Zamfara: APC Za Ta Maka PDP A Kotu Kan Zargin Matawalle Da Hannu A Satar Mutane
Published: 12th, June 2025 GMT
Haka kuma, ya zargi Matawalle da karɓar Naira miliyan 300 daga tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, don a sako ɗaliban, amma ya bai wa ‘yan bindiga miliyan 30 kacal.
APC ta ƙaryata wannan zargi.
Ta kuma bayyana cewa zargin Kaura yana shafar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar kamar tsohon Gwamna Abdulaziz Yari, wanda yanzu ke wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa.
Jam’iyyar APC ta ƙalubalanci Kaura da ya kawo hujjoji kan wannan zargi da kuma wasu mutane da aka sace a jihar, kamar satar ɗalibai mata 270 daga makarantar Government Girls Secondary School da ke Jangebe a ranar 26 ga watan Fabrairun 2021, da kuma satar ɗaliban Kwalejin Noma da Kiwo da ke Bakura.
APC ta jaddada cewa gwamnatin Matawalle ta yi ƙoƙari wajen yaƙi da ‘yan bindiga da ceto al’ummomi da dama.
Ta bayyana yankuna kamar Gwaram, Kanoma, Kaya, Faru, Janbako, Lilo da Anka, a matsayin wuraren da aka gudanar da ayyukan tsaro da taimako.
Jam’iyyar ta kuma ce tana duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan gidan talabijin na Maibiredi TV da ya watsa hirar da ake ganin an shirya don ɓata sunan ministan.
Ta zargi PDP da ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga gazawarta ta hanyar yaɗa ƙarya da tayar da fitina don samun moriyar siyasa.
A ƙarshe, APC ta yi kira ga mambobinta da su zauna lafiya da bin doka, inda ta bayar da tabbacin cewa gaskiya za ta fito fili, kuma za a yi adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Matawalle Zamfara Zargi
এছাড়াও পড়ুন:
ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark
Shugaban riƙon ƙwarya na jam’iyyar ADC, David Mark, ya ce Arewacin Najeriya na cikin mawuyacin hali, kuma jam’iyyarsu ce kaɗai za ta iya warware waɗannan matsaloli idan aka zaɓe ta.
Ya bayyana hakan ne a taron jam’iyyar ADC da aka yi a Abuja Continental Hotel, inda mambobi da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban suka halarta.
Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCNDavid Mark, wanda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ne, ya gabatar da jawabi mai taken: “Haɗin kai da zaman lafiya su ne mafita ga matsalolin Arewa”.
Ya ce Arewa na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar su rashin tsaro, talauci, rikicin ƙabilanci da addini, rikicin siyasa da kuma durƙushewar tattalin arziƙi da zamantakewa.
Ya ce, “Waɗannan matsaloli ba yau aka fara su ba, kuma ba za su gushe ba sai mun tashi tsaye tare da ɗaukar matakai na gaskiya da haɗin kai.
“Dole ne mu karɓi gaskiya cewa mu ne muke da hannu a cikin matsalolinmu. Ka da mu ci gaba da ɗora laifi kan wasu idan muna so mu samu mafita ta gaskiya.”
Ya ƙara da cewa yin shiru kan matsalolin na ƙara dagula lamarin.
Ya buƙaci al’ummar Arewa su koma kan ɗabi’unsu na adalci, daidaito, mutunta juna da yin aiki tare, waɗanda suka sa Arewa ta zama abar koyi wajen zaman lafiya da ci gaba.
“Lokacin koke-koke ya wuce,” in ji shi.
“Arewa na zubar da jini, kuma mu kaɗai ne za mu iya warkar da ita. Mu guji kalaman ƙiyayya da siyasar raba kawuna. Mu mayar da hankali kan abubuwan da za su haɗa mu waje ɗaya; ilimi da lafiya.
“Mu kuma riƙa ɗaukar alhakin abubuwan da muka yi ko muka kasa yi, sannan mu haɗa hannu domin dawo da zumunci da haɗin kanmu.”
Ya ce idan aka yi haka, za a iya sake gina Arewa ta zama cibiyar zaman lafiya, fahimta da ci gaban tattalin arziƙi da fasaha.
David Mark, ya nuna damuwa kan yadda ’yan bindiga, ’yan ta’adda da rikicin ƙabilanci suka mayar da wasu ƙauyuka a Arewa tamkar wuraren yaƙi.
A cewarsa miliyoyin mutane sun rasa matsuguni, kuma tattalin arziƙin yankin ya durƙushe.
Ya ƙara da cewa duk da albarkatu masu tarin yawa da Arewa ke da su, ita ce mafi talauci a Najeriya, inda jahilci, rashin aikin yi da rashin ababen more rayuwa suka yi yawa.