2025-08-14@17:54:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7812
«karin kudin mai a»:
Wasu mutum biyu da ake zargin ɗaliban jami’a ne a Jihar Bayelsa sun mutu bayan wata mota ƙirar tifa ta murƙushe su lokacin da suke kan babur mai ƙafa uku a kan hanyar Tombia zuwa Ammassoma. Daily Trust ta samu rahoton cewa haɗarin wanda ya afku a ranar Talata, ya kuma sa wasu fasinjojin da ke cikin babur ɗin sun samu munanan raunuka. Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun A cewar wasu mazauna yankin, haɗarin ya afku ne a kusa da wani lanƙwasa mai haɗarin gaske a kan babbar hanyar, sakamakon rashin kyan hanyar da kuma gudun wuce ƙima. Sun ce babbar motar...
A yayin da yake martani kan suka da ake yi masa na rashin gabatar da kudirori a gaban majalisar, ya bayyana cewa, “tun da na je Majalisar, ba bu wani dan mazabata da ya rubuto min wani kudiri ko bukata da zan gabatar a gaban Majalisa, duk zarge-zargen karya ne suke yi min, kuma idan har akwai, wani ya fito ya kalubalance ni,” inji shi. “Hatta gabatar da kudirori da korafe-korafe a majalisar, sai an biya kimanin naira miliyan 1, ko naira miliyan 2, ko naira miliyan 3, domin karantawa a zauren majalisar, bayan an karanta kudirin, sai ka bibiyi ‘yan majalisa sama da 360 domin su goyi bayan a amince da kudirin.” Dan majalisar ya kuma yi...
Ya kara da cewa, kasar Sin tana kira ga kasa da kasa su ci gaba da tallafa wa ayyukan UNRWA, yana mai cewa a shirye Sin take ta yi abun da zai kawo karshen rikicin da samar da mafita mai adalci da dorewa bisa manufar kafa kasashe biyu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sabuwar mai bada shawara kan harkokin lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan_islam) ta bayyana cewa samar da dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne fatansu. Maryam ta bayyana hakan ne a lokacin da babban jami’in kula da ayyukan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mohammed Malick Fall, ke maraba da ita a ofishin majalisar da ke Abuja. An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Mohammed ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake buƙata don jin daɗin rayuwar ɗan Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuraɗiyya da...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku. Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata. Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Odutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku. Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF,...
“Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar ‘yan bindiga,” in ji shi. Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya ɗauki matakaki a kan waɗanda suka aikata wannan kisan gilla, sannan ya roƙi jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin kawo ƙarshen duk wata ɓarna a Zamfara. Sarkin Kauran Namoda, Dokta Sunusi Ahmad Rashad, wanda ya raka gwamnan, ya yaba masa bisa saurin ɗaukar mataki bayan faruwar lamarin. “Wannan ziyara tana da...
Gwamnatin Tarayya ta amince a kafa karin sababbin jami’o’i masu zaman kansu guda guda tara a fadin Najeriya. Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya sanar da hakan ranar Laraba lokacin da yake jawabi ga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa jim kadan da kammala taron Majalisar Zartarwa ta Kasa. Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron wanda aka gudanar a Abuja. A cewar ministan, sababbin jami’o’in da aka ba lasisin sun hada da Jami’ar Tazkiyah da ke Kaduna, Jami’ar Leadership da ke Abuja, Jami’ar Jimoh Babalola da ke Kwara da Jami’ar Bridget da ke Mbaise a...
Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa (DHQ), ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewar ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji, ya miƙa wuya ba gaskiya ba ne. Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye ne, ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja a ranar Alhamis yayin bayani kan ayyukan sojoji. Rashin Lantarki: Babu wanda za mu zaɓa a 2027 — Jama’ar Talasse Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons Ya ce: “Turji bai miƙa wuya ba. Har yanzu muna neman sa.” Turji na daga cikin manyan ’yan bindigar da ake nema ruwa a jallo a Najeriya. Turji ya jagoranci kai wa al’umma hare-hare a Jihohin Zamfara da Sakkwato, inda suka...
Al’ummar garin Talasse da ke Ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe, sun ce sun gaji da rayuwa cikin duhu har na tsawon shekaru 19. Sun kuma bayyana takaicinsu bayan tsayawar aikin wutar lantarki da ya tsaya. Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe Aikin, wanda ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Billiri da Balanga, Ali Isa JC, ya fara tun farkon wannan shekara, ya sanya al’ummar yankin farin ciki bayan an kafa turakun wuta da na’urorin taransifoma. Sai dai cikin watanni biyu da suka gabata, aikin ya tsaya ba tare da wani bayani ba. “Yan siyasa su kan zo da alƙawura a lokacin zaɓe, sannan...
Dukkanin mutanen biyu na Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar, kuma za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike. Kwamishinan ’Yansandan jihar, Emmanuel Olugbemiga Adesina, ya gargaɗi masu aikata laifi su daina ko su bar jihar. Ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki don tabbatar da masu laifi sun fuskanci hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Yi Tsokaci Kan Furucin Netanyahu Game Da Kafa “Babbar Kasar Isra’ila’
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tsokaci kan furucin Netanyahu game da kafa ‘Babban Kasar Isra’ila’ Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana a safiyar yau alhamis cewa: Kafafen yada labaran yammacin duniya a al’ada na zargin duk wanda ya ambaci ra’ayin ‘yan sahayoniyya na kafa “Babban kasar Isra’ila” da kiyayya ga wata al’umma. Bayanin Araqchi, wanda aka yi da sanyin safiyar Alhamis a shafinsa na yanar gizo na dandalin sada zumunta na X, yana mai mayar da martani ga kalaman fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu game da batun kafa “Babban kasar Isra’ila.” A cikin shafinsa na yanar gizo, Araqchi ya yi tambaya cewa: “Shin suna daukan furucin Netanyahu kansa a matsayin mai adawa da wata...

Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”. Wadannan kalamai tana nuna karara aniyar gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasashe masu cin gashin kansu da suka hada da Masar, da Jordan, da Lebanon da kuma Syria, tare da la’akari da su a matsayin babban misali na keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa. A cikin wani rubutu da...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya Bayyana cewa: Shugabannin gwamnatin nuna wariyar al’umma suna kokarin yaudarar al’ummar Iran A martaninsa ga fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ya yi a baya-bayan nan, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Kasar Iran a yayin da yake gabatar da wasu takardu kan matsalar karancin ruwa da kuma matsalar fari a yankunan da aka mamaye na Falasdinu, ya bayyana cewa; ‘Yan Nazi na karni na 21, wadanda suka kai hari kan babbar tashar ruwa da ke arewacin birnin Tehran a dandalin Tajrish da makami mai linzami, a yanzu haka suna kokarin yaudarar al’ummar Iran da kofin ruwa da aka yi masa magani. Amma al’ummar Iran a tsawon tarihi, sun dauki ko da mafi gogaggen...
Gwamanatin Sudan ta yi maraba da sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na yin Allah wadai da shirin kafa gwamnatin hadaka a kasar Sudan Sudan ta yi marhabin da sanarwar da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar a jiya Laraba, inda ta yi watsi da shirin dakarun kai daukin gaggawa na kafa gwamnatin hadaka a yankunan da ke karkashinta. Sanarwar ta yi gargadin cewa wannan matakin na barazana ga hadin kan kasar, kuma yana iya yin kasadar kara ta’azzara rikicin, yayin da aka dakile wani hari da dakarun kai daukin gaggawa na kungiyar Rapid Support Forces suka kaddamar a yankin kudu da kudu maso yammacin birnin El Fasher. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar...
Lauyan Maïga, Cheick Oumar Konaré, ya bayyana cewa kamun bai dace ba saboda Maïga ba shi da niyyar guduwa ko lalata shaidu, yana kuma zargin cewa wannan wani mataki ne na siyasa saboda tsohon Firaministan ya daɗe yana sukar gwamnatin soja tun bayan tsawaita mulkinsu ba tare da gudanar da zaɓe ba. Maïga, ya hau kujerar Firaminista a watan Yulin 2021 bayan gwamnatin sojoji ta yi juyin mulki, inda ya goyi bayan dakatar da shirye-shiryen zaɓe don bai wa gwamnatin soja ƙarin lokaci. Sai dai daga baya ya fara sukar wasu matakan gwamnati, musamman bayan an dakatar da shi daga kujerarsa a watan Nuwamban 2024. Tun bayan juyin mulkin 2020 da na 2021, Mali ta kasance ƙarƙashin mulkin soja, kuma...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi mai shekara 18 bisa zargin aikata fashi da makami a jihar. An kama shi ne a garin Kwadon bayan samun sahihin bayani daga jama’a. NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi a Gombe ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama matashin ne ranar 9 ga watan Agusta, 2025 da misalin ƙarfe 2:30 na rana. Hakazalika, ya ce an samu ƙunshi ganyen da ake zargin tabar wiwi ne. Bincike ya nuna cewa matashin na cikin mutanen da ’yan sanda ke nema game da aikata fashi da makami, waɗanda ake shari’arsu a babbar kotun jihar. A cewar DSP Abdullahi,...
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a Jihar Gombe ta ce ta lalata wata babbar gonar Tabar wiwi a Karamar Hukumar Kaltungo a jihar Gombe. Hukumar ta kuma ce ta kama miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai miliyoyin naira tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025. ’Yan ci-rani 26 sun nitse a teku suna ƙoƙarin tsallakawa Turai Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Kwamandan Hukumar a jihar, Mallam Maijama’a Muhammad ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar kulla zumunci da ya kai wa Darakta-Janar na kafar yada labarai mallakar jihar Gombe (GMC), Ibrahim Isa. Ya ce an kama mutum 69 maza da mata da suke kokarin shigar da miyagun kwayoyi cikin jihar a wasu lokuta. Muhammad...

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Ta Bayyana Rashin Gamsuwa Da Manufar Shugaba Trump Ta Korar Marasa Galihu
Sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ya kuma nuna cewa, kaso 92 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na bayyana matukar damuwa game da tsaron rayukan al’ummun Amurka, yayin da kaso 81.7 bisa dari suka ce muggan laifuka, da karuwar masu kwana a kan tituna sun zamewa manyan biranen Amurka alakakai, lamarin da ya zamo cutar Amurka mai matukar wahalar magani. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da hukumomi masu ruwa da tsaki domin hanzarta shari’o’i da kuma rage cunkoson gidan yarin. A lokacin ziyarar, ya lura da cewa yawancin fursunonin na zaune a ƙasa babu katifa. Don inganta rayuwarsu, ya umarci a samar musu da katifu 500. Gwamna Sule ya yaba wa jami’an gidan yari da sauran jami’an tsaro saboda sake kama wasu daga cikin waɗanda suka tsere. Ya kuma roƙi jama’a da su kasance cikin shiri su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga wani mai kama da wanda ake nema. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Akalla ’yan ci-rani 26 sun mutu bayan jiragen ruwan da suke ciki guda biyu sun nitse a teku a kusa da tsibirin Lampedusa na ƙasar Italiya. Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ana hasashen ƙarin wasu mutanen kuma sun ɓace yayin da ake ci gaba da aikin ceto su. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Galibi dai ’yan ci-ranin da suka fito daga ƙasashen Afirka na ƙoƙarin tsallakawa nahiyar Turai ne domin samun ingantacciyar rayuwa. Ko a ranar Laraba dai ma’aikatan ceto sun ce sun ceto mutum 60 da ransu, wadanda suka hada da maza 56 da kuma mata hudu, sannan aka...
Shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Berri ya tarbi Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran a hedikwatar shugaban kasa ta biyu dake Ain al-Tineh. Larijani ya tabbatar da cewa bayan ganawar da aka yi tsakanin kasashen Labanon da Iran lamarin ya yi kyau da armashi. Ya jaddada cewa Iran ba ta da niyyar yin katsalandan a cikin harkokin cikin gidan kasar Labanon, yana mai cewa bai kamata wasu kasashe su ba da umarni ga gwamnatin Lebanonba, musamman kan wasu batutuwa masu sarkakiya wadanda al’ummar Lebanon ne tare da gwamnatinsu kawai za su iya yanke shawarar a kansu. Larijani ya jaddada cewa Iran ba ta zo da wani shiri a Labanon ba, sai dai Amurkawa sun zo ne...
Masar ta yi Allawadai da kalaman Benjamin Netanyahu game da abin da ya kira shirinsa na kafa babbar kasar yahudawa ko kuma Isra’ila Babba. Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Masar ta fitar, bayan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana kan wanann batu, wanda ya tayar da hankulan Larabawa kuma suka yi watsi da shi. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce “tana tabbatar da aniyarta ta abbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tare da yin Allah wadai da abin da wasu kafafen yada labaran Isra’ila suka ruwaito dangane da abin da ake kira Isra’ila Babba. Ya yi bayanin cewa, “ya bukaci a yi karin haske kan hakan, bisa...
