Rashin wutar lantarki ya durƙusar da kasuwanci a Arewa Maso Gabas
Published: 12th, June 2025 GMT
Rashin wutar lantarki a Arewa maso Gabashin Najeriya ya tilasta wa jama’a da ’yan kasuwa zaman ɗari-ɗari da asarar dukiya, sakamakon aikin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ke yi na aikin sabbin turakun wutar lantarki.
Rashin wutar, wanda ya fara daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni, ya shafi layin wutar lantarki na Jos–Bauchi–Gombe mai ƙarfin 132kV.
A Jihar Adamawa, musamman a birnin Yola, jama’a na cikin matsanancin hali.
Hajiya Aisha Babangida daga Jimeta, ta ce rashin wutar ya tilasta masa soye dukkanin naman ragon sallarta domin babu wutar da za ta ajiye shi a firinji.
“Na fi son dafawa, amma dole na soya gaba ɗaya. Wannan matsala ta wuta ta zo ne a lokacin da ake buƙatar wutar,” in ji ta.
Kasuwanci da harkokin yau da kullum sun tsaya cak a wurare da dama.
Adamu Abubakar, mai sayar da lemun kwalba a kasuwar Jimeta, ya koka da cewa rashin sanyin ruwa ya rage masa yawan kwastomomi.
“Mutane na so ruwan sanyi, amma ba zan iya samun mai sanyi ba. Ina amfani da ƙanƙara ne yanzu don na ci gaba da kasuwancina,” in ji shi.
Muhammad Zaharaddeen, wani barber mai shagon aski a Bauchi, ya ce kasuwancinsa ya durƙushe sakamakon rashin wutar lantarki.
“Shagona na buƙatar wutar lantarki sosai. Ko da na kunna janareta, farashin mai ya tashi fiye da yadda mutane ke biya a baya,” in ji shi.
“Da ba don wani ɗan kasuwanci da nake yi a gefe ba, da ko abinci ba zan iya siya ba.”
A Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, asibitoci da ƙananan ‘yan kasuwa na kokawa kan hauhawar kuɗin aiki.
Asibitin Federal Medical Centre ya koma amfani da janareta, wanda hakan ke sa wa ana biyan maƙudan kuɗaɗe wajen zuba man fetur.
“An daɗe da yanke wutarmu, yanzu da aka dawo mana da ita, sai kuma ga wannan matsalar. Duk manyan na’urorinmu suna amfani ne da dizal,” in ji Dokta Aisha Adamu Sani, daraktar asibitin.
Masu niƙa, masu walda da masu ɗinki a Jalingo sun dakatar da aiki.
Mallam Haruna Garba, wanda ke da injin niƙa, ya ce ya rufe shagonsa gaba ɗaya.
“Ba zan iya niƙa babu wutar lantarki ba. Man fetur ya yi tsada sosai. Na rufe kasuwancina na ɗan lokaci,” in ji shi.
A Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, al’umma na fama da ƙarancin ruwa da hauhawar farashin ruwan sanyi da kayan masarufi.
Musa Adamu, mai sayar da lemu, ya ce: “Babu wuta, babu sanyi. Dole na ɗan kara farashi, amma ya kamata jama’a su fahimtci rayuwar da ake ciki,” in ji shi.
Masu ƙananan sana’o’i irin su Yusuf Bukar, wani masassaƙa a Damaturu, na kashe dubban Naira kullum wajen siyan mai domin kammala ayyukansu.
“Idan wannan hali ya ci gaba, zan rasa kwastomomina. Na kashe Naira 10,000 a jiya kacal a kan mai,” in ji shi cikin baƙin ciki.
TCN ta bayyana cewa katse wutar na da matuƙar muhimmanci domin kammala gina sabbin turakun wuta masu ƙarfin 330kV domin inganta tsarin samar da wutar a yankin.
Kakakin TCN, Ndidi Mbah, ta ce turakun za su zama mafita daga yawan katsewar wuta a gaba.
“Da zarar an kammala aikin, za a iya amfani da layin Bauchi da Gombe. Jos ma za ta iya riƙa kai wa Bauchi wuta kai-tsaye,” in ji ta.
Sai dai masana sun ɗora alhakin matsalar kan rashin wata hanya da za ake samar wa Arewa maso Gabas wuta.
Wani tsohon ma’aikacin TCN da ya nemi a sakaya sunansa ya ce: “Idan layin Jos-Bauchi-Gombe ya faɗi, kowa zai tsunduma cikin duhu. Ya kamata a ce an gina wata hanya ta biyu tun da daɗewa.”
Wannan ba shi ne karon farko da yankin ke faɗawa cikin duhu ba.
A baya, wasu da ba a san ko su waye ba sun lalata turakun wuta da bam, wanda ya sa aka ɗauke wuta gaba ɗaya a Arewa maso Gabas.
Sai dai wannan katsewar wutar wata hujja ce ta gaggawar sake fasalin tsarin wutar lantarki a yankin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Adamawa Lantarki Rashin Wuta Taraba Turaku wutar lantarki rashin wutar
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da cewa daga lokacin da aka tsayar da wuta zuwa yanzu adadin Falasdinawan da HKI ta kashe sun kai 200, yayin da wasu kusan 600 sun jikkata.
Sanarwar ta ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta kuma ci gaba da cewa; A cikin sa’o’i 48 da su ka gabata,an sami shahidai 22, biyar daga cikinsu basu dade da yin shahada ba, sai kuma 17 da aka tono su daga karkashin baraguzai. Haka nan kuma na kai wasu 9 zuwa asibitocin da suke a yankin.
Wani sashe na sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza ya ce, har yanzu da akwai shahdai masu yawa da suke a karkashin baraguzai, wasu kuma a kan hanyoyi, saboda rashin kayan aiki da kungiyoyin agaji za su yi amfani da su.
Tun daga ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin shahidai ya kai 68,858, sai kuma wani adadin da ya kai 170,664 da su ka jikkata.
Amma daga tsayar da wuta a ranar 11 ga watan Oktoba zuwa yanzu, an sami shahidai da sun kai 226, sai kuma wasu 594 da su ka jikkata. Haka nan kuma an iya tsamo gawawwakin shahidai daga cikin baraguzai har su 499.
Haka nan kuma ma’aikatar kiwon lafiyar tra sanar da karbar gawawwaki 30 da HKI ta mika wa bangaren Falasdinawa ta hannun hukumar agaji ta “Red-Corss.
Tun bayan tsagaita wutar yaki, har ya zuwa yanzu dai HKI tana ci gaba da kai hare-hare a sassa daban-daban na Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Kasar Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Amurka Na Shirin Kai Hari Kan Kasar Venzuwela A Kowanne Lokaci November 1, 2025 Iran Ta Sanya Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3 October 31, 2025 Isra’ila Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza October 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci