Sabani Tsakanin Bin Gafir, Smotresh Da Zamir Kan Makomar Fursinonin Yahudawa A Gaza
Published: 1st, July 2025 GMT
Barazanar babban hafsan hafsoshin sojojin HKI na fadada yaki a Gaza don kubutar da fursinoni yahudawa da suke hannun falasdinawa ya jawo cece kuce tsakaninsa da bin gafir da kuma Smotresh,
Kakafen yada labaran Ebri ko HKI sun bayyana cewa ministan kudi na HKI Betsal’il da kuma Smotresh ministan tsaron cikin gida na haramtacciyar kasar suna daga cikin wadanda suke adawa da ra’ayin babban hafsan sojojin mamayar Iyyal Zaamir wanda yake son gaggauta fadada yakin da yake jagoranta a Gaza don kubutar da fursinonin yahudawan da suke hannun kungiyar Hamas da sauran falasdinawa a gaza.
Smotresh da kuma Ben gafir suna ganin fadada yakin zai kasance hatsari ga rayuwar fursinonin.
Jaridar ‘Yadi’un-Ahrunut’ ta nakalto ministocin na fadar haka a taron ministocin haramtacciyar kasar kan cewa suna son fursinoni yahudawa su dawo da rayukansu ba gawaki ba. Don haka suna bukatar a san abinda za’a yi wand aba zai jefa rayukansu cikin harsari ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Falasdinu: Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar HKI suna ci gaba da kai hare-hare a yammacin kogin Jordan, inda a safiyar yau lahadi su ka kutsa cikin wani gida a garin Jenin,kamar kuma yadda ‘yan share wuri zauna su ka kutsa gidan wani bafalasdine a kudancin Nablus.
Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu suna cewa; an yi taho mu gama a tsakanin Falasdinawa da ‘yan mamaya a garin Tal a kudancin Nablus.
A sansanin ‘yan hijira na Jenin sojojin na mamaya sun tarwatsa wani gida na Bafalasdine wanda ya haddasa tashin hayaki da kuma jin kara mai tsanani a sassa mabanbanta na garin Jenin.
Haka nan kuma ‘yan mamayar sun yi amfani da motar Buldoza wajen rusa wasu gidaje a sansanin na Jenin.
A makon da ya shude ma dai ‘yan mamayar sun rusa wasu gidaje masu yawa na Falasdinawa a yammacin Kogin Jordan a karkashin shirinsu na rusa gidaje 95.
A garin Tubas da yake a wannan yankin Iyalai da dama sun yi hijira saboda kaucewa hare-haren da ‘yan share wuri zauna suke kai musu.
Tun bayan 7 ga watan Oktoba na 2023 Amurka take goyon bayan HKI a yi wa Falasdinawan Gaza, kisan kiyashi da kuma kwacewa Falasdinawan yammacin Kogin Jordan gidajensu da zummar korarsu daga yankin.