Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun sake yi wasu sabbin kutse a yankunan Quneitra na kasar Siriya

Rahotonni sun bayyana cewa:  Da sanyin safiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kutsa cikin yankunan garin Saida da kuma kauyen Abu Mathra da ke yankin kudancin Quneitra na kasar Siriya. 

Wannan ya zo daidai da wani sintiri da sojojin mamayar Isra’ila da ke ci gaba da yi a kauyen Kodna da ke cikin karkarar Quneitra, ba tare da wata arangama ko gargadi daga mahukuntan Siriya ba.

Ana ci gaba da yin shiru a hukumance dangane da irin wadannan tsauraran matakan da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a kan iyakar kasar da tuddan Golan na Siriya da ta mamaye, lamarin da ya sanya ayar tambaya na cikin gida da na kasa da kasa game da yanayin tsaro a yankunan.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Siriya ta sanya ido kan yadda sojojin mamayar Isra’ila da suka hada da tankar yaki da mota mai sulke da kuma babbar mota dauke da sojoji kusan 30, inda suka kutsa cikin kauyen al-Samadaniyya al-Sharqiya da ke cikin yankin Quneitra. Sojojin mamayar Isra’ila sun binciki gidaje da dama kafin su janye zuwa sansanonin su, ba tare da samun rahoton kama mutane ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila kasar Siriya

এছাড়াও পড়ুন:

Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’
  • Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
  • Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida 
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fushin Sojojin Kasar
  • Iran Tace Ma’aikatar Harkokin Waje Kasarce Take Kula Da Lamuran Makamacin Nukliyar Kasar
  • Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata
  • Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli
  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre