Gwamna Sule Ya Hori Masu Ziyarar Ibada Ta Kirista Su Zama Jakadu Na Gari
Published: 27th, February 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Nasarawa ya hori Kiristoci masu niyyar ziyarar su zama jakadu na gari tare dayin addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba idan sun isa can.
Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bankwana da masu ziyarar su 162 da zasu tashi zuwa Isra’ila.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin da’a a yayin tafiyar tasu, inda ya bayyana cewa su dauka su Allah ya nufa da wannan ziyarar a bana.
Ya kuma tabbatar wa maziyartan jihar cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwarsu, tare da samar da matsuguni da abinci kyauta a tsawon tafiyarsu.
Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin hukumar kula da masu ziyarar kiristoci ta jihar Nasarawa, Davide Ayiwa, wanda ya yabawa gwamnatin jihar kan gyaran ofishin hukumar ya kuma bukaci maziyartan da su ci gaba da gudanar da aikinsu.
Bikin ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar Dr. Emmanuel Akabe da alkalin alkalan jihar, Mai shari’a Aisha Bashir Aliyu, kwamishiniyar yada labarai da sauran kwamishinoni da sakataren gwamnatin jihar Labaran Shu’iabu Magaji babban akanta janar na jihar.
COV/Aliyu Muraki/Lafia
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya
Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar a matsayin shugabanta bayan rasuwar Sheikh AbdulRasheed Hadiyyatullah.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar a yau Laraba ta ce an amince da shuagabancin Dokta Bashir ne kai-tsaye saboda kasancewarsa mataimakin shugaba.
A ranar Litinin ne Sheikh Hadiyyatullah ya rasu yana da shekara 81 a Jihar Osun.
“Nan gaba za a sanar da mataimakin shugaban,” in ji sanarwar da Nafiu Baba Ahmed ya sanya wa hannu a matsayin sakataren majalisar.
Sheikh Bashir sanannen malami ne kuma shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Al-Furqan da ke Alu Avenue a Unguwar Nasarawa ta Jihar Kano.