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe wani tsohon malami kuma manomi, Andrew Imuekheme, a Jihar Edo. Lamarin ya faru ne a ranar Talata a garin Ikabigbo, da ke Masarautar Uzairue, a Ƙaramar Hukumar Etsako ta Yamma. Allah zai kunyata masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Zamfara — Gwamna Dauda Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya Rahotanni sun ce Malam Andrew na kan hanyarsa daga gona lokacin da maharan suka tare shi, tare da ɗauke shi zuwa daji. Wata mata da ta tsere daga hannun maharan ta koma cikin gari tare da sanar wa mafarauta, waɗanda suka fara bincike nan take. Tuni jami’an tsaro suka umarci manoma da ke da gonaki a kusa da yankin da su koma gidajensu...
Ministan harkokin wajen Yemen Jamal Amer a ranar Laraba ya karbi wata wasika daga Dr. Khalil al-Hayya shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda wakilin kungiyar a Sanaa, Moaz Abu Shamala ya mika. A cikin wasiƙar nasa, al-Hayya ya bayyana matuƙar godiyar Hamas ga sadaukarwa da tsayin dakan al’ummar Yemen, yana mai bayyana su a matsayin “‘yan’uwa na gaskiya, Ansar Allah,” a tinkarar mamayar Isra’ila da kawayenta duk da gagarumar sadaukarwa, barazana, da hare-hare. Ya tabbatar da cewa nisan da kasar Yamen ke da shi da Falasdinu ya kara dankon kusancinta da al’ummar Palastinu ne kawai da kuma kudurinta na ci gaba da ba da taimako da taimako da kuma kare Gaza da Palastinu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe...
Wani mazaunin Safana, Iliyasu Sani, ya ce sulhun ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, domin yanzu suna iya zuwa kasuwa da yin noma ba tare da fargaba ba. Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce talauci da rashin tsaro ne suka sa jama’a neman mafita da kansu. Ya kuma bayyana cewa idan duk ɓangarorin suka tsaya kan alƙawarin da aka yi, wannan sulhu na iya zama mataki na farko na samun zaman lafiya na dindindin a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da kara wayar da kan direbobi da fasinjoji da Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta ce tana yi, ana kara samun ƙaruwar wadanda ke rasa rayukansu sakamakon hadura a titunan kasar nan. A shafinta na internet, FRSC ta ce a watanni uku na farkon 2024, mutane 1,471 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota. Kazalika, a watanni uku na farko na wannan shekara ta 2025, adadin ya haura zuwa mutane 1,593 — karin mutum 122, ko kuma kashi 8.3 cikin dari. NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci...
Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya ziyarci wasu garuruwa a Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda, bayan jerin hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Gwamnan, ya la’anci kisan gillar, tare da bayyana shi a matsayin marasa imani, kuma Allah zai fallasa su ya kunyata su. Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 A ranar Laraba, ya ziyarci ƙauyuka biyar da abin ya fi shafa; Banga, Sakajiki, Kuryar Madaro, Maguru, da Tambarawa, inda mutane da dama suka rasa ’yan uwansu. Bayan samun labarin hare-haren, nan da nan ya tura mataimakinsa ya je ya jajanta wa mutanen da abin ya shafa. Bayan dawowarsa Gusau, ya je da kansa...
A yayin ziyarar, Gwamna Lawal ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu tare da tabbatar wa al’ummar yankin ƙudurinsa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, gwamnan ya yi kakkausar suka ga hare-haren da ’yan bindiga ke kai wa a baya-bayan nan, yana mai cewa da gangan maƙiya ke nufin waɗannan munanan ayyuka don yaɗa tsoro a tsakanin al’umma. “Na ziyarci garin Banga ne domin jajanta wa jama’a game da harin da ‘yan bindiga suka kai a kwanakin baya. “Lokacin da abin takaicin ya faru, na kasance ba na kusa, amma daga samun labarin, na umarci mataimakin gwamna da ya jagoranci wata babbar tawaga domin ziyarar jaje. “A jiya ne na dawo...
Muryoyi daga ko’ina cikin duniya sun nemi a warware matsalar bisa turbar adalci. Shugabannin tarayyar Turai sun yi ta kira ga kasashen Sin da Amurka da su kiyaye bude kasuwanni da gudanar da gasa ta gaskiya. Kasashen kudu maso gabashin Asiya, sun ba da shawarar tabbatar da kwanciyar hankali. Kasashen Afirka da na Latin Amurka sun nuna damuwa da halin da ake ciki saboda barazanar da lamarin yake yi ga damarmakin zuba jari da kasuwancin kasashensu. Gyaruwar dangantakar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka za ta iya haifar da wani sabon zamani na hadin gwiwa, da kirkire-kirkire, da ci gaban da ya kunshi kasashen duniya baki daya. A wannan duniyar tamu wadda bukatar hada hannu da juna ke kara bayyana,...
Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi Wannan mataki, a cewar Ministan Ilimi Dakta Olatunji Alausa, an ɗauke shi ne domin rage yawan makarantun da ba a amfani da su yadda ya kamata, lamarin da zai ba da damar mayar da hankali wajen gyara da inganta waɗanda ake da su yanzu. Da yake zantawa da manema labarai bayan taron na FEC a fadar shugaban ƙasa ranar Laraba,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan Alhamis din zai bar Abuja domin fita ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ta tabbatar. Sai dai gabanin isa ƙasashen biyu, Tinubu zai soma yada zango a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa sannan daga bisani ya ƙarasa Japan. An naɗa sabon Sarkin Alkaleri a Bauchi Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe A yayin da shugaban yake Japan, zai halarci taron Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) karo na tara a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta. Taken taron na bana shi ne “Haɗa Hannu da Afirka Wajen...
Tinubu ya yi kira da a sake duba kudaden gudanar da aikin NNPC da ake cire kashi 30 cikin 100 wanda doka ta tanadar a karkashin dokar masana’antar mai. Shugaban ya bayyana godiya ga mambobin majalisar bisa jajircewarsu da aiki tukuru wajen aiwatar da gyare-gyare masu tsauri da wahala wadanda suka dabaibaye ci gaban tattalin arzikin kasa a baya, amma a yanzu, za su karfafa kwarin gwiwar masu zuba jari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dr) Rilwanu Suleiman Adamu, ya naɗa tsohon babban jami’in Hukumar Kwastam mai ritaya, Alhaji Bala Muhammad Gidado, a matsayin Sarkin Alkaleri, wanda zai gaji marigayi Sarkin Alkaleri, Alhaji Muhammad Abdulkadir. Da yake jawabi yayin naɗin, Sarkin Bauchi ya jaddada cewa sabon Sarkin Alkaleri ya samu wannan muƙami ne bisa la’akari da cancanta, ilimi, gogewa da kuma nagarta. Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno Ya buƙaci sabon sarkin da ya yi amfani da wannan gogewa wajen ci gaban masarauta, tare da tabbatar da gaskiya, adalci, riƙon amana da haɗin kan jama’a. Sarkin ya yi addu’ar Allah Ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa kasashen yamma masu babakere kan al-amura a duniya suna son haramtawa mutanen kasar Iran ilmin zamani da kuma ci gaba a fasahar Nukliya. Amma gwamnatin kasar Iran ta dage kan cewa yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar ba zai hana ta ci gaba da shirinta na makamashin nukliya ba. A wani bangare a maganarsa, shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran...
Hukuma mai kula da sauka da tashin jiragen sama a birnin Paris ya dakatar da wani ma’aikacinsa, wanda yake aikin a bangaren kula da sauka da tashin jiragen sama, saboda ya shelantawa wani jirin HKI wanda ke kokarin sauka a tashar jiragen kan cewa “yanci-yenci Falasdinu”. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar kafafen yana labarai na kasar Faransa na cewa, ma’aikacin ya fadi wadannan kalmomi ne ga matukin HKI wanda ya tashi a tashar ‘Charles de Gaulle’ da ke birnin Paris. Labarin ya kara da cewa matukin jirgin ne ya bada wannan rahoton ga hukumomin kasar Faransa don daukar matakin da ya dace. Ba’a bayyana sunan ma’aikacin ba, amma a jiya talata ce hakan ya auku,...
Jakadan kasar Irak a washintong ya bayyana cewa kasar Iraki entacciyar kasa she, tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da ko wace kasa da take so, wannan bayan korafin da gwamnatin Amurka tayi na yarjeniyar tsaro wacce kasar Iraki ta kulla da JMI. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jakadan yana cewa, kasar Iraki tana da yencin kulla yarjeniyar tsaro da kasashe makobta musamman kasar Iran wacce take da iyaka da mai tsawo da ita don samun amincin a kan iyakokin kasashen biyu. Ba ruwammu da abinda wani yake yake cewa. Tehran ta bagdaza dai suna da dangantakan tsaro mai karfi da juna, tun bayan samun nasara da Daesh, kuma suna haka kai don tabbatar da cewa...
Miistan harkokin wajen kasar Masar ya sake ganawa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi da kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya Rafael Grossi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labarana Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar na cewa jami’am gwamnatin kasashen biyu da kuma Grossi sun tattauna al-amura da suka shafi sake komawa kan taburin tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya ne bayan yakin kwanaki 12 wadanda HKI da Amurka suka kaiwa kasar Iran. Badar Abdullatf ministan harkokin wajen kasar Masar yana kokarin sake maida dangantakar hukumar AIEA da kuma Iran bayan tayi tsami a watan yunin da ya gabata, inda Iran tana zargin Grossi da hada kai da Amurka...
Shin kun san, a lokacin da Sinawa suka hadu da juna, gaisuwar da suke yi ita ce, “Shin ka ci abinci?” Wannan gaisuwa mai sauki tana nuna damuwar mutanen dake rayuwa bisa aikin noma, wato ma’ana, tambaya ce a kan ko ana da isasshen abinci? A halin yanzu, wannan gaisuwa mai cike da nuna damuwa, tana samun sauyi mai ban sha’awa a yankunan karkarar kasar Sin. Dai Yihui, wadda ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba, ta koma garinta na lardin Jiangsu, domin kula da gandun noma na iyalinta, inda ta yi kokarin kara yawan amfanin gona da kashi 35 bisa dari ta hanyar amfani da injunan noma na fasahar zamani, sai dai kuma mazauna garin sun canza gaisuwar...
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Gombe, mai wakiltar Nafada ta Kudu, Adamu A. Musa, ya zargi gwamnati da ‘yan majalisun jihar da kasa aiwatar da dokokin da suke zartarwa. Ya ce akwai dokar da aka zartar shekaru takwas da suka gabata domin yaƙi da fyaɗe da cin zarafin mata da yara, amma har yanzu ba a aiwatar da ita ba. Sojoji sun kashe babban Kwamandan ISWAP, Amirul Fiya a Borno Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki A cewarsa, majalisa tana yin doka sannan ta tura wa gwamna ya sanya hannu, amma daga baya a bar ta kamar ba ta da amfani. Ya yi gargaɗin cewa irin wannan sakaci yana ƙara wa masu aikata laifi ƙwarin guiwa...
Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya gode wa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya saboda ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin GOSTEC aiki a matsayin cikakkun ma’aikata. Ya ce wannan mataki ya nuna jajircewar gwamnati wajen taimaka wa matasa domin rage zaman banza da kuma ba su damar dogaro da kai. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Gwamnatin Gombe za ta ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13 Ya ƙara da cewa, yanzu wasu daga cikin matasan sun za su hidimata wa al’umma, saɓanin halin da suke ciki a baya. Ya roƙi matasan su zama masu gaskiya, riƙon amana da kishin ƙasa, inda ya bayyana cewa su ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. Ɗaya daga cikin...
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya miƙa ƙudiri zuwa Majalisar Dokokin Jihar domin neman amincewarta a ƙirƙiri sabbin ƙananan hukumomi 13. Gwamnan, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa gwamnati wajen kusantar al’umma, da ayyukan raya ƙasa. Jama’a sun koka kan rashin kammala aikin titi a Kafanchan Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki Sabbin ƙananan hukumomin da ake shirin ƙirƙira za su fito daga ƙananan hukumomin da ake da a jihar. A cewar gwamnan sabbin ƙananan hukumomin za su mayar da hankali kan samar da tsaro, ilimi, kiwon lafiya, gina muhalli da sauran muhimman ayyukan jama’a musamman a yankunan karkara. Za su kuma yi aiki tare da masarautu da shugabannin al’umma wajen tabbatar...
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugaban sun hada da kara farashin kudin takin gwamnati daga ₦20,000 zuwa ₦22,000 kan kowane buhu; hada rikici tsakanin shugabannin Siyasar yankin; raba kan Kansilolin karamar hukumar; tsunduma cikin harkokin siyasa masu raba kan jama’a ta hanyar bayar da dukiyar gwamnati ga abokan siyasarsa kawai; da dai sauransu. Kwamitin majalisar, ya zauna da bangarorin biyu a ranar Talata, 12 ga watan Agusta inda shugaban ya yi watsi da wasu zarge-zargen da cewa, ba su da tushe balle makama, amma ya amince da karin farashin kudin takin gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar Ci Gaban Masarautar Jama’a (JEDA), ta roƙi Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, da ya kammala manyan titunan Birnin Kafanchan, wanda aikin ya tsaya tun zamanin Nasir El-Rufai. Muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Ahmad Usman Husain, ya ce waɗannan tituna na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki da rayuwar yau da kullum a Kudancin Kaduna. Majalisar Kano ta dakatar da ciyaman kan zargin karkatar da taki Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura Ya ƙara da cewa abin takaici ne a ce ba a haɗa titunan Kafanchan cikin jerin sabbin ayyukan da gwamnan ya ƙaddamar ba, duk da cewa ya yi alƙawarin kammala su a lokacin yaƙin neman zaɓe. Ƙungiyar ta bayyana Kafanchan a matsayin cibiyar...
