Xi Ya Zanta Da Takwaransa Na Kasar Koriya Ta Kudu
Published: 10th, June 2025 GMT
Da safiyar yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Koriya ta kudu Lee Jae-myung ta wayar tarho.
Da farko, Xi Jinping ya sake taya Mista Lee murnar lashe babban zaben shugaban kasa. Sa’an nan, ya jaddada cewa, ya kamata kasashen Sin da Koriya ta Kudu su tsaya tsayin daka kan burin tallafawa juna da cimma moriyar juna, tare da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon matsayi, domin ba da karin tallafi ga al’ummun Sin da Koriya ta Kudu, da samar da tabbaci cikin yankin da ma kasashen duniya baki daya, inda ake fuskanar da sauye-sauye da tashe-tashen hankula.
A nasa bangare kuma, shugaba Lee Jae-myung ya ce, yana mai da hankali matuka kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana kuma fatan hada gwiwa da kasar Sin wajen zurfafa zumuncinsu, da kyautata dangantakar abokantaka a tsakanin al’ummomin kasashen biyu, ta yadda kasashen biyu za su cimma sakamako da dama bisa hadin gwiwarsu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Faransa Zata Bayyana Amincewa Da Samuwar kasar falasdinu
Shugaban kasar faransa Emanuel macron ya bayyana a jiya Alhamis kan cewa zai shelanta amincewar gwamnatin kasar Faransa da samuwar kasar falasdinu mai cikekken iko a taron babban zauren MDD a cikin watan satumba mai zuwa.
Jaridar ‘Arabnews’ ta kasar saudiya ta nakalto macron yana fadar haka a shafinsa na X ‘ ya kuma kara da cewa, da farko yana son ganin yaki a gaza ya zo karshe, sannan fararen hula da suke gaza su tsira daga kisa da kuma yunwan da aka dora masu.
Kasar faransa dai ita ce babbar kasa a cikin kasashen turai da suka fara amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta. Kafin haka dai kasashen 140 a duniya sun amince da samuwar kasar falasdinu mai zaman kanta.
A jiya Alhamis gwamnatin kasar faransa a hukumance ta mikawa mataimakin shugaban PLO a birnin Qudus Hussain Al-sheikh. Shugaba Mahmood Abbas yay aba da matsayin da shugaban kasar faransa ya dauka ya kuma gode masa da wannan kokarin.
Kamar yadda aka saba, HKI ta yi allawadai da matsayin na shugaba macron. Haka ma Marco Rubio