HausaTv:
2025-07-31@16:19:13 GMT

Iran Da Saudiyya Sun Tattauna Kan Taron OIC Mai Zuwa

Published: 27th, February 2025 GMT

Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah.

Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran (RII).

A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da tattauna taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OIC da za a yi a Jeddah.

Dama a kwanan baya bangarorin sun tattauna kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwace zirin Gaza dama tilasta wa falasdinawan yankin kaura zuwa Masar da Jordan, shirin da dukkan kasashen biyu sukayi fatali da shi.

Araghchi ya la’anci shirin na Amurka da ‘yan sahyoniya na tilastawa al’ummar Gaza komawa wasu kasashe a matsayin ci gaba da shirin ‘yan mulkin mallaka na shafe Falasdinu, yana mai jaddada bukatar daukar kwararan matakai na kasashen duniya don tunkarar wannan makirci.

Ya kuma yi kira ga al’ummar musulmi da sauran al’ummar duniya baki daya da su dauki matakin gaggawa kan lamarin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai

Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu.

A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci.

Haka nan kuma ya ce; Daga cikin manufofin da HKI ta Shata cewa za ta cimmawa a yayin yakin, shi ne samar da sauyi a cikin wannan yankin, shi ya sa da dama daga cikin hukumomin kasashen larabawa su ka fahimci cewa raunana Iran yana nufin raunana kasashensu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ministan Harkokin Wajen Siriya Yana Rasha Don Bude Sabon Shafi Tsakaninsu
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Yi Allah Wadai Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Mata
  • Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Tallafin Miliyoyin Naira Ga Ƴan NURTW da Mahauta a Jigawa
  • Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • Kasashen Yankin Caribbean Suna Son Bunkasa Alakarsu Ta Kasuwanci Da Nahiyar Afirka
  • Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Batun Hadin Gwiwar Kafofin Watsa Labarai A Tsakaninsu
  •  Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza