Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Afrika
Published: 11th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika.
Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna jiya Talata a Changsha, babban birnin lardin Hunan, da ministocin da suka hada da Musalia Mudavadi na Kenya da Yassine Fall ta Senegal da Mahmoud Thabit Kombo na Tanzania da Selma Ashipala-Musavyi ta Namibia da Phenyo Butale na Botswana da kuma Tete Antonio na Angola.
Da yake ganawa da Musalia Mudavadi na Kenya, Wang Yi ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Kenya wajen aiwatar da matsayar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, da karfafa goyon bayan juna da aminci a tsakaninsu, da karfafa tubalin dangantakar Sin da Kenya da ci gaba da kara wa dangantakarsu kuzari.
Yayin ganawa da Yassine Fall ta Senegal kuwa, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da gabatar da sabbin damarmakin ci gaba ga kasashen Afrika, ciki har da Senegal, domin taimakawa kasashen zamanantar da kansu. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
Yayin ganawarsa da firaministan Thailand, Shugaba Xi Jinping ya ce a shirye kasarsa take ta karfafa hadin gwiwa da Thailand kan dabarun samun ci gaba, tare kuma da gabatar da gogewarta na samun ci gaba a sabon zamani, kuma ya yi kira da a gaggauta gina layin dogo tsakanin Sin da Thailand da bunkasa hadin gwiwa a bangaren cinikin amfanin gona da tattalin arziki mai kiyaye muhalli da kuma kirkire kirkiren fasaha. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA