Al’ummomi Daga Sassan Duniya Suna Yin Tofin Allah Tsine Kan Sace Masu Fafatuka A Kan Hanyarsu Ta Zuwa Gaza
Published: 10th, June 2025 GMT
Al’ummu daga dukkan sassan duniya suna mayar da martaninsu cikin fushi bayan sace jirgin ruwa Madeleine mai dauke kayayyakin jin kai zuwa Gaza
Kwamandojin sojojin mamayar Isra’ila sun yi garkuwa da jirgin ruwan farare hula Madeleine, wanda ke yunkurin karya killace yankin Zirin Gaza da aka yi a kokarinsu na shigar da kayan agaji ga al’ummar yankin da suka rage.
A wani sabon laifin da ya saba wa dukkanin ka’idojin kasa da kasa da na jin kai, sojojin mamayar Isra’ila sun yi awon gaba da jirgin ruwan da kekokarin karya killace Gaza na Madeleine, tare da yin awungaba da masu fafutuka na kasa da kasa da ke cikin jirgin. Jirgin yana kan hanyar zuwa zirin Gaza dauke da kayan agaji ne.
Sojojin mamaya sun kai jirgin zuwa tashar jiragen ruwa ta Ashdod domin yi wa masu fafutuka tambayoyi tare da tabbatar da ko su wane ne su, har zuwa lokacin da ake yi musu tambayoyi a wani sansanin sojin ruwa da ke tashar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp