A hanzarta kwangilar yashe Madatsar Ruwa ta Alou — Gwamnatin Borno
Published: 11th, June 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanzarta ɗaukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam ɗin Alou da ya haifar da ambaliya a bara.
Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mummunar ambaliya.
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaro na Jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin.
“Har yanzu ba mu ga ’yan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka.
“Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala.
“Ya kamata a ce an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba zai ambaliya ba,” in ji Farfesa Tar.
A damunar bara ne dai madatsar ruwa ta Alou Dam ta cika ta tunbatsa inda ta kuma karye, wani abu da ya janyo ambaliyar ruwa da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Maiduguri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jihar Borno Madatsar Ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Wulaƙanta Naira: Kotu ta bayar da belin Hamisu Breaker da G-Fresh
Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta bayar da belin fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira.
Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari, bayan sun amsa laifin da ake tuhumarsu a gaban kotu.
Sojoji sun ceto yaro da aka sayar shekaru 3 a Filato Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Sarkin GusauHukuncin ya biyo bayan tuhumar da Hukumar EFCC ta shigar da su a gaban kotu, bisa laifin wulaƙanta Naira.
A cewar ƙarar, G-Fresh ya watsa kuma ya taka takardun Naira 1,000 har na Naira 14,000 yayin da yake rawa a shagon wata mai suna Rahma Sa’idu a Ƙaramar Hukumar Tarauni.
Shi kuma Hamisu Breaker, ya watsa Naira 30,000 na takardun Naira 200 a wani taron walima da aka yi a Hadeja da ke Jihar Jigawa.
Dukkaninsu sun aikata laifin ne a watan Nuwamban 2024.
Laifin ya ci karo da Sashe na 21(1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007, wadda ta haramta cin zarafi ko wulaƙanta Naira.
Bayan amsa laifinsu, kotun ta ba su damar biyan tara maimakon zaman gidan yari.
Kowannensu ya biya tarar Naira 200,000, wanda hakan ya sa aka sake su bayan tsare su.
Wannan hukunci na nuna cewa gwamnati na ɗaukar wulaƙanta Naira a matsayin babban laifi, duk da cewar akwai damar samun beli ko biyan tara.