Bayanai sun nuna cewa, harin na faruwa, aka sanar da jami’an tsaro.

Sun isa cikin gaggawa da motocinsu da jirgin sama mai saukar ungulu.

Amma maharin ya ƙi miƙa wuya, hakan ya sa aka bindige shi.

Daga cikin waɗanda suka mutu, mata shida ne, maza uku, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga.

Hukumomi sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike don samo ƙarin bayani game da wannan mummunan al’amari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ɗalibai Ɗalibi Harbi

এছাড়াও পড়ুন:

NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025

Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO), ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare (SSCE) na shekarar 2025.

Daga cikin ɗaliban da suka zana jarabawar guda 818,492, kashi 60.26 sun ci aƙalla darusa biyar da suka haɗa da Lissafi da Turanci.

Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Shugaban NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya ce ɗalibai 1,367,210 suka yi rajistar jarabawar; maza 685,514 da kuma mata 681,696.

Amma daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka zana jarabawar.

Ya ce ɗalibai 1,144,496, wanda ya kai adadin kashi 84.26, sun samu darusa biyar ba tare da cin Lissafi da Turanci ba.

Sai dai an dakatar da sakin sakamakon makarantu takwas a Ƙaramar Hukumar Lamorde ta Jihar Adamawa saboda rikicin ƙabilanci da ya auku tsakanin 7 zuwa 25 ga watan Yuli, 2025.

Rikicin ya yi sanadin wanda ya hana zana jarabawar darusa 13 da takardu 29.

Hukumar na tattaunawa da gwamnati don sake bai wa ɗaliban damar rubuta jarabawar.

NECO ta kuma bayyana cewa an samu makarantu 38 daga jihohi 13 ds laifin aikatar satar amsa yayin zana jarabawa.

Za a gayyace su zuwa babban ofishin NECO kafin ɗaukar mataki a kansu.

Haka kuma, hukumar ta dakatar da mutum tara da ke aikin sanya ido sake kula da jarabawa saboda gazawarsu wajen hana satar amsa.

Mutanen da aka dakatar, uku sun fito daga Jihar Ribas, uku daga Babban Birnin Tarayya, da kuma mutum ɗai-ɗai daga Jihohin Neja, Kano da Osun.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Sojoji Sun Kashe Mayaƙan ISWAP 11 A Borno Da Adamawa
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • Wata Ta Kashe ’Yar Uwarta Kan Bashin Naira 800 A Ondo
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Sarkin Shuwaka Na Kanam A Filato
  • Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Fasinjoji 17 A Zamfara