Iran ta Ki Amincewa Da Ziyarar Shugaban Hukumar IAEA Zuwa Kasar
Published: 28th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, yana daukar shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya IAEA Rafael Grosi a matsayin wanda ya ingiza HKI kaiwa kasar Iran hare-hare a ranar 13 ga watan Yuni. Ya kuma kara da cewa, Grossi a halin yanzu ya matsa yana son zuwa kasar Iran don ya dubi irin barnan da Amurka ta yiwa cibiyoyin nukliyar kasar Amma Iran ta ce ba zata bashi daman haka ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa tuni majalisar dokokin kasar suka jingije aiki da hukumar saboda halayen munafursi na shugaban hukumar ta IAEA zuwa lokacinda Iran ta fahinci cewa za’a mutunta hakkinta.
Ministan ya kammala da cewa wannan shi ne sakamakon ayyukan Gorossi na munafurci a huldarsa da kasar Iran a hukumarsa.
Jiragen yakin Amurka samfurin B2 sun kai hare-hare a kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran guda 3 Natanz Fordo da kuma Esfhan. Trump ya bayyana cewa sun lalatasu kwata-kwata amma amma Iran ta musanta hakan, ta dai yarda an lalata wasu gine-gine kusa da su, amma ba mai hana aikin nukliya ya ci gaba ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.
’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSSWannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.
A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.
Cikakken rahoto na tafe…