Hamas ta karɓi tayin tsagaita wuta a Gaza
Published: 3rd, July 2025 GMT
Ƙungiyar Hamas ta sanar da karɓar tayin tsagaita wuta a yaƙin Gaza kuma tuni ta soma nazarin sabuwar yarjejeniyar aka gabatar mata.
Hamas wadda ta nuna alamun samun masalaha ta bayyana cewa manufar yarjejeniyar ita ce kawo ƙarshen hare-hare Isra’ila da janye dakarunta daga yankin.
Za mu ɗauki mataki kan mambobinmu da ke shirin shiga haɗakar ADC — PDP 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADCƘungiyar ta ce tana tuntuɓar abokan shawararta, sannan ta jinjina wa ƙoƙarin masu shiga tsakanin.
Shugaban Amurka ne ya gabatar da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kwana 60, wadda ya ce tuni gwamnatin Isra’ila ta amince da ita.
To sai dai rahotonni na cewa da dama cikin ministoci masu ra’ayin riƙau ba su gamsu da ita ba, yayin da Firaminista Benjamin Netanyahu ya dage cewa yana son kawo ƙashen Hamas.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sabani Tsakanin Bin Gafir, Smotresh Da Zamir Kan Makomar Fursinonin Yahudawa A Gaza
Barazanar babban hafsan hafsoshin sojojin HKI na fadada yaki a Gaza don kubutar da fursinoni yahudawa da suke hannun falasdinawa ya jawo cece kuce tsakaninsa da bin gafir da kuma Smotresh,
Kakafen yada labaran Ebri ko HKI sun bayyana cewa ministan kudi na HKI Betsal’il da kuma Smotresh ministan tsaron cikin gida na haramtacciyar kasar suna daga cikin wadanda suke adawa da ra’ayin babban hafsan sojojin mamayar Iyyal Zaamir wanda yake son gaggauta fadada yakin da yake jagoranta a Gaza don kubutar da fursinonin yahudawan da suke hannun kungiyar Hamas da sauran falasdinawa a gaza.
Smotresh da kuma Ben gafir suna ganin fadada yakin zai kasance hatsari ga rayuwar fursinonin.
Jaridar ‘Yadi’un-Ahrunut’ ta nakalto ministocin na fadar haka a taron ministocin haramtacciyar kasar kan cewa suna son fursinoni yahudawa su dawo da rayukansu ba gawaki ba. Don haka suna bukatar a san abinda za’a yi wand aba zai jefa rayukansu cikin harsari ba.