Ba Mu Iya “Gina” Ayaba A Amurka
Published: 10th, June 2025 GMT
A wani taron sauraron bayanai da aka gudanar a kwanan baya, ‘yar majalisar wakilan kasar Amurka Madeleine Dean ta yi wa ministan kasuwanci na kasar, Howard Lutnick tambayoyi game da yanayin ciniki da manufofin harajin kwastam na kasar, inda ta tono shirmen da ke cikin matakan haraji da Amurka ta dauka a kan kayayyakin da take shigarwa daga kasa da kasa.
A hakika, a yayin da tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen duniya ke kara dunkulewa baki daya, kasa da kasa su kan samu mabambantan fifiko a sana’o’i daban daban sakamakon bambancin albarkatun da suke da su, ko kuma bambancin ci gabansu, lamarin da ya sa suke yin musayar kayayyakin da suke da fifikonsu don tabbatar da bunkasa ta bai daya, hakan nan kuma sana’o’i daban daban na dogara ga juna. Kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kasar Amurka ita kanta ta amfana da bunkasuwar tattalin arzikin duniya da kuma ciniki mai ‘yanci.
Duk da haka, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki matakan haraji na barkatai a yunkurin daidaita matsalar da ya kira wai “gibin kudin ciniki”, matakin da ba haifar da munanan matsalolin haraji a fadin duniya kawai ya yi ba, har da daga farashin kayayyaki a cikin kasar kansa. Lallai Amurka tana fama da rashin lafiya, amma ta sa sauran kasashe shan magani. Hakan ba zai taimaka ga daidaita matsalolin da tsarin tattalin arzikin kasar ke haifarwa ba, sai ma kara tsunduma shi cikin mawuyacin yanayin tattalin arziki. (Mai Zane:Mustapha Bulama)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kasar Amurka
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp