Aminiya:
2025-06-12@08:31:03 GMT

Dalilin da Nijeriya ke fuskantar tsaiko wajen karɓar rancen $5bn daga Saudiyya

Published: 10th, June 2025 GMT

Nijeriya tana fuskantar tsaiko a tattaunawar da ake yi da kamfanin man fetur mafi girma a duniya mallakin Saudiya wato Aramco, dangane da shirin karɓar rancen Dala biliyan biyar.

Wani rahoton Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ne ya bayyana hakan da cewar Nijeriyar na neman rancen kuɗin ne wanda take shirin ƙulla yarjejeniyar biya da ɗanyen manta.

Gwamnan Kebbi ya bai wa ’yan kasuwar katako tallafin ibtila’in gobara A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote

Wasu majiyoyi huɗu sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa faɗuwar baya bayan nan da farashin ɗanyen mai ya yi a kasuwannin duniya shi ne ya janyo tsaikon, bayan da bankunan da ake sa ran za su taimaka wajen aiwatar da yarjejeniyar suka bayyana damuwa kan sauyin farashin da aka samu.

Wasu alƙaluma dai sun nuna faɗuwar farashin ɗanyen mai nau’in Brent da kashi 20 cikin 100, inda ya koma Dala 65 daga Dala 82 a cikin watan Janairun da ya gabata, abin da ke nufin idan har ba za a fasa ƙulla yarjejeniyar karɓar rancen na Dala biliyan 5 ɗin ba, to fa dole Nijeriya ta ƙara yawan gungunan ɗanyen man da za ta yi amfani da su wajen biyan bashin.

Biyu daga cikin majiyoyin da suka zanta Reuters, sun ce an fara tattaunawa kan shirin karɓar rancen ne a watan Nuwamban da ya gabata, lokacin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da Yarima mai jiran gadon Sarautar Saudiya Muhd Bin salman a yayin taron tattalin arziƙin da aka yi tsakanin Saudiyan da ƙasashen Afrika. Sai dai tun babu wani ƙarin bayani da aka taɓa bayyanawa kan neman bashin da Najeriyar ke yi, in banda yanzu da kamfanin dillancin labarai na Reuters da ya ruwaito.

Idan za a iya tunawa cikin watan Mayu, Shugaba Tinubu ya nemi amincewar ’yan Majlisar ƙasar kan buƙatar gwamnati ta karɓo bashin Dala biliyan 21 daga ƙasashen ƙetare, wanda kuma a ciki ne Najeriyar ke neman rancen na dala biliyan 5 daga kamfanin man Saudiya na Aramco.

Ya zuwa yanzu dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai gano manyan bankunan da za su taimaka wajen aiwatar da wannan yarjejeniya ba, sai dai majiyoyinsa sun shaida masa cewar akwai guda daga nahiyar Afrika, yayin da ragowar za su kasance daga yankin Gabas ta Tsakiya.

Idan har wannan yarjejeniyar karɓar bashin ta ƙullu, za ta kasance mafi girma irinta da Nijeriya ta shiga, kuma karo na farko kenan da irin hulɗar ke shiga tsakanin Nijeriyar da Saudiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Aramco rance Saudiyya karɓar rancen Dala biliyan

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Afrika

Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na kasashen Afrika da suka zo kasar Sin domin halartar taron ministoci masu jagorantar aiwatar da sakamakon da aka cimma yayin a taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika.

Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya tattauna jiya Talata a Changsha, babban birnin lardin Hunan, da ministocin da suka hada da Musalia Mudavadi na Kenya da Yassine Fall ta Senegal da Mahmoud Thabit Kombo na Tanzania da Selma Ashipala-Musavyi ta Namibia da Phenyo Butale na Botswana da kuma Tete Antonio na Angola.

Da yake ganawa da Musalia Mudavadi na Kenya, Wang Yi ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Kenya wajen aiwatar da matsayar da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, da karfafa goyon bayan juna da aminci a tsakaninsu, da karfafa tubalin dangantakar Sin da Kenya da ci gaba da kara wa dangantakarsu kuzari.

Yayin ganawa da Yassine Fall ta Senegal kuwa, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da gabatar da sabbin damarmakin ci gaba ga kasashen Afrika, ciki har da Senegal, domin taimakawa kasashen zamanantar da kansu. (Mai Fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gini ya kashe Ba’indiye a Zariya
  • Ɗan Ƙasar Indiya Da Wasu 12 Sun Gurfana A Kotu Kan Satar Wa Dangote Dizal Na Naira Biliyan 4
  • Dalilin da babu abin da gwamnatin NNPP ta taɓuka a Kano — APC
  • Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Afrika
  •  Shugaban Kasar Amurka Ya Siffata Masu Zanga-Zanga A Los Angeles Da Dabbobi
  • Nijeriya Ta Fuskanci Cikas Wajen Karɓo Rancen Dala Biliyan 5 Daga Saudiyya
  • Saudiyya za ta fara bayar da bizar Umara
  • Ƙungiyar G-5 Ta Ceto Nijeriya Daga Faɗa Wa Rikici — Wike
  • Wani Kamfanin Kera Kayankin Aikin Likita Ya Gabatar Da Sabon Na’urar Tiyata