Ana zargin uwa da kashe ’yarta kan Naira 100 a Zariya
Published: 11th, June 2025 GMT
Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan zargin kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur Tukur da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a unguwar har maƙwabta suka ƙi yi wa gawar yarinyar sallah saboda tsoron abin da zai biyo baya.
Wasu maƙwabta sun bayyana cewa Khadija ta doke Fadila da taɓarya ne saboda ta zargi yarinyar da satar Naira 100.
Sun ce irin wannan ɗabi’a na duka da tsangwama ba sabon abu ba ne domin sau da dama idan ta tura Fadila talla aka samu matsala, sai ta lakaɗa mata dukan tsiya.
Wani mutum ya ce: “Dalilin da ya sa muka ƙi yi mata sallah shi ne, ba a ɗauki matakin da ya dace ba. An zubar da gaskiya. Saboda haka mu ma muka yanke shawarar ba za mu yi mata sallah ba.”
Amma mahaifiyar da ake zargi, wato Khadija, ta musanta zargin cewa ta yi wa ’yarta da duka da taɓarya.
Ta ce a lokacin da ta ke dukan yarinyar, ba kowa a gidan sai yara.
Mijin matar, Malam Mustapha Musa, ya shaida wa wakilinmu cewa lokacin da lamarin ya faru ba ya gida, don haka bai san yadda abin ya wakana ba.
Tuni mahaifin Fadila ya ɗauki gawar ’yarsa zuwa ƙauyensu da ke ji6har Kano domin yi mata sutura.
Ya ce: “Na bar komai da hannun Allah.”
Wani jami’in tsaron sa-kai wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce sun gayyaci Khadija da mijinta ofishinsu domin amsa tambayoyi, amma daga baya sai suka janye bayan sun ga ’yan sanda sun isa wajen.
Wakilinmu ya kai ziyara babban ofishin ’yan sanda da ke Ɗan Magaji, amma ya tarar babban jami’in ba ya nan.
Mataimakinsa ya ce ba su da masaniya game da lamarin.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya ce: “Ka jira, zan tuntuɓi ofishin yankin don jin yadda lamarin yake.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga ’yan sandan ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yawon Sallah Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
Ya ce kuma kayan da ake fitarwa zuwa waje waɗanda ba man fetur yanzu su kusa yin kai da kai da fetur.
Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasar a waje ya haura kusan dala biliyan 42, daga biliyan 32 lokacin da Tinubu ya hau mulki.
Har ila yau, ya ce an biya bashin da ya haura biliyan bakwai, ciki har da miliyan 800 da ake bin jiragen saman Nijeriya.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce yanzu jihohi na iya biyan albashi da fansho a kan lokaci, sannan suna da rarar kuɗi don ayyukan raya ƙasa, abin da ba a saba gani ba a baya.
“Bayan shekara biyu da watanni biyar kacal a ofis, Shugaba Tinubu ya cimma abubuwa da dama. Ko da Atiku da magoya bayansa ba su yadda ba, ’yan Nijeriya suna ganin sauyin,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta kuma zargi Atiku da jam’iyyar PDP da yaɗa maganganun da za su kawo tashin hankali.
Ya bayyana cewa yawancin matsalolin da ake fuskanta sun samo asali ne daga rashin kyakkyawan shugabanci tun a lokacin PDP, lokacin da Atiku yake mataimakin shugaban ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp