Rasha Tana Kokarin Kara Samun Gindin Zama A Cikin Nahiyar Afirka
Published: 10th, June 2025 GMT
Fadar mulkin Rasha ” Kremlin” ta sanar da cewa; Kasar Rasha tana fadada fafagen yin aiki da kasashen Afirka da su ka hada da fagage masu muhimmanci na soja da tsaro.
Kakakin fadar ta “Kremlin” Dmitry Viskov da yake amsa tambaya akan tasirin shigar Rasha cikin nahiyar Afirka, ya ce; Sannu a hankali Rasha tana kara shiga cikin nahiyar ta Afirka’ sannan kuma ya yi ishara da azamar da Rashan ta yi na ganin wannan alakar ta bunkasa tare da mayar da hankali akan tattalin arziki da kuma zuba hannun jari.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Yi Kira Da A Kara Azamar Gina Kasa A Gabar Da Ake Bikin Cika Shekaru 120 Da Haihuwar Dan Mazan Jiya Chen Yun
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a yi koyi daga akidun dan mazan jiya, kuma jagora na gari Chen Yun, tare da kara azamar dorar da kyawawan dabi’unsa cikin himma da kwazo, don gina kasar Sin mai matukar karfi.
Shugaba Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar, ya yi kiran ne a yau Juma’a, cikin jawabin da ya gabatar, yayin taron bikin murnar cika shekaru 120 da haihuwar Chen Yun, taron da ya gudana a babban dakin taruwar jama’a dake tsakiyar birnin Beijing
Shugaban na Sin ya ce, an haifi Chen a shekarar 1905, ya kuma shiga JKS a shekarar 1925. Ya kuma kasance shahararren dan gwagwarmaya a rundunar ‘yantar da al’umma kuma dattijon arziki, kana daya daga cikin kusoshin da suka kafa tsarin tattalin arziki na gurguzu na kasar Sin. Kazalika, ya kasance muhimmin memba cikin jerin shugabannin JKS zangon farko mai Mao Zedong a matsayin babban jigo, kana da shugabannin JKS zango na biyu mai Deng Xiaoping a matsayin babban jigo. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp