Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatun Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha
Published: 11th, June 2025 GMT
Akpabio ya shigar da buƙatu a gaban kotun inda ya nemi ƙarin lokaci don ɗaukaka ƙara a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 10 ga watan Maris, 2025.
Wannan shari’a ta haɗa da Sanata Natasha da ke ƙarar Sakataren Majalisar Tarayya da wasu mutane uku kan dakatar da ita.
Haka kuma, Akpabio ya nemi kotu ta ba shi izini ya ɗaukaka ƙara da kuma dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar a Babbar Kotun har sai an yanke hukunci a kotun ɗaukaka ƙara.
Sai dai yanzu da aka janye ƙorafe-ƙorafen kuma kotu ta yi watsi da su, hakan na nufin waɗannan bukatu na Akpabio ba za su ci gaba da sauraron su a a kotun ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar.
Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna.
Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a BornoDa yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na ilimi, noma, kiwon lafiya, kasuwanci, da samar da ababen more rayuwa.
“Babu wani sashe a jihar da aka bari a baya a cikin ayyukan ci gaban da Gwamna Mai Mala Buni ke aiwatarwa,” in ji Adamu.
A nasa martanin, Gwamna Buni, wanda mataimakinsa, Alhaji Idi Barde Gubana, ya wakilta, ya karɓi karramawar a matsayin “hanyar mayar da martani mai ƙarfi” da ke tabbatar da tasirin gwamnatinsa a matakin farko.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin kai Yobe matsayin jiha da za ta iya gogayya da takwarorinta a fagen ci gaban ƙasa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ’yan siyasa daga ciki da wajen jihar, da kuma sarakunan gargajiya.