A saurari sauyin da za mu yi wa ɓangaren man fetur a Nijeriya — Dangote
Published: 10th, June 2025 GMT
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce nan ba da jimawa ba al’ummar Nijeriya za su ga gagarumin sauyi a ɓangaren man fetur ɗin ƙasar.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai, a lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci matatar mansa da ke yankin Lekki a Jihar Lagos.
Ya ce sauyin da al’umma za su gani a yanzu, ba wai na rage farashin man ba ne kaɗai, wanda zai sauya baki ɗaya yadda ake gudanar da harkokin mai ne a ƙasar.
“A yanzu da shugaban ƙasa ya ziyarcemu, kuma ya ba mu ƙarin makamashi, ina mai shaida muku cewa nan ba da jimawa ba za ku ji daga garemu, kuma zai kasance sauyi ne a ɓangaren mai baki ɗaya a ƙasar, ba wai kawai rage farashinsa ba kaɗai.”
A watan Oktoban bara ne dai Matatar Dangote ta fara saida man fetur, lamarin da ya kawo saukar farashinsa a ƙasar.
To sai dai dillalan man fetur a Nijeriya, na ganin ya kamata Matatar Dangoten ta riƙa saida lita ɗaya ƙasa da Naira ɗari 8, la’akari da cewar ana sayar wa kamfanin ne da ɗanyen mai a kuɗin Naira maimakon dalar Amurka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matatar Dangote
এছাড়াও পড়ুন:
Nijeriya za ta kece raini da Gabon a wasan neman tikitin Kofin Duniya
A yammacin wannan Alhamis ce tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya Super Eagles za ta fafata da ƙasar Gabon a wasan neman tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Wasan da za a buga da karfe 5 na yamma a filin wasa na Prince Moulay Hassan da ke Rabat, Morocco, zai zama wasa na farko tsakanin ƙasashen tun bayan shekarar 2005, lokacin da Nijeriya ta doke Gabon da ci 2-0.
Wannan wasan dai shi ne zai tabbatar da nasarar Nijeriya na samun tikitin shiga gasar kafin haɗuwar ta da Kamaru ko Dimokuraɗiyyar Congo a ranar Lahadi.