Bugu da kari dakarun na “Sarayal-Kuds’ sun sanar da kai wa tankar yaki samfurin Mirkava hari ta hanyar wata nakiya mai karfi akan hanyar Zannah,dake gabashin unguwar Shuja’iyyah a birnin Gaza.
Abinda ya biyo baya shi ne kai wani harin da “Sarayal-Kuds’ ta yi akan sojojin mamaya da suke cikin wani gida, ta hanyar amfani da makamin TBG. Da dama daga cikin sojojin mamayar sun halaka da kuma jikkata.
A ranar Talatar da ta gabata ma dai dakarun “Sarayal-Kuds” sun kai wasu hare-haren na hadin gwiwa da ‘ Kassam’ akan cincirindon sojojin mamaya a arewacin Khan-Yunus.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Sarayal Kuds
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati Za Ta Biya Wasu Kudaden Ariyas Ga Masu Fensho Wannan Wata
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari.
Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja.
Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden.
Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin bata martaban kasan nan.
Hakan kuma masu karban fensho a Radion Tarayya na kasa FRCN da Gidan talabijin na kasa NTA dake Kaduna sun nuna damuwarsu game da zargin da ake yi cewa ana kokarin wulakanta shugabannin kungiyar ma’aikatan da suka yi ritaya karkashin jagorancin kwamaret Munkaila Ogunbote.
DAGA SULEIMAN KAURA