Iran Za Ta Kara Yawan Sanadarin Urani’um Da Take Tacewa A Wuri Na Sirri
Published: 12th, June 2025 GMT
A wani bayani na hadin gwiwa da hukumar makamashin Nukiliya ta Iran da kuma ma’aikatar harkokin wajen Iran su ka fitar, sun bayar da umarnin a bude wani wuri na daban na sirri domin ci gaba da tace sanadarin Urani’um, sannan kuma a maye gurbin bututu tace sanadarin mai mataki na daya, da mai mataki na shida a cibiyar “Pardo.
Bayanin dai ya zo ne a matsayin mayar da martani ga sanarwar da ta fito daga kwamitin alkalai na hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa akan Iran.
Bugu da kari, bayanin na Iran ya kuma ce; A kodayaushe jamhuriyar musulunci ta Iran tana aiki da nauyin da ya rataya a wuyanta, kuma har ya zuwa yanzu babu wani rahoto na hukumar wanda ya bayyana cewa; Iran ba ta aiki da ka’idojin hana yaduwar makaman Nukiliya.”
Haka nan kuma bayanin ya ambaci cewa; Tare da cewa Iran tana daukar rahoton da cewa na siyasa ne, wanda Amurka da kasashen turai suke amfani da hukumar a matsayin makami, ba tare da dogaro da wani dalili na ilimi ba.
Har ila yau Iran din ta zargi Amurka da kasashen na turai da wuce gona da iri wajen tsara rahoton da yake cin karo da rahoton da shugaban hukumar ta makamashin Nukiliya ya fitar, wanda bai sami wani abu mai shiga duhu ba a cikin Shirin na Iran na zama lafiya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wulayati: Hanyar Zangezur Wata Shirin Amurka Ne Don Matsa lamba Kan Kasashen Iran Da Rasha
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran.
Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba.
A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da wadannan tsare-tsare.”
Ya kara da cewa, manufar farko ita ce raunana gwagwarmaya da yanke alakar Iran da yankin Caucasus da kuma killace Iran da Rasha ta kasa a kudancin yankin.
Ya bayyana cewa: “Wannan aikin ba wai kawai wani bangare ne na shirin Amurka na maye gurbin Ukraine da yankin Caucasus a matsayin wani sabon fage na matsin lamba kan Rasha da Iran ba, amma ana aiwatar da shi ne tare da goyon bayan kungiyar tsaro ta NATO da kuma wasu kungiyoyin ‘yan kishin kasa na Turkiyya (Pan-Turkist).