Yawan Kudin Shiga Da Sin Ta Samu A Fannin Sana’ar Manhaja A Watanni 5 Na Farko Na Bana Ya Wuce Yuan Triliyan 5.5
Published: 2nd, July 2025 GMT
Yau Laraba, Hukumar Kula da Fasaha ta Kasar Sin (MIIT) ta ba da rahoton yanayin tafiyar masana’antar manhajoji ta kasar daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2025 da muke ciki.
A cewar rahoton, masana’antar manhaja da hidimar fasahar sadarwa ta Sin tana gudana yadda ya kamata. Da farko, yawan kudaden shiga da aka samu kan sana’ar manhaja ya karu karara.
Na biyu, ribar da aka samu a fannin kuma ta habaka da kashi 10% ko fiye. Daga Janairu zuwa Mayu, jimilar ribar da aka samu a bangaren sana’ar manhaja ta kai kudin Sin yuan biliyan 672.1, wadda ta karu da kashi 12.8 cikin dari kan na makamancin lokacin bara.
Na uku, yawan manhajojin da aka fitar ya ci gaba da karuwa cikin inganci. A cikin watanni biyar na farkon bana, darajar kayayyakin manhaja da aka fitar ya kai dalar Amurka biliyan 22.71, adadin da ya karu da 3.3% bisa na makamancin lokacin a bara. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Hori Ma’aikatan Lafiya Su Kara Kokari Wajen Rike Aikin su
Shugaban hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitoci kula da lafiya a matakin farko ta kasa Alhaji Dr Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya hori ma’aikatan kiwon lafiya a matakin farko da dukkannin masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya su rubanya kokari fuskar tabbatar da kwarewa domin inganta ayyukan kula da lafiya a Nijeriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya yi wannan kiran ne a Katsina lokacin bukin rufe taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku na wannan shekarar wanda aka shiryawa Malaman koyar da darusan kiwon lafiya a matakin farko.
Taron wanda ya samu halartan jami’an kiwon lafiya daga dukkannin jihohin yankin arewa maso yamma, yana da nufin ilimintar dasu ne kan yadda za su rungumi sabbin dabarun aiki irin na zamani dai dai da tsarin dokokin hukumar kula da makarantun kiwon lafiya da bada lasisi ga likitocin kula da lafiya a matakin farko ta Naheriya.
Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya bayyana cewa wajibi ne dukkannin ma’aikatan hukumar da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya a matakin farko su kara zama masu kwazo tare da yin aiki da sauran dokokin aiki na fasahohin zamani domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Don haka shugaban hukumar ya sake yin kira ga malarta taron su yi amfani da abubuwan da suka koya yadda suka dace domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a Naheriya.
Maryam Idris