Kasashen Iran Masar Da Kuma Omman Sun Gudanar Da Taro A Oslo
Published: 12th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas aragchi da tokwransa na kasar Masar Badr Abdullati da kuma tokwaransu na kasar Omman Badr ben Hamad Al-Busaidi sun tattauna a tsakaninsu a birnin Oslo inda suka halattar taron tattaunawa ta 22th da ake gudanarwa a birnin na Oslo babban birnin kasar Norway.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa bangarorin biyu sun yi maganar rikice-rikicen da ke faruwa a yankin da kuma hanyar warwaresu.
Taron oslo na shekara shekara dai a wannan karon ya maida hankali ne kan abubuwan da suke faruwa a yankin Asiya da kuma hanyoyin da yakamata abi don rage halin da ake ciki a yankin. Musamman matsalar yaki da kima kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza da kuma yadda HKI ta sabawa dukkan dokokin kasa da kasa a yakin.
Jaridar The National ta kasar Amurka ta bada labarin cewa kasashen Iran da masar wadanda basa da dangantakar Diblomasiyya na kimani shekar 40 sun tattauna batun maida huldar jakadanci a tsakaninsu, inda daga cikin ministan harkokin wajen Masar ya bukaci a shafin hoton Khalid Islam buli wanda ya kashe tsohon shugabann kasar Masar a shekara 1980 wanda aka sanya a kan wani babban titi a birnin Tehran. Har yanzun dai ba’aji ta bakin gwamnatinn kasar Iran kan hakan ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Yanke Hukuncin Kisa Kan Yan MKO A Nan Iran
Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi sani da munafukai.
Kamfanin dillancin larabann Tasnim na JMI ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa mutanen biyu Mahdi Hassani da Behrouz Ehsani, sun yi amfani da makamai wadanda suka hada da gurneti da kuma wasu ind suka kashe mutane fararin hula a dai dai lokacinda ake hargitsi a cikin kasar don tada hankalin mutane da kuma wargaza harkokin tsaro a cikin kasar.
Labarin ya kara da cewa an tabbatar da tare da wata shakka ba suna aiki tare da kungiyar ta MKO wadanda suke adawa da JMI tun ranar kafa ta.
Kungiyar MKO dai it ace babban kungiya wacce take adawa da JMI ta kuma kashe mata manya-manyan malaman addini a farkon nasarar juyinn juya halin musulunci a kasar. Sannan daga baya tare da taimakon gwamnatin kasar Iraki ta yaki JMI a warare da dama. Daga karshe ta maida cibiyarta zuwa kasashen turai da Amurka inda suke samun makudan kudade don kimar da JMI. MKO ta kashe mutanen iran akalla 17000 tun lokacin shekara 1979 ya zuwa yanzu.