Gwamnatin Zamfara Ta Tabbatar Da Kashe Manyan Mayakan Bello Turji Fiye Da 100
Published: 29th, June 2025 GMT
Alhaji Ahmad Manga ya ce, “an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar gwamnatin jiha da gwamnatin tarayya”.
Jami’an CPG na Zamfara sun kuma samu goyon bayan dakarun Civilian JTF na jihar Borno, inda suka ƙaddamar da harin a-yi-ta-ta-ƙare na bazata ga maɓoyar ta Bello Turji.
Gwamnatin jihar Zamfara ta ce artabun na ranar Litinin da haɗin gwiwar jami’an tsaro suka fara da ɗan fashin dajin tamkar buɗe sabuwar ƙofar ci gaba da yaƙarsa ne.
“Alhamdulillahi an tarar da shi har gida nai inda ba a taɓa zuwa ba, kuma ya ga cewa ana iyawa, kuma an isko shi,” inji Ahmad Manga.
Ya ƙara da cewa “an kuma buga wuta, an yi nasarori da dama inda aka kashi mutanensa, wanda shi kansa bai iya ƙididdige abin da ya rasa, sai dai daga baya”.
Ya ce duk inda ka ga gawawwaki to akasari na yaransa ne.
Mataimaki na musamman kan sha’anin tsaron ya ce Bashari Maniya ya gamu da ajalinsa ne sakamakon hatsarin da motarsu ta yi lokacin da ta faɗa wani rami.
“Sabuwar mota ce wanda ba duk mutum ya san kanta ba, sun taka wani rami ne mai kama da rijiya kuma suna a guje, motar ta ƙwace kuma ta je ta faɗi. Ba wai shi ne ya yi nasarar buge motar ba, a’a.”
Ya ƙara da cewa lokacin da aka kai musu ɗauki an samu Maniya da sauran waɗanda ke cikin motar ne ba a hayyacinsu ba, saboda motar harbi ba ya ratsa ta.
Alhaji Ahmad Manga ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Zamfara za ta ci gaba da farautar Bello Turji ba rdare ba rana.
“Wallahi sai abin da ya ci gaba. Alhamdulillahi! Duk ɗan jihar Zamfara zai gaya maka musamman ɗan yankin Shinkafi sun sani, abin da aka yi shekara 14 yana gallaza wa mutane. Shi ya san rawar da jami’an tsaro suka taka yanzu ba a taɓa isko shi ba, irin yadda aka tarad da shi har gidansa.
Ya bayyana aniyar gwamnatin Zamfara na shigo da ƙarin dakarun sojoji don ci gaba da tunkarar Bello Turji
A cewarsa, ko a faɗan da aka yi ranar Litinin Bello Turji laɓewa ya riƙa yi, kafin daga bisani ya arce.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mummunan Hatsari Ya Lashe Rayukan ‘Yan Mata 18 A Kasar Masar Dukkaninsu ‘Yan Kasa DA Shekara 21
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai
Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin.
Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18. Dukkansu sun fito ne daga kauye daya, Kafr El-Sanabseh, a gundumar Menoufia, kuma dukkansu ‘yan kasa da shekara 21 ne.
Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda motar bas din ta lalace gaba daya. Hotunan akwatunan gawarwakin ‘yan matan da aka jera su sun haifar da bakin ciki sosa a tsakanin al’umma.
Jami’an tsaro sun cafke direban babbar motar da ke da alhakin hatsarin bayan ya arce daga wurin. An mika shi ga ofishin gabatar da kara na gwamnati, wanda ke gudanar da bincike.