Shugaban Kasar Amurka Ya Siffata Masu Zanga-Zanga A Los Angeles Da Dabbobi
Published: 11th, June 2025 GMT
Shugaban kasar ta Amurka wanda ya gabatar da jawabi a gaban sojojin kasar a sansanin ‘Fort Bragg’ dake Jahar North Carolina ya bayyana cewa; Jahar Los Angeles tana fuskantar mamaya daga makiya ‘yan kasashen waje.”
Har ila yau shugaban na Amurka ya ce; Ba za mu bari a rika kai wa jami’an tsaron gwamnatin tarayya hari ba, ba kuma za mu bari a mamaye wani gari daga cikin garuruwan Amurka ba.
Shugaban kasar ta Amurka ya kuma ce; Abinda birnin Los Angeles yake fuskanta hari ne daga kowace kusurwa da ‘yan daba suke yi, kuma suna dauke da tutocin kasashen waje.”
Birnin Los Angeles yana fuskantar gangami da Zanga-zanga saboda nuna kin amincewa da Shirin korar ‘yan ci-rani ba bisa ka’ida ba.
An sami sabani da rashin jituwa a tsakanin gwamnatin tarayya da kuma ta jaha akan matakin da ya kamata a dauka domin magance matsalar bakin hauren.
Gwamnan Jahar ta Califonia ya zargi shugaban kasar Donald Tump da kama-karya saboda aikewa da sojoji akan titunan birnin domin fuskantar masu gangamin da Zanga-zangar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
A yau Litinin ne tawagogin kasashen Sin da Amurka, suka sake tattaunawa a rana ta biyu, game da batutuwan tattalin arziki da cinikayya a birnin Madrid na kasar Sifaniya. A jiya Lahadi, sassan biyu sun gudanar da zaman farko ne a fadar Santa Cruz, inda ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Sifaniya yake.
A cewar kakakin ma’aikatar cinikayyar kasar Sin, sassan biyu za su tattauna batutuwan da suka hada da matakin Amurka na kakaba jerin haraji daga bangare guda, da keta matakan kayyade fitar da hajoji, da batun dandalin TikTok. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp