Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Jaddada Cewa: Iran Tana Da Hakkin Tace Sinadarin Uranium A Kasarta
Published: 28th, June 2025 GMT
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa: Iran za ta ci gaba da tace sinadarin Uranium a cikin kasarta
Jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani ya bayyana cewa: Iran tana jaddada matsayinta na cewa dole ne ta gudanar da ayyukan tace sinadarin Uranium a cikin kasarta, yana mai cewa: “Kungiyar masu sa-ido zata iya kasance a Iran, amma ba za ta maye gurbin Shirin Iran na cikin gida ba.
Jakadan Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Irawani a wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al-Monitor, ya kara da cewa: “Iran ta kasance tana neman mafita ta hanyar lumana don tunkarar matsalolin da ake iya fuskanta game da shirinta na makamashin nukiliya.
Irawani ya jaddada cewa: “Mahimmin batu shi ne amincewa da ‘yancin Iran a matsayin memba na yarjejeniyar NPT.” Kuma ba ta son fiye da hakan ko kuma daukarta kasa da ke da hakkoki kamar sauran membobi a karkashin yarjejeniyar NPT, domin kowace kasa memba na da ‘yancin gudanar da bincike, samar da ci gaban kasarta ta hanyar amfani da makamashin nukiliya don zaman lafiya. Iran tana da niyyar yin amfani da dukkanin bangarori uku na wannan hakki, musamman ‘yancin gudanar da ayyukan makamashin nukiliya a cikin kasarta.”
Jakadan na Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba kimiyya a cikin kasarta kuma karkashin ikonta. Wannan ba yana nufin bata son yin aiki tare da wasu ƙasashe ba ne.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran a Majalisar Dinkin Duniya a cikin kasarta ya jaddada cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19
Gwamna Oyebanji ya godewa ‘yan majalisar zartarwar jihar da abin ya shafa tare da yi musu fatan samun nasara a ayyukansu na gaba.
Sai dai, umarnin bai shafi babban Lauyan jihar da kwamishinan shari’a ba.
Har ila yau, daga cikin wadanda sallamar ba ta shafa ba, akwai Kwamishinonin Lafiya da Ayyukan Jama’a, Noma da Tattalin Abinci da Ayyuka.
Bugu da kari, kwamishinan ciniki, saka hannun jari, masana’antu da kungiyoyin hadin gwiwa; Mai ba da shawara na musamman kan Ilimin masu bukata ta Musamman; da mai ba da shawara na musamman kan tsare-tsaren kasa, duk suna nan kan mukamansu.
Haka kuma, duk Daraktocin da ke cikin majalisar zartarwa ta Jihar, za su ci gaba da rike mukamansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp