Ministan man fetur na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana cewa kasarsa zata ci gaba da saida danyen man fetur ga masu sayensa a kasashen waje duk tare da kokarin gwamnatin kasar Amurka na kara kuntatawa kasar a bangaren saida makamashin kasar ga kasashen waje.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya laraba bayan taron majalisar ministocin kasar a nan Tehran.

Ministan ta kara da cewa shirin Amurka na hana Iran saida danyen manta ga kasashen waje zai rugurguje kamar yadda ya rugurguje a baya. Y ace don mun rika mun gano kan zaren lalata duk wani shiri na hana mu saida danyin man ga masu sayan man kasar.

Ministan ya bayyana cewa labara ya zo masa kan cewa gwamnatin Amurka na kokarin kakabawa kasar takunkuman tattalin arziki kan sinadarin Methanol na kasar, shi ma suna aiki a kansa.

Gwamnatin Amurka ta Donal Trump tun watan Fabray run wannan shekarar ta fara wani sabin shiri na takurawa Iran, daga ciki har da maida sayar da danyen man fetur na kasar zuwa sifili.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Lebanon: Za A Yi Jana’izar  FItaccen Mawakin Gwagwarmaya Da Kishin Kasa Ziyad Rahbani A Yau Litinin

A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma.

Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya.

Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya.

A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya.

A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.

সম্পর্কিত নিবন্ধ