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda shi ne shugaban masu rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala, ya ce binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da kansiloli tara daga cikin goma na Rano suka sanya wa hannu. A cewarsa, ƙorafin ya zargi shugaban da yin sakacin kuɗi, sayar da shaguna, da karkatar da takin zamani da aka ware wa ƙaramar hukumar, tare da wasu zarge-zarge daban. Lawan ya bayyana...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina. Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78. Daga Bello Wakili
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta dakatar da Shugaban Ƙaramar Hukumar Rano, Muhammad Nazir Yau, na tsawon wata uku domin gudanar da bincike kan zargin yin amfani da kujerarsa ba bisa ƙa’ida ba. Kansilolinsa sun zarge shi da karkatar da kayayyaki da kuma almundahana wajen tafiyar da dukiyar jama’a. Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno Lafiyar Tinubu kalau – Soludo An yanke wannan hukunci ne bayan majalisar ta karɓi rahoto daga kwamitin karɓar koke-koke na jama’a, wanda shugaban marasa rinjaye na majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa, ya jagoranta a zaman ranar Laraba. Majalisar ta kuma umarci ma’aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu ta jihar da ta bai wa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar damar riƙon...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya karbi bakuncin Mataimakin Ministan Noma na Jamhuriyar Liberia, David Akoi, a wata ziyara ta musamman domin nazarin dabarun noman shinkafa a jihar, wadda ita ce kan gaba a fitar da shinkafa a Najeriya. A yayin ziyarar ban girma a fadar gwamnati da ke Dutse, Mista Akoi ya ce wannan ziyara za ta ba tawagarsa damar fahimtar dabarun noma da sarrafa shinkafa, samun horo a aikace, tare da koyo game da dukkan sassan harkar noman shinkafa. Ya bayyana cewa, wannan zai taimaka wa Liberia rage dogaro da shinkafar da ake shigowa da ita daga waje. “A Liberia muna cin shinkafa safe, rana da dare. A shekarar 1979, an yi tarzomar shinkafa da ta kifar...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama. A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni, amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.” Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda...
Dubban mazauna garin Kirawa da ke jihar Borno da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu, sun ce yanzu kullum a kasar Kamaru suke saboda gudun harin ’yan Boko Haram cikin dare. Mutanen, wadanda yanzu haka ke samun mafaka a kauyukan kasar ta Kamaru, sun kuma koka da halin kuncin da suke ciki a yanzu. ‘Zan iya shiga mummunan yanayi idan Dangote bai aure ni ba’ Lafiyar Tinubu kalau – Soludo Mazauna yankin shin shaida wa wata kafar yada labarai a ranar Talata cewa tun bayan harin da aka kai ranar Asabar da ya kai ga janye sojoji daga yankin mazauna kauyuka da dama sun bazu a kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru. Sun kuma ce a sakamakon haka,...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da bikin makon shari’a na shekarar 2025 wanda ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) reshen jihar Jigawa ya shirya, inda ya yi kira da a ƙara ƙarfafa bin ƙa’idojin aikin shari’a da hanzarta gudanar da shari’a a duk fadin jihar. A jawabinsa wajen bikin bude taron a Dutse, Gwamna Namadi ya yaba wa shugabannin NBA bisa hadin kai da kwarewarsu wajen gudanar da aiki. “Na shafe watanni da dama ina bin diddigi da sha’awar yadda kuka kafa, tare da gudanar da ayyukan kungiyar reshen jihar, cikin haɗin kai da ƙarfafawa, inda ya zama wata gagarumar kafa wacce ke kare muradun aikin lauya da mambobin ƙungiyar a Jigawa ma da wajen ta.” In ji shi. “Na...
Wata ’yar siyasa a jihar Bauchi mai suna Aishatu Haruna, ta ce ta shafe shekaru shida tana dakon soyayyar attajirin nan na Afirka, Alhaji Aliko Dangote a ranta, inda ta ce za ta iya shiga mummunan hali idan bai aure ta ba. Ta ce sau uku tana yin mafarkin ta aure shi, kuma ba ta jin za ta iya auren wani ba shi ba a duniya. A cikin wata tattaunawarta da gidan rediyon Albarka da ke jihar Bauchi, Aishatu, wacce aka fi sani da Gimbiyar Mawakan Bauchi, ta kuma ce sau uku tana zuwa kamfanin attajijin na Obajana, ko za ta hadu da shi a can. Ranar Hausa ta duniya: Za a yi gagarumin biki a fadar Sarkin Daura Lafiyar...
Ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙudiri niyyar kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da kuma inganta rayuwar ’yan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida ta NUJ ta shirya domin fara taron makon manema labarai na shekara ta 2025, da kuma bikin cika shekara 45 daka guda a Ilorin jihar Kwara Ya shawarce su da su bi ka’ida wajen gudanar da ayyukansu na yada labarai. Imam Lukman ya bukaci masu aikin yada labarai da su kasance masu adalci da kyautatawa a tsakaninsu . A nasa jawabin, Fasto...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Masana Iran da suka yi shahada a lokacin yaki babu laifin da suka aikata ban da hidima ga al’ummarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka kan shirun da masu da’awar kare hakkin bil’adama da zaman lafiya da tsaro suka yi dangane da laifukan gwamnatin ‘yan sahayoniyya, yana mai cewa: Masana kimiyyar Iran da suka yi shahada ba su aikata komai ba face hidimar al’ummar Iran a fadin duniya, amma gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe su. Masoud Pezeshkian ya halarci bikin karrama masana kimiyya da suka yi shahada a tsangayar koyar da fasahar nukiliya ta jami’ar Shahid Beheshti a safiyar ranar Talata, inda ya jinjinawa hotunan malaman kimiyya da suka yi shahada...
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai. Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin taronsu. Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya yaba wa kungiyar ta NUJ bisa zabar Kano a taron ta na kasa, yana mai jaddada cewa wannan shaida ce ta kyakkyawar alakar aiki tsakanin gwamnatin jihar Kano da kafafen yada labarai. Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen inganta rayuwar jama’a, da kuma tabbatar da cewa dole ne a cika...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: A Lokaci Ya Yi Da Za A Daina Kakaka Takunkumi Da Ba Dace Ba Kan Kasashe
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Lokaci ya yi da za a amince da takunkumin da bai dace ba a matsayin laifi ga bil’adama Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce lokaci ya yi da za a amince da takunkumin bai daya da Amurka da kawayenta suka kakaba wa Iran a matsayin wani laifi na cin zarafin bil adama. A cikin shafinsa na dandalin X, Araqchi ya bayyana cewa: “Gwamnatocin yammacin duniya a koyaushe suna da’awar cewa takunkumin zaman lafiya ne maimakon yakin zubar da jinni, amma gaskiyar tana bayyana wani labari na daban.” Ya yi nuni da wani bincike na baya-bayan nan da aka buga a cikin jaridar The Lancet, wanda ya nuna cewa takunkumin bai-daya-musamman wanda...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU), Jami’ar Jihar Taraba Jalingo, ta bayar da wa’adin makonni biyu ga gwamna Agbu Kefas da shugabannin jami’ar da su gana da ita ko kuma ta shiga yajin aikin. A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron majalisar da aka gudanar a ranar 7 ga wata. Agusta 2025, kuma shugaban kwamitin, Comr. Bitrus Joseph Ajibauka, da sakatare, Mamki Joshua Atein, kungiyar ta bayyana rashin jin dadin ta kan yadda gwamna Kefas ya kasa mutunta yarjejeniyar da kungiyar ta cimma da Gwmanati a wata ganawa da shugabannin kungiyar tare da samar da samfuri da tsarin biyan basussukan da ake bin su a makon farko na watan Fabrairu, 2025, sun bayyana matakin da gwamnan ya...
Jam’iyyar ta naɗa Abdulrazaq Abubakar Isah Iko a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, da Adamu Aliyu a matsayin sakataren riƙon ƙwarya har sai an gudanar da sabon zaɓe. ADC ta gargaɗi shugabannin da aka dakatar kada su ci gaba da kiran kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar ko gudanar da harkokinta. Haka kuma ta soke tarukan siyasa da suka shirya, tana mai cewa hakan ya saɓa wa dokar zaɓe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Biyo bayan wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fitar na cewa sama da likitoci 16,000 ne suka bar Najeriya a cikin shekaru bakwai da suka gabata domin neman aiki a wasu kasashe, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri na cike gurbin da likitocin suka haifar. Da yake zantawa da manema labarai a Katsina, Shugaban Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, ya ce hukumar ta kaddamar da wani shiri na musamman domin horar da karin likitoci, ma’aikatan jinya, masu harhada magunguna da kwararrun dakin gwaje-gwaje a manyan makarantun kasar nan. Ya ce tuni hukumar ta TETFUND ta zuba sama da Naira biliyan 100 a manyan makarantu goma sha takwas domin...

Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Iran za ta kasance tare da al’ummar Lebanon a koyaushe Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya tabbatar da cewa: Alakar al’adu tsakanin Iran da Lebanon ta taimaka wajen karfafa alaka tsakanin al’ummomin kasashen biyu. A cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Beirut a yau Laraba, Larijani ya yi nuni da cewa, Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da al’ummar Lebanon. Larijani ya kara da cewa: Iran da Labanon suna da dadaddiyar wayewa, kuma a ko da yaushe akwai alaka ta kut-da-kut a tsakanin al’ummomin kasashen biyu. Ya kara da cewa, wannan alaka ta al’adu ta haifar da alaka ta musamman tsakanin al’ummomin...
Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha. Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar harin inda ya jaddada cewa maharan sun kuma kashe shugaban kungiyar masu sayar da babura na yankin a yayin farmakin. Achida ya ci gaba da cewa, kwana biyu kacal kafin harin masallacin, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka biyu da ke makwabtaka da su, Gidan Taru da Kwargaba, inda...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kundin tsarin mulki na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da asusun samar da ayukka na kasa da kasa (USPF), dukkanin su a karkashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani. A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce an nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC, yayin da Dr. Aminu Waida ya ci gaba da zama mataimakin shugaban zartarwa/Babban jami’in gudanarwa, mukamin da aka nada shi a watan Oktoban 2023 kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Nuwamba na wannan shekarar. A baya Olorunnimbe ya yi aiki a hukumar kula da ayyukan yi na jihar...
Gwamnatin Iraki ta bayyana cewa: Yarjejeniyar da Iran ta kulla da Iraki zata yi gagarumar amfani a fagen tsaron yankin Ofishin jakadancin Iraki a Amurka ya tabbatar da cewa: Iraki kasa ce mai cin gashin kanta kuma tana da hakkin kulla yarjejeniyoyin da kuma yarjejeniyar fahimtar juna. An yi nuni da cewa, yarjejeniyar tsaro da aka rattabawa hannu a baya-bayan nan tsakanin Iran da Iraki ta zo ne a cikin tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu don tabbatar da tsaro da kuma kula da kan iyakokin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa: Ofishin jakadancin ya bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Iraki INA ya watsa cewa: “A matsayin martani ga kalaman da kakakin...
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara karkashin jagorancin Bashar Aliyu Gummi, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta hada kai da ayyukan tsaro a Jihar domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, kamar yadda babi na biyu na kundin tsarin mulki ya tanada. A zaman taron na ranar Talata, mambobin sun yi zargin cewa, ‘yan bindiga sun mamaye al’ummomi da dama a fadin jihar Zamfara, kuma sun zargi Gwamnan da mayar da hankali kan burin siyasa da kuma zargin abokan hamayya. Sun kuma yi zargin cewa, Gwamnan bai kai ziyara ko aika tallafi ga al’ummomin da hare-hare ya shafa ba, inda suka ce ziyarar da ya shirya kai wa al’ummar Banga da ke karamar hukumar Kaura Namoda ta kasance da...
Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja, ya yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kama Abubakar Abba, jagoran kungiyar Mahmuda, daya daga cikin manyan kungiyoyin ta’addanci da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi a Najeriya. An ce an kama shi ne a Wawa da ke karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja inda aka kai shi Abuja domin ci gaba da bincike. Gwamna Umar Bago ya bayyana matakin a matsayin nuni da irin jajircewar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi na tabbatar da tsaro da walwalar ‘yan Nijeriya. Gwamnan wanda ya yi magana ta bakin babban sakataren yada labaran sa, Bologi Ibrahim, ya ce, “Eh gaskiya ne, zan iya tabbatar da cewa hukumar...
