Aminiya:
2025-10-22@21:51:32 GMT

HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina

Published: 1st, July 2025 GMT

An yi jana’izar fitaccen attajirin ɗan kasuwar nan Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina na ƙasar Saudiyya.

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Alhaji Aminu Ɗantata

এছাড়াও পড়ুন:

Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce babu wanda zai yi nasara wajen rusa tarihin Kano da aka kafa tsawon shekaru.

Ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Talata, yayin gabatar da littattafai biyu da Dokta Munzali Dantata, ya rubuta; Behind the City Wall da Aminu Dantata: Life and Times of a Nigerian Entrepreneur.

An gano sauro a karon farko na tarihin ƙasar Iceland Gwamnatin Borno rufe makarantun jihar saboda rigakafin ƙyanda da Polio

A cewar Sarkin, tarihin Kano ya samo asali ne daga tsohuwar al’ada ta jajircewa, ilimi, kasuwanci, da ƙwarewa.

“Mun zo nan ne don murna, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne muna taya Kano murna, birni wanda ya samar da iyalan Dantata kuma ya samar da wasu daga cikin attajiran Afirka,” in ji Sarkin Sanusi.

“Kano ta tashi ne a kan ginshiƙai na ƙwarewa, ko a addini, ilimi, kasuwanci, ko mu’amala. Na taɓa faɗa a baya: duk wanda yake tunanin zai iya rusa Kano yana ɓata lokacinsa ne. Ba zai yi nasara ba.”

Sarkin ya yi kira ga ’yan Najeriya, musamman mutanen Arewacin ƙasar, da su riƙa rubuta tarihinsu da labaransu da kansu.

 

“Dole ne mu riƙa faɗin labarinmu da kanmu,” in ji shi.

“Idan ba mu rubuta tarihimmu ba, wasu za su rubuta mana shi kuma ba za su bayyana shi yadda ya dace ba. Rubuta tarihi yana da muhimmanci domin kare ginshiƙinmu a ƙasa.”

Ya kuma yaba wa iyalan Dantata da sauran manyan ’yan kasuwa na Kano da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina jihar.

“Ba za a iya bayyana girman tarihin Kano ba tare da ambaton iyalan Dantata da sauran fitattun ’yan kasuwanta ba,” in ji shi.

Sarkin, ya ce tun da farko ya amince da ra’ayin Dokta Munzali na rubuta tarihin mashahuran ’yan kasuwar Kano.

“Lokacin da Munzali ya zo wajena da ra’ayin waɗannan littattafai, na ce masa dole ne mu rubuta namu labarin,” in ji Sarkin.

“Winston Churchill ya taɓa cewa, ‘Tarihi zai nuna mana adalci domin mu kanmu za mu rubuta shi.’ Waɗannan littattafai su ne tarihin al’umma baki ɗaya.”

Marubucin littattafan, Dokta Munzali Dantata, ya bayyana cewa littattafan biyu labarai ne na mutum ɗaya da al’umma waɗanda ke nuna ƙoƙari da ci gaban Kano.

“Waɗannan littattafai nawa labarai ne guda biyu; ɗaya na mutum ɗaya da ɗaya na al’umma, amma duk suna ɗauke da ƙoƙarin ci gaban kasuwanci,” in ji shi.

“Manufar Kano tana koyar da cewa arziƙin al’umma ba ya rabuwa da ƙoƙarin ’yan ƙasarta.”

Farfesa Munzali Jibril, ya yi nazarin litattafan yayin da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya kasance babban mai gabatarwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Waɗanda ke son rusa Kano ba za su yi nasara ba — Sanusi II
  • Yemen : An yi jana’izar babban hafsan sojin kasar Shahid al-Ghamari a Sana’a