Shugaba Bola Tinubu ya soke shirin yi wa ‘yan kasa jawabi kai tsaye da aka shirya gudanarwar tun farko a ranar Alhamis, 12 ga watan Yuni, domin tunawa da cikar ranar dimokradiyyar Nijeriya shekaru 26. A maimakon haka, zai gabatar da jawabinsa na ranar dimokuradiyya a gaban wani zama na musamman na hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar.

An bayyana sauyin ne a wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na ofishin SGF, Segun Imohiosen ya fitar a ranar Laraba. Amma Duk da haka, sauran shirye-shiryen ranar Dimokradiyya za su ci gaba da gudana kamar yadda aka sanar a baya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Super Falcons Zasu Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja.

A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya.

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC Na Ƙasa, Farfesa Yilwatda

“Ina alfahari da ku, Nijeriya gaba ɗaya na alfahari da ku. Kun ɗaga martabar ƙasarmu, ku abin koyi ne a zamanin ku. Ina mika godiya ta musamman ga masu horar da tawagar,” in ji Tinubu, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar. Shugaban ya kuma miƙa saƙon ban girma ga Rasheedat Ajibade da ta samu lambar gwarzon ‘yar wasa a gasar.

Yayin da yake zantawa da tawagar, Tinubu ya yi addu’ar dawowar su lafiya zuwa gida, yana cewa: “Ina fatan zaku iso lafiya, Allah ya saka muku da alheri.” A madadin tawagar, Rasheedat ta gode wa shugaban ƙasa bisa amincewa da biyan cikakken alawus na ‘yan wasan, tana mai tabbatar masa da cewa tawagar za ta ba da dukkan ƙoƙarinta wajen kawo kofin WAFCON zuwa Abuja.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Ƙaddamar Da Shirin Bai Wa Malaman Manyan Makarantun Nijeriya Rancen Miliyan 10
  • Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir
  • An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
  • An gano gwawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja
  • Mazauna Sokoto Sun Yi Murna Bayan Nasarar Kashe Fitattun ‘Yan Bindiga 3 A Jihar
  • Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
  • Super Falcons Zasu Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu
  • An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe
  • ‘Yan Majalisa Sun Zargi Hukumomin Gwamnati Da Wawure Sama Da Naira Biliyan 103.8
  • Majalisa Ta Ba Wa Shugaban NNPCL Awa 24 Ya Bayyana Gabanta Ko Ta Sa A Kamo Shi