Leadership News Hausa:
2025-07-27@20:16:18 GMT

Sin Da Kenya Sun Zurfafa Hadin Gwiwa A Bangaren Kiwon Lafiya

Published: 11th, June 2025 GMT

Sin Da Kenya Sun Zurfafa Hadin Gwiwa A Bangaren Kiwon Lafiya

Kasashen Sin da Kenya sun zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren kiwon lafiya, inda kasar Sin ta bayar da guraben tallafin karatu 500 da kaddamar da shirye-shiryen musaya 20 a kwacce shekara.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron da aka yi tsakanin jakadar Sin dake Kenya Guo Haiyan da babban sakataren ma’aikatar lafiya ta kasar Aden Duale, ta ce hadin gwiwar kasashen biyu na da muhimmanci wajen kyautata makomar kasar ta zama jagora a bangaren kiwon lafiya.

A cewar Adel Duale, bangarorin biyu sun kuma tattauna game da kafa cibiyoyin samar da riga kafi da harhada magunguna ta hanyar amfani da fasahar kasar Sin.

Ya kara da cewa, shirin hadin gwiwa na dala miliyan 500 a tsakaninsu zai mayar da hankali wajen karfafa tsarin samar da kayayyaki a kasar Kenya da rage dogaro kan shigar da kayayyaki daga ketare da samar da guraben ayyukan yi da kai kasar ta gabashin Afrika matsayin jagora a fannin samar da kayayyakin kiwon lafiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya

Kamfanin kera manyan motocin dakon kaya na kasar Sin Sinotruk ya kaddamar da motocinsa kirar H2 mai dakon kaya marasa nauyi da ta H3 ta dakon kaya masu matsakaicin nauyi a kasar Kenya, tare da kamfanin CFAO Mobility a matsayin mai rarraba motocin a cikin gida.

Babban manajan kamfanin CFAO Mobility na Sinotruk Sarfraz Premji, ya shaida wa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, an kera samfuran motocin ne ne don kawo sauyi ga masana’antar sufuri saboda suna iya daukar kaya masu nauyi, sannan an sa musu manyan tankunan mai, inda hakan zai rage bukatar yawan zuwa shan mai da kuma ba da damar daukar dogon lokaci ana tafiya, kana wannan zai rage yawan kudin da ake kashewa wajen shan mai.

Premji ya ce “bisa tabbatar da ingancin dogaro da su da kuma karkonsu na dogon lokaci, wadannan manyan motocin sun zamo na daban da babu irinsu kuma ababen zabi a cikin nau’o’in manyan motoci masu dakon kaya masu karami da matsakaicin nauyi.”

Ya kuma yi nuni da cewa, ana samun karuwar rungumar manyan motocin kasar Sin a kasuwannin kasar Kenya ne, saboda suna dacewa da titunan mota na Afirka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo
  • Hanyoyin Gyaran Gashi
  • ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark
  • Jagora: Za’a Gaggauta Ci Gaba A Ilmi Da Fasahar Tsaron Sojojin Kasar
  • Tallafin Lafiya: Ƙungiyar Rotary Ta Raba Kayan Haihuwa kyauta Ga Mata Masu Juna Biyu  A Kaduna
  • Yawan Mutanen Da Suka Rayukansu A Rikicin Lardin Suwaida Na Kasar Siriya Ya Kai 1,400
  • Kamfanin Sinotruk Na Kasar Sin Ya Kaddamar Da Sabbin Motocin Dakon Kaya A Kenya
  • Bukatar Hukunta Masu Jagorantar Kashe-kashe A Nijeriya
  • Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Tattaunawa Tsakanin Shugabannin Sin Da EU Karo Na 25 Tare Da Shugaban Majalisar EU Da Shugabar Hukumar EU
  • Alakar Sin Da EU Na Bukatar Hadin Gwiwa Ba Raba-gari Ba