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare 4 na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Haifa, Negev, Umm al-Rashrash, da kuma Bi’ersheba na Falasdinu da aka mamaye. Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: “Ayyukan sun cimma nasarar cimma manufofinsu,” yana mai jaddada ci gaba da ayyukan bayar da tallafi har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza. Sari’e ya ce: Ci gaba...
Gwamnatin jihar Katsina ta ce shirye-shirye sun kankama domin bin sahun sauran sassan duniya a yayin bikin Ranar Hausa ta Duniya a za ake gudanarwa ranar 26 ga watan Agustan kowacce shekara. Shugaban Hukumar Kula d Tarihi da Al’adu ta jihar, Dr Kabir Ali-Masanawa ne ya bayyana hakan yayin wani jawabi ga manema labarai a Katsina ranar Talata. Ya ce za a yi taron ne a Fadar Sarkin Daura da ke jihar, kuma ana sa ran manyan baki daga kasashe akalla 24 za su halarta. Masanawa ya ce wannan shi ne karo na farko da gwamnati ta shiga cikin shirya bikin, inda ya ce hatta Gwamnan jihar, Dikko Umaru Radda ya tsaya tsayin daka wajen ganin bikin ya yi nasara....
An ce ya amsa cewa an aikata fashi da makami sau biyu da shi, kuma yanzu hakan ana shari’arsu a kotun jihar Gombe. An miƙa shi tare da kayan da aka gano ga Sashen Yaƙi da Tashin Hankali domin ƙara gudanar da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.” Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba. Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya tabbatar da cewa, Isra’ila da Amurka ne suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da suka fuskanci martani mai tsanani a lokacin da suka kaddamr da hare-hare kan kasar Iran. A yayin da yake karbar bakuncin babban kwamandan rundunar tsaron kasar a Afirka ta Kudu, Janar Hatami ya ce, hukumomin Isra’ila da Amurka sun yi amfani da dukkan karfinsu wajen kai wa Iran hari, amma sun kasa cimma burinsu. Har ila yau, ya bayyana matakin da Afirka ta Kudu ta dauka na shigar da kara kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila a kotun kasa da kasa a matsayin wata babbar Jarunta, yana mai jaddada cewa tarihi zai tabbatar da wannan...
Ministan Ruwa na Habasha Habtamu Etfa ya jaddada cewa, babbar madatsar ruwa ta kasarsa amfanin dukkanin kasashen yankin ne. Etfa ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kamar yadda shafin yanar gizo na Ethiopian Monitor ya bayyana cewa, ” kwararar kogin Blue Nile ya karu a lokacin noman rani, yayin da muka ga raguwar ambaliya da kuma jinkiri fiye da wata guda.” Ya jaddada cewa abin da muke hasashe kuma muke bayyanawa yau da kullun ya tabata a aikace.” Ya kara da cewa, “Grantin Renaissance Dam na Habasha ba kawai ya kara yawan filayen noma da ake nomawa a kasashen da ke gabar kogin Blue Nile ba, har ma ya taimaka wajen kare...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP). Haka...
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi. A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba. DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi Sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya...
Nijeriya da Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta karfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni daban-daban, kamar batun yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma bayar da horo na musamman ga jami’an tsaron Nigeria. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar a Abuja. Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa da muhimmanci tsakanin bangarorin biyu. A yayin taron, wakilan bangarorin biyusun tattauna batutuwan da suka shafi tsaro a duniya, musamman yaƙi...
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi. “CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil. Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin. An garzaya da Chukwuebuka...
A halin da ake ciki, EFCC ta yi Allah wadai da jam’iyyar ADC bisa zargin sanya siyasa a binciken da ta gudanar kan Tambuwal. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A matsayinta na mai jagorantar zamanantar da duniya, Sin tana gabatar da ilimin da ya danganci fasahar zamani ga kasashen Afrika domin su tsaya da kafarsu tare da samun kyakkyawar makoma. Wannan zai samarwa matasa dama mara iyaka ta fadada ilimi da fahimta da samun aikin yi da zai kai su ga yin kirkire kirkiren da za su tallafawa al’ummar da cike gibin dake akwai tsakanin masu ilimi da marasa shi. Kuma yayin da duniya ta dunkule wuri guda saboda fasahohin zamani, matasa a nahiyar Afrika za su kara fahimtar yanayin da duniya take cike da fahimtar juna da kara wa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen waje, lamarin da zai share fagen gogayyar ilimi da samar da...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekaru 18, Hassan Aminu Sadiq, bisa zargin aikata fashi da makami a lokuta daban-daban, bayan wani samame da aka kai unguwar unguwar Yelwa da ke garin Kwadon a Karamar Hukumar Yemaltu Deba. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana, yana ɗauke da kunshin ganyen da ake zargin tabar wiwi ne. An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe EFCC ta saki Tambuwal Binciken da aka soma gudanarwa ya nuna cewa Hassan yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa-a-jallo, bisa zarginsa da hannu a...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake, Mohammed Tukur mai shekaru 55, a kauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. EFCC ta saki Tambuwal Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a ya aikata ta’asar. Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami’an...
Harin ya matukar tayar da hankalin al’ummar yankin, inda mazauna wurin suka tsere domin tsira da rayukansu. Rundunar ‘yansandan jihar Sokoto ba ta fitar da adadin waɗanda suka mutu ko suka ji rauni ko kuma aka sace su ba a yayin kai harin. Shugaban jam’iyyar APC a jihar Sokoto, Honarabul Isah Sadeeq Achida, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, inda ya bayyana shi a matsayin harin dabbanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani bayanin hadin giwa wanda ministocin harkokin wajen kasashe 27 suka rattabawa hannu, ya bukaci firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bude hanya don shigoda abinci cikin gaza, don kawo karshen yunwa da ta bayyana a fili. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa daga cikin kasashen da suka sanyawa bukatar hannu har da kasashen Faransa da Burtaniya da kuma tarayyar Turai a yau Talata. Bayanin ya kara da cewa lalle musibar yunwa da ta sami Gaza, ta kai matsayinda mutum ba zai sawwara shi ba, suna bukatar Natanyahu ya bada izinin a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba tare da bata lokaci ba. A wani labarin kuma yawan mutanen da abincin da ake jefawa...
Wani babba`ani babba`sojojin kasar Iran ya gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa duk wasu hare-hare kan kasar zai kara fushin sojojin kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI Major General Abdolrahim Mousavi yana fadar haka a lokacin ganawarsa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Afrika ta kudu General Rudzani Maphwanya a yau talata a nan Tehran. Janar Mousavi ya kara da cewa dakarun kare juyin juta halin musulunci a nan Iaran wato IRGC sune sojojin da suka fi kawo fada da yan ta’adda a duniya, sannan rundunar a shirye take ta yi aiki da sojojin Afrika Ta Kudu don samun irin kwarewan da rundunar take da shi a wannan bangaren...
Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani ya bayyana cewa gwamnatocin kasashen Lebanon da Iran basa daukan umurni daga Iran. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Dr Larijani yana fadar haka bayan kammala ziyaran aiki a kasar Iraki. Ya kuma kara da cewa kasashen Iraki da Lebanon suna da asasshen kwarewa a tafiyar da kasashensu. Don haka basa bukatar daukar umurni daga kasarsa. Sai dai wannan ba zai hana kasashen su shawarci JMI a kan wasu al-amura da suka shafesu ba. A ziyarsa a kasar Iraki dai babban sakataren ya gana da shugaban kasa, firai minister da shugaban majalisar dokoki da kuma tokwaransa na kasar Iraki. Daga birnin Bagdaza dai ana saran Dr...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ma’aikatarsa ce take kula da dukkan al-amuran da suka shafi shirin makamashin Nukliya na kasar, tun bayan da majalisar dokokin kasar ta bukaci a jingine aiki da hukumar makamashin Nuikliya ta Duniya IAEA bayan yakin kwanaki 12 da HKI da Amurka suka kaiwa kasar. Aragchi ya bayyana cewa mai yuwa nan gaba, majalisar koli na tsaron kasar ta kula da lamarin shirin makamashin nukliya ta kasar. Amma a halin yanzu tana hannun ma’aikatar harkokin wajen kasar ne. A jiya talata ce mataimakin babban sakataren hukumar makamashin nukliya ta duniya ya ziyarci Tehran, ya kuma tattauna dangane da yadda mu’amalar kasar zata kasance da hukumar. Labarin ya bayyana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau Talata, ta wayar tarho a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi. A cikin wannan makon ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranci yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen Azarbaijan dangane da yankin karabakh a fadar White House. Sannan akwai labarin cewa za’a gina wani babban titi wanda zai ratsa kasashen bitu. Kasashen dai suna makobtaka da kasar Iran, don haka dangantakarsu...
Ejodame ya rahoto CAS, yana cewa “Tare da ingantattun jirage da ke da ingantattun tsare-tsaren kai hare-hare na dare, jirgin NAF ya kai hare-hare guda 798”. A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yabawa NAF bisa ci gaba da bayar da tallafi ta sama wajen gurgunta karfin ‘yan ta’adda da kuma kare al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9 ga watan Afrilun bana, inda ta saka wasu sassa 28 na Amurka cikin wadanda ta sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, wato hana sayar musu kayayyakin amfanin jama’a da ake iya amfani da su a bangaren soja. Har wa yau, domin tabbatar da matsayar da aka cimma a wajen shawarwarin manyan jami’an Sin da Amurka a bangaren tattalin arziki da cinikayya, an yanke shawarar cewa,...
Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma taimaka wajen renon wasu ‘ya’yan Ronaldo guda uku – Cristiano Jr., wanda aka haifa a watan Yuni 2010, da tagwaye Eva da Mateo wadanda aka haifa ta hanyar dashen kwayoyin halittta a watan Yunin 2017. Ronaldo, mai shekaru 40, ya na cikin kakar wasa ta hudu tun bayan komawarsa kungiyar Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, tsohon dan wasan Real Madrid, Manchester United da Juventus...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin ta kammala shari’ar da ta shafe shekaru goma tana yi wa tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram. Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, bayan amincewa da buƙatar gwamnati ta ɗage zaman domin kawo ƙarin shaidu da kuma ba wa Dasuki damar fara kare kansa. Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Ya kuma umurci gwamnati ta kira sauran shaidunta domin...

Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
Biyo bayan sanarwar hadin gwiwa bayan taro kan tattalin arziki da cinikayya da aka yi tsakanin Sin da Amurka a birnin Geneva a ranar 12 ga watan Mayun 2025 wato sanarwar Geneva, da tarukan da aka yi a birnin London a ranekun 9 da 10 ga watan Yunin 2025, da wanda aka yi a Stockholm a ranekun 28 da 29 ga watan Yulin 2025, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin da gwamnatin Amurka, sun waiwayi alkawuran da suka dauka karkashin sanarwar hadin gwiwa ta Geneva, kuma sun amince cewa daga ranar 12 ga watan nan na Agusta, za su fara aiwatar da matakai kamar haka: Amurka za ta ci gaba da gyara matakan karin haraji kan kayayyakin kasar Sin, ciki har...
Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
Nijeriya da ƙasar Isra’ila sun sake jaddada aniyarsu ta ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a fannoni masu muhimmanci kamar yaƙi da ta’addanci, musayar bayanan sirri, samar da kuɗin tsaro da kuma horaswa ta musamman. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar haɗin gwiwa wadda Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, da Mataimakiyar Ministan Harkokin Waje ta Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz suka fitar bayan wani taro na musamman da suka gudanar ranar Litinin a Abuja. Tinubu na amfani da EFCC ya muzguna wa ’yan adawa — Atiku Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna Sanarwar, wadda mai magana da yawun Ofishin Ƙaramar Ministar Harkokin Wajen, Dokta Magnus Eze ya fitar, ta ce taron ya nuna alaƙa mai ɗorewa...
Babban sakataren Majalisar Kolin Tsaron kasar Iran Ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah ba ta bukatar juya akalarta Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani ya bayyana cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah tana da cikakken ilimin siyasar da zata gudanar da al’amuranta bisa dacewa, kuma gwagwarmaya ba ta bukatar horo. Larijani ya kara da cewa a wani taron manema labarai a birnin Bagadaza na kasar Iraki; “Dukkansu sun damu da tsaron yankin baki daya, kuma al’ummar Iraki ba sa bukatar wani takunkumi.” Larijani ya jaddada cewa: Rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da kasar Iraki na da nufin hana duk wata barazana ga tsaron kasashen biyu. A yayin da yake mayar da martani ga wasu nazari...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar da za ta tsawaita dakatar da harajin da ya ƙaƙaba wa ƙasar China na tsawon kwanaki 90. Trump ya sanar da hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, sa’o’i kaɗan kafin wa’adin farko da ya tsara ya ƙare. Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi Mastering diverse trading strategies for market success A ɗaya hannun, ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar China ta kuma tabbatar da cewa ita ma ta dakatar da ƙarin haraji kan kayayyakin Amurka daga yanzu zuwa tsawon kwanaki 90, a matsayin martani. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa tun a watan Mayun...