Falasdinawa Masu Yawa Sun Yi Shahada A Cibiyoyin Raba Kayan Agaji
Published: 11th, June 2025 GMT
Sojojin HKI sun kai hari akan Falasdinawan da su ka yi cincirindo domin karbar abinci da hakan ya yi sanadiyyar shahadar da dama daga cikinsu.
Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin HKI su ka rika kai hare-hare akan cibiyoyin cibiyoyin raba agaji wadanda dama suna a karkashin kulawar su kansu ‘yan sahayoniyar da kuma Amurka.
Majiyar Asibitin “Audah” ta sanar da cewa an kai shahida 4 da kuma wadanda su ka jikkata sanadiyyar hare-haren na sojojin mamaya a wurin raba kayan agaji dake kan titin “Salahuddin” a tsakiyar zirin Gaza.
A arewacin yankin Gaza kuwa wasu samarin Falasdinawa 4 sun yi shahada bayan da jiragen yakin HKI su ka kai hari a kusa da makarantar “Usamatu Bin Zayd” dake yankin Safdhawi.
Wasu jiragen yakin na ‘yan mamaya sun kai wasu hare-haren a unguwar “Basrah’ dake birnin Gaza. Ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan adadin wadanda su ka jikkata ko yin shahada.
A kusa da mashigar ‘al-Buraij’ ma sojojin mamayar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan mutane da suka yi cirko-cirko suna tsumayen kayan agaji.
Wasu wuraren da aka sami shahidai sun hada da sansanin ‘yan hijira na “Nusairat’ da “Muwasi” a Khan-Yunus, sai kuma “Badhnus-samin”.
Tun a makwannin da su ka gabata ne dai MDD ta sanar da cewa ba za ta shiga cikin tsarin dake karkashin HKI da Amurka ba, na raba kayan agaji, saboda manufarsa korar Falasdinawa daga gidajensu. Ita kuwa kungiyar Hamas ta ce, wuraren na rabon agaji sun zama tarko kisa